Part 27

1.4K 172 3
                                    


Se October akai releasing result dinmu Alhamdulillah komai ya tafi daidai as plan, wannan Karon Abhi da mummy ne suka zo daukarmu har Chennai, seda mukai Kwana hudu muna yawo kafin kuma muka wuce New Delhi mukabi flight zuwa Abuja. Cikin jirgin baki daya babu Abinda nake tunani se Wacce Irin rayuwa kuma zanyi a Nigeria? Bansan wacce kurar zan kuma je in tarar ba, haka dai na dinga tunani kafin can bacci yayi awon gaba dani.

Muna isowa nigeria dama a Lagos jirgin yayi landing hakan yasa muka Kwana a wani hotel cikin Lag din don kuwa past 2am muka iso. Washegari se yamma mukabi jirgi zuwa kano inda su Hanifa dasu uncle kamal sukaxo daukarmu murna kam ba'a magana, su Rafee'ah muka Fara kaiwa sannan muka wuce gida. Gidan an gyara shi yayi kyau sosae, daki na yana can ciki ni daya abuna, na Mameh da Hanifa Kina shigowa parlour Se na Anty idan Taxo Nikam se kinbi wani corridor kafin ki iske dakina, Wanda asali na Baffa Malam ne, Allah sarki Baffa na Allah ya jikanka da rahma, bana taba manta wannan tsohon cikin rayuwata, Allah dai ya haskaka kabarinahi. Wanka na fara yi kafin na fito parlour inda Hanifa Ke jirana, abinci irinsu dambu, finkasau, masa, sinasir shi muka ci naji dadi sannan na shiga gaida Mameh, Tana zaune kan couch rikeda waya nayi sallama, amsawa tayi sannan na karasawa ciki nace

Mameh ina yini

A hankali ba kamar ko Yaushe ba tace

Lapiya lau Nadia.....

Seda na dago don wannan shi ne Karo na farko da Mameh ta kirani da Nadia, hakan ya bani mamaki ba kadan ba

......kin dawo lapiya?

Lapiya lau

Na bata ansa kafin na fice ina fadin sabon salo kiran sallah da whistle.

Seda nayi Kwana biu Banje ko ina ba, banda bacci babu abinda nake, a rana ta uku ne na Fara shirin bikin Rafeey gadangadan. Yau ta kasance laraba, a Washegari kuma zaa Fara bikin my one and only Rafee'ah, komai da zamu Yi amfani dashi Yana aje, Tun safe mukaje gidan kunshi aka rangada mana shi na gani na kuma fada, muna dakin Rafee'ah Anty ta aiko kirana, ita da mummy ne kadai cikin dakin Abhi na shiga da sallama don mutane sun Fara taruwa mussaman yan jimeta,

Baby shigo gamu a nan

Shiga nayi ina fadin

Mummy ai mutum bazai San kuna ciki ba, gani

Yawwa

Mummy ta fada

Gidan Rafee'ah nake son kije dake da Hanifa da Biebie ku gyara mata kaya

Kayan suna ina?

Na tambaya, key Anty ta miko min da yawa tace

Leave in secret saboda idan aka San zakuje mutane zasu biku, kayan jiya na Kai da daddare gyarawa kawai zakuyi.

To

Nace da su kafin na fita amma se Anty ta kwalla min kira, ina zuwa tace ga motar ta naje da ita, Tunda dama tun lokacinda na dawo nayi joining driving school amma saboda tsoro Irin nawa seda nayi wata daya kafin na iya da kyau. Tare muka tafi Inata driving abina, ni kaina ina mamakin how happy I'm, ban taba mafarkin akwai ranar da zai zo in cigaba da farin ciki ba, amma da yardar Allah gashi Inata farin ciki.

Gidan Rafee'ah a dambazau road yake, yayi kyau gidan sosae, sede upstairs ne da downstairs, upstairs na Rafee'ah shikuma downstairs na brother dinsa Wanda xa'ayi musu auren tare, amma tsarin gidan zai burgeka yadda babu Wanda zai samu access da dayan sede idan zagayawa daya yayi, haka muka shiga muna shirya mata wardrobe dake 2 bedrooms ne Dayan empty yake se Dayan a rufe yake ina tunanin na Anas ne. Tun muna yi da dadin rai har muka fara gajiya amma ya muka iya, hakan yasa muka cigaba, wajen maghrib wayata ta Fara ringing , dama mun gama su Hanifa sun sauka kasa se ni ina locking kofofin, wayar na zaro nayi picking ina fadin

Ango! Ango! Ango! Kasha kamshi

Inajin dariyar shi kafin yace

Tace min kina nan, gani nazo kawo muku abinci.

Godiya muke ango, amma kamara don gani nan ina fitowa.

To Ina jiranki.

Maida wayar Nayi cikin wallet dita Dama da ita daya nazo, a hankali na taho Sede naji wata muguwar faduwar gaba ta ziyarce ni sakamaakon wanda idanuna suka hango min ya juya baya, a hankali na shiga karya ta kaina akan bashi bane, no it can't be him! Tamkar yasan na iso gurin shima ya juyo wanda yayi sanadin bugawar zuciyata nasan shima tashi ta buga don kuwa gwara ni na cigaba da daga kafafuna amma shikam nasan ya manta inda yake don kuwa Anas na tayi masa magana amma hankalinshi na kaina don kuwa inajin hot gaze dinsa a kaina.

Karasawa nayi ina masking mood dina ni a dole inasan nuna I don't know of MUKHTAR's existence a gurin,

Ango ango ango Kasha kamshi

Murmushi yayi yace

Ga babban bako na kawo miki, tuntuni yake damuna akan na kawo shi gurinki ya nemi yafiyar ki.

Murmushi nayi nace

Allah sarki, kar ya damu already Nikam na manta da wannan shafin, Bari mu tafi it's getting late.

Ina fadar haka na fada mota ta na Barsu a gurin Dukkansu suna mamakin yadda na zama. Washegari aka Fara biki cikin nasara, tabbas munyi kyau nayi yadda nake so, haka aka jera kwanaki uku kafin aka kai Amarya, ban wani tsaya ba na sulale saboda kukan da Rafee'ah take kuma bana son haduwata da mukhtar.

Bayan Kwana uku na huce gajiyar biki se nacin Rafee'ah akan Yaushe zanzo to Yau dai na shirya naje muka yini, naji ta bani Sha'awa musamman yadda suke nan nan da juna, Nikam ko zan taba yin aure? Ko zan dandana wannan rayuwar haka kullum nake wannan tunanin, sallamar Anas ce ta katse min tunani na, shi kadai ya shigo Ina kallo Rafeey aka kashe mishi ido kafin ta nufe shi, se kuma ya juya ya fita, tana Zama se gashi da mukhtar, ta gefen ido na Kare mishi kallo yayi baki yayi Rama kamar ba MK dana sani ba, zama yayi kujerar dake facing dina yayinda shi kuma ya zauna gefen matarshi suna wani murmushi wanda yake nuna min tamkar komai is set up, mukhtar ne ya fara fadin

Hajiya Nadia Ashe kin gama school

Da murmushi nace

Wallahi kua

Yaji dadin ganin murmushi na wanda baisan kawai faking nake ba yace

Congratulations, Allah ya sanya alkhairi

Amin

Na furta ina maida kaina kan wrist watch dina kafin na Mike ina fadin

Amarya, ango, MK ni zan wuce Allah ya bamu alkhairi.

A tare dika suka mike Anas na fadin

Haba tun yanxu

Murmushi nayi nace

Ina laifi yau baki daya gidan ku na yini, nima I need to go somewhere.

Rafee'ah kamar zata fashe ko magana Batayi min ba har suka rakani bakin mota kafin nace

Rafeeey chill, Meye abin fushin?

Tsaki tayi Wanda ya sani sake dariya kafin nayi waving dinsu na bar gidan, na rasa me yasa indai mukhtar na guri to bazan taba sakewa ba, haka ni Bana jin haishinsa amma inajin wani tabo cikin zuciyata da bazai gogu ba.

Kofar gidan Mameh nayi parking saboda ba nan zan Kwana ba gidan Anty zanje to inason karbar mata sako hannun Mameh, ko Mintina biyar banyi ba na fito hannuna rikeda Leda sede da mamaki ganin motar mukhtar tsaye bayan tawa, Yana tsaye ya harde hannayensa Yana kallona tareda sakin murmushi, dauke kaina nayi zuciya ta na fadin

Don't let him destroy you again!

To fa! Nadia have completely healed, ga mukhtar ya dawo, to fa me zai faru? Mu cigaba da kasancewa da Nadia Don jin yadda Za'a kaya!

Shatuuu ♥️

MATSALARMU A YAU! Where stories live. Discover now