Part 31

1.4K 176 6
                                    

Anas ne ya fara mika masa hannu sukai musabaha, kafin ya kalle ni yace

Yan mata har yanxu Bakiyi unblocking dina ba, saboda na kasa fitar da motar.

Kallonshi nayi sosae babu alamun wasa yake min saboda he's giving me a serious look, Amma ni nasan na bashi hanya to me ya faru kuma? Rafee'ah ce tace

Dama baki bude shi ba?

Kaina na mayar kanta nace

Nidai na bude gaskiya, sede idan wata motar ce kuma.

Kallona ya kuma Yi yace

Inason tafiya ya xa'ayi kenan?

kafin nayi magana Anas yace

Nadia kije ki Kara dubawa mana

Tsaki nayi raina a bace don nasan rainin hankali ne, ya za'ai yace banyi unblocking dinshi ba, mikewa nayi na dauki handbag dita sannan na dubi Hanifa wadda tuni ta Mike nace

Mu wuce kawai Daga nan, ku kuma Allah ya bamu alkhairi

Shi ya fara yin gaba Se Hanifa se ni a bayansu ina tafiya tamkar Bana so, a raina kuma ina tunanin kalar rashin mutuncin da zanyi mishi idan har banyi blocking dinsa ba, muna isa parking space Naga yasa motarshi yayi blocking dina, kallonshi nayi sannan na kalli motar nace

Ta ina nayi blocking dinka? Ina tunanin kamar Kai zaka matsa na fita tukun.

Murmushi yayi me kayatarwa amma da yake raina a bace yake ban ma ga kyaun murmushin ba, jingina yayi jikin mota ta yace

Abu nake son karba Daga gurin ki, Kingane?

Ya fada Yana dage min gira, ko kafin na bashi answer wayata tayi ringing hakan yasa na ciro ta sede ganin Anty yasa gabana faduwa, ina picking tace

Baby ya har yanxu shiru baku dawo ba? Jiranku fa nake zan karba sako

A hankali na Daidaita murya ta nace

Kinga mun fito yanxu zamu karaso ma

Kui sauri dai

Ta fada kafin ta katse call din, Hanifa na kalla se murmushi take Daga gefe, harararta nayi kafin na maida kallona kanshi se kallo na yake da wasu milky eyes dinsa a gurin

Ka daina kallo na, sannan ka bude ni zan tafi jirana ake

Bata fuska yayi yace

This is rude! Ya zakice na daina kallonki bayan Kinada abin kalla, ki......

Da sauri na katse shi saboda naga dan rainin wayo ne shi nace

Spare me Plxxxxxxxxxx, ka bude ni zan tafi baka jin Hausa ne

Na fada ina daga murya, dariya yayi yace

Kina bani phone number dinki I swear bazan Kara minti daya ba zan Baki hanya ki tafi.

Wani kallo nayi mishi Irin you're insane nace

How? Kai!

Se kuma nayi shiru na bude motar na shiga, Inata huci saboda Tunda nake ba'a taba raina ni ba kamar yadda wannan gayen yayi min ba, Hanifa ce ta shigo tace

Adda please ki bashi Meye ne number?

Dallah can rufe min baki, ke ki bashi taki mana

Ashe duka yana jinmu gani nayi ya leko yace da Hanifa

Little Sis rabu da ita, bata shirya tafiya bane number kawai no more no less kin gane.

Raina yayi tsananin baci zuwa lokacin, indai se na bashi number ta to tabbas Sede ya rike motar, budewa nayi na fito na aje masa key din nace

MATSALARMU A YAU! Où les histoires vivent. Découvrez maintenant