part 13

1.4K 186 2
                                    


Tunda Anty ta tafi America na manta da ita, dama ba wai na wani Santa bane, haka na tashi bansan wani abu waishi soyayya ba, ko kuma caring babu komai tsakanina da Mameh se zallar hantara, duka da kyara slight mistake zanyi ta hau dukana.

Inada shekaru takwas lokacin na shiga primary 3 wanda yayi shekaru uku da tafiyar Anty America kuma tunda ta tafi bata dawo ba shi daddy ne ma yazo sau biyu amma itakam tana can, Hanifa kam anayin Hutu ake kawota gurin Mameh don ta Saba da dangin mamanta, ina sonta sosae Tun a wannan lokacin nakanyi tunanin may be ni yar Baffa ce mama na ta mutu kamar yadda nake karantawa cikin passage a English text books da kuma story books. Wani abu da babu Wanda ya sani Ashe Baffa tun lokacinda aka sanar da cikin Anty ya samu hawan jini, shi kadai ya sani kuma bai sanar da kowa sede yana Zuwa follow up.

Ranar ta kasance Monday, Misalin karfe takwas na safe Nidai nasan ba Hutu akai ba Amma lokacin kowa baya fita amma ina tunanin workers na Nigeria sun tafi strike ne saboda Mameh ma ranar tana gida bata fita ba.

Dama Tunda nayi six years nanny dina ta tafi, na zama independent da kaina nake wanka, nayi wankin uniform both Boko Dana islamiyya, Wanda yayi min nauyi se na kaiwa mummy ta wanke mana nida Rafee'ah, hatta wankin toilet, gashi duka Nayi kai har girki nake saboda yadda Mameh ta dage tun ina jagwalgwalo har na Fara tabuka abin arziki. Kullum ka ganni a rame nake bana kiba, shima Baffa Malam bai cika fitowa ba, balle yasan me yake faruwa abu daya na sani kafin ya kwanta zai biyo ni har daki dayake I've my own daki ni daya se idan Hanifa tazo ne nake sharing da ita, zai tambayeni naci abinci? How was my day? Yaya school? What I learned new? Haka dai sort of questions wasu lokutan with all cheers zan bashi labari a times kuma ina kuka zance mishi babu, ganin yadda hankalinshi Ke tashi yayi ta fada idan yaga ina kuka yasa na koyi boye damuwa ta Sede idan baya nan baya kusa nayi kuka da haka aka gina rayuwata, na tashi da tunanin kowa azzalumi ne kowa bayada imani, duniya ba gurin dariya bace ko kuma gurin jin dadi.

Ina kwance kan gado gashi lokacin ana muku mukun sanyi saboda December ce, kawai naji ruwa me kauri a jikina, kunsan idan ruwa ya kusa kankara wani Irin kauri yake to shi Mameh ta watsa min a jiki, wani Irin ihu na saki na diro Daga kan gadon na saboda har ga Allah nayi zaton aljanu ne suka watsa min, hakan yasa na tafi dakin Baffa a million Ku kwace marathon race ake saboda gudun da nayi, ina shiga na fada kanshi Yana kudundune cikin bargo wanda its unlike him don idan ya tashi yayi sallah to karatun qurani yake wani Lokacin tare muke kafin kuma ya fita walk dinsa, amma saboda yadda nake a gigice yasa ban yi wannan tunanin ba, se rungumeshi da nayi ina fadin

Baffa aljanu sun zuba min ruwan kankara.... Baffa ka tashi sun biyoni!

Kirrrrrrrr haka naji yana Jan numfashi hakan yasa na Daidaita kaina na yaye bangon sede na tsorata da yanayin dana ganshi, he was restless and helpless, da kyar yake Jan numfashi, se zufa yake da duk sanyin da ake hakan yasa na kamo hannunshi ina fadin

Baffa na! Meye ke damunka? Tashi muje asibiti!

Gaba daya na gigice na rasa Mai zan mishi and to cut everything short he died at my hands, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Bansan mutuwa ba Amma haka na dinga jijjiga shi Sede shiru se na tuna malamin islamiyyar mu ya siffanta mana mamaci hakan yasa na tabbatar my only savior ya rasu, mutum kwaya daya tak daya soni tun kafin a haifeni, mutumin Dana dauke shi matsayin uba, mutumin....... Haka na fito a guje na nufi dakin Mameh wadda ta gaji da nemana ta koma daki Tana tunanin Irin dukan da zatayi min idan na dawo don Batayi tunanin gurin Baffa Malam Naje ba, hannunta na kama ina fadin

Kizo gurin Baffa..... Kizo Baffa

Wannan abin da nayi ya tabbatar mata babu lafiya Don tasan ko giyar wake nasha bazan iya hakan ba, hakan yasa ta nufi dakin shi cikin sauri na bita, sede kafin na karasa Naji ihun ta hakan ya tabbatar min Baffa Malam ya rasu. Daga nan ban kuma sanin Meke faruwa ba, na farka hannun Anty wadda ta zabge tayi Baki ta rame dukda bawai na Santa bane Amma akwai ramar da idan kayi mutum for the first time ya ganka zai tabbatar ka rame, kuka Na Fara ina fadin

Baffa! Baffa! Baffa!

Hakan ya sake dagawa Anty hankali ta dinga kuka Bayan ta rungumeni saboda ko a yadda ko a karyata nafi Anty sanin dadin Baffa Malam, nasha wahala kafin nayi coping da ranshi, kowa mamaki yake karama Dani nasan zafin mutuwa, to ya zanyi shi ne uwata da ubana I knew no one else except him.

Bayan rasuwar kowa ya watse, Anty ma ta koma wannan karan kukan da tayi Yafi na kowanne Lokaci Don ta tabbatar rayuwa ta Sede addu'a kuma, amma ya zatayi haka ta tafi ya rage daga ni se Mameh wadda take a gida saboda zaman takaba da take, a wannan lokacin na tabbatar duniya ba gurin jin dadi bace, ko aiki aka dakko ni karshen wahalar da zanyi kenan, da safe ko nace asuba ina tashi zan Fara da gyaran kitchen na Dora breakfast, Nayi sallah da wanka sannan na gyara tsakar gida dakinta, dakina da parlour. Sannan na tafi school, wani Lokacin bana fahimtar abinda ake koyarwa, ni nasan inada brain amma xulimin komawa gida da abinda zan tarar yasa kwata kwata bana fahimtar komai, kullum idan result ya fito ina last 10 Rafee'ah kuwa Tana first 10, babanta sosae ya damu saboda yadda Anty itama hankalinta yake a tashe ganin yadda performance dina yake hakan yasa mummy(Bilkisu) da Abhi(Hammad) suka je school ganin proprietress da kuma class teacher dinmu, an tattauna sosae inda Anty Jane class teacher dinmu tace

Nadia is very intelligent kawai dai a gida akwai Abinda yake damunta, kamar tana da damuwa saboda most time ana lesson se tayi shiru tayi ta tunani kuma she's too young Tana hakan zai iya affecting health dinta.

Haka su Abhi sukai alkawarin daidai ta abin, sun yanke shawarar dauke ni amma fir Mameh take tace

Seda na gama cin kashin ta sannan Za'a rabani da ita to baku isa ba, idan ma ita Mami dince ta turo Ku, ko ita tayi kadan ta dauke ta daga gurina.

Haka suka tafi jiki a sanyaye, daga baya suka samo mata me aiki hakan yasa na Fara samun sauki Da week days amma da weekends kam wannan house help din ta fini yanci, to inda aka dan samu sauki performance dina ya fara improving, kuma duk lokacinda naje gidan mummy ta dinga yimin nasiha akan hakuri kenan, haka rayuwa ta ta cigaba da gudana Dama tuntuni Abhi Ke biya min school fees, ko pant Mameh bata taba siya min ba, kuma har lokancin Baffa yana nan daram cikin zuciya ta! Na kasa mantawa dashi kulkum se na yi mishi adduar Allah ya yafe mishi kurakuranshi ya haskaka labarinashi.


Shatuuu ♥️

MATSALARMU A YAU! Where stories live. Discover now