Part 14

1.4K 183 2
                                    

My wattpaddians, how are we? Muna lapiya? Ya sanyi? I hope kowa is OK kamar yadda shatuuu take. I love you so much darlings

A Kwana a tashi a Kace babu wahala a gurin Allah haka na kammalla primary dina inada shekaru goma, anan na samu admission na Fara jss1 dina, Watarana na fita kofar gida Bayan na gama Lunch,  dayake Mameh taje wani biki, ina nan tsaye na hango abu kamar snail yana tafiya, nan take na tuna assignment dinmu da arts teacher dinmu ya bamu, take kuwa na ruga inda na hangoshi na tsugunna don dauka ashe mota ta taho a guje, gani na yasa yaci wawan birki wanda yasa na jiyo a tsorace sannan a birkice, hakan ya janyo hankulan samarin dake zaune kofar wani shop inda dama nan din gurin zamansu ne hakan yasa suka taso Baki daya suka yo kaina, shima driver din fitowa yayi ya zo inda nake tsaye, fuskata babu alamun tsoro saboda ko wani abu dukda cikin raina tsoro ne fal a ciki, saboda zuciyata a dake take ina ganin dukkan abinda zaayi mini am ready for it.

Wani cikin samarin yace

Ke dallah me kikeyi anan gurin? Shegiyar yarinya kawai

Wani ciki yace

Meye abin ce mata shegiya, Allah ya kiyaye ai Tunda bai buge ta ba Alhamdulillah.

Wanda ya kirani da shegiyar yace

Ba shegiyar bace, ko tanada uba? Idan tanada shi fadamin.....

Haka suka dinga cecekuce yayinda kawai abinda Ke min yawo da amsa kuwwa cikin kunnena bai wuce

_Ba shegiyar bace, ko tanada uba? Idan tanada shi fadamin....._

Ganin abin Yana neman zama fada yasa driver wanda Tunda yazo baice uffan ba se bina da kallo yake tareda sauraren shirmensu Don haka na dauki Wannan abun a lokacin, yace

Ya isa haka, whatever it's Tunda ban bigeta ba shikenan, Yarinya tafi gida abinki sannan kina kula.

Kaina kawai na gyada na wuce gida, zuciyata Cikeda haushin snail din da ban samu na dauka ba. Bayan La'asar sega Uncle bashir ya shigo wanda shima anan yake Zaune gidan mu, muna shiri ba kamar uncle kamal ba, bayan yaci abinci ya dubeni yace

Ya akai naga ranki kamar a bace princess?

Dayake haka yake kirana, nayi mamaki tunda ni ban kasance me dariya ba balle fara'a, kullum fuskata a hade take the only time xakaga nayi murmushi shi ne idan Rafee'ah Tana shirmenta saboda Rafee'ah is a comedian.

Uncle, idan akace da mutum shege me ake nufi?

Dammm! Gabanshi ya fadi saboda tambayar tazo masa unexpected, shiru yayi Yana chewing words dinsa saboda Kada Ya kwafsa, a hankali yace

Waye ya fada miki hakan?

Mameh haka take cemin, kuma yau......

Na kwashe komai na fada mishi, nanma kasa magana yayi kafin can yace

Kinaji ba, shege kawai zagi ne idan ba'a son mutum ko kuma yayi laifi ake kiranshi dashi kada ki Bari hakan ya dameki kinji?

Kaina na girgiza alamun ban gansu ba nace

Amma Mameh cemin take Marar asali wai Marar uba.... Dama Baffa ba shi ne baba na ba? Wani a waje yace wai banida uba idan inada shi a nuna masa

Kanshi ya dafe kafin ya Mike da sauri yana fadin

Kinga princess bari naje yanxu zan dawo

Bai jirani ba ya nufi part dinsu, hakan da yayi ya tabbatar min tabbas akwai abinda yayi breaking along the line, haka na zauna jugum Inata tunanin da ni kaina bansan me nake ba kuma banida wanda zaimin bayani Kai ko ni bansan me nake tunani ba.

Haka na cigaba da rayuwa ta Amma wannan magana tana nan daram cikin rai na, na kasa mantawa kuma bana tunanin zan manta. Bangaren Anty na tana America abinta har ta samu aiki acan matsayin banker, dama idan baku manta ba banking and finance ta karanta, lokacin ta kara haihuwa yara har biyu duka Maza, babban Mahmud me sunan Baffa ana kiranshi Asim se Zubair baban daddy Ashir ana kiranshi Abunnur , Tana zuwa amma ba akai akai ba haka take min aike akai akai na Santa dai amma bansan matsayinta ba.

A makaranta kam idan aka dauke Rafee'ah se Hafsa Bana kula kowa, bana yiwa kowa magana Dama magana ba Hali na bace don yan class dinmu ma bawanda yake kulani am always in isolation ko a class akai laifi to definitely Za'a ware ni don ansan bana laifi se a hukunta sauran.

Da wannan rayuwar da halayen na girma na kai shekaru goma Sha biyar, Amma idan ka ganni zakai tunanin shekara ta sha uku saboda kankanta, wannan lokacin ina ss1 kuma na Fara fahimtar Abinda rayuwa ke ciki, na fara fahimtar wacece ni da abubuwan da ake boye min.

Ina kwance kan gado hannuna dauke da qurani ina tilawa dayake Nayi hadda duka Tun inada shekaru Sha uku, na kammalla komai daga cikin Abinda ya kamata nayi, daga gefena Hanifa na Zaune tana saurarena se ji mukai

Ina shegiyar yarinyar nan, Dan ubanki kina ina?

A hankali na rufe qura'ani na mike don amsa kiran Mameh, ina Daga curtain tana shigowa, wani Mari ta sakar min a kunci tana fadin

Ba wanki na sakaki ba? Shi ne kika xo kika kwanta Ke isashiyar ko? Wannan shi ne illar DAN SHEGE!

Tunda ta Fara magana ban kalleta ba se hannu na dake dafe kan kuncina ina jin yadda azabar Ke radiating cikin jikina, amma jin ta kirani da 'yar shege Yafi komai yimin ciwo, Dama ta saba tayi min abu naki kuka, ko kuma nayi mata banza, yau ma rabe ta nayi zan wuce ai kuwa a harzuke ta rufeni da duka da cord wire dake hannunta, Tun ina dakewa har na fara ihu ina kuka, Hanifa ta taho da sauri tana fadin

Haba Mameh Adda Nadia ki Ke duka haka?

Ta fada tana kuka, Mameh kam ko kulata batai ba ta cigaba da dukana, seda ta fasa min baya tukun ta bar dakin Tana fadin

Kuma Wallahi minti biyu na Baki ki wanke idan ba haka ba se nayi miki fin na yanzu.

Kuka sosae nake wanda ban taba yin Irinshi ba, inajin na gaji na tsani rayuwa ta, mikewa nayi ina layi na nufi inda dusters din suke, Hanifa ta biyo ni tana fadin

Adda, ki bari zan wanke kinga jini bayanki.

Ban kulata ba, kawai na debo su na fara wankewa ina ta kuka, wani Irin abu nake ji zuciyata kunci take min, haka na gama na koma daki Hanifa na biye dani, seda nayi wanka sannan na fito don shirin islamiyya dukda na daina kuka amma har lokancin ajiyar zuciya nake, Dama Hanifa tuntuni ta shirya don tasan bazan mata magana ba, ina gamawa na dauki jakata na fita sede ina zuwa kofar gida nayi kicibis da uncle bashir zai shigo, Yana ganina yace

Haneey me ya samu Addar ki?

Inajin haka na Kara sakin kuka, Abinda hardly Kaga nayi shi ne nayi breaking gaban mutane, I prefer nayi daban idan na kebe, amma yau ankai ni bango.

Mameh ce ta dake ta

Inajin haka kawai na fice daga gidan, Rana ta farko a cikin rayuwata na Fara tuhumar kaina dalilin da yasa Mameh Ke treating dina haka, Naji inason sanin Meye asalina? Na fara jin bakin cikin abinda ake min, Sede waye zai fadamin?

Shatuuu ♥️

MATSALARMU A YAU! Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang