Page 5

606 50 1
                                    

*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*

    *SALIM ko SAMIR👬*

     *story and writing*
                 *by*
*Ayshatu(momin twince)*

   *Whattpad AishaApali*

          Page 5

*Wanene samir*

     Malam Aminu shine sunan mahaifin samir, da mahaifiyar sa mesuna lubabatu wacca suke kira da ummi, mahaifinsu yakasance mutumin kirkine sana'arsa kuwa shine d'inkin hula, samir yasamu kukawa da tarbiya da samun karatu awajan iyayensa dukda kasan cewar basuda karfi.

    Samir nada shekara bakwai a duniya mahaifiyar sa ta haifi 'ya mace, samir yayi matukar farinciki kwarai yace ummi nice zanna mata wanka inmata kwalliya ingoyeta har saitayi bacci,  ummi tayi dariya tace to yaya ai kanwar kace saiyanda kayi da ita.

   "Suna cikin hiransu ne malam aminu yashigo wanda samir ke kira da abba ya samesu samir narike da jaririya yana zaune,  dariya yayi yace yayan baby anya zaka bari wani ya d'auki babyn nan kuwa? Duk sukayi dariya. Samir yace abba meye sunanta? Abban yace ai yaya shizaisa ma kanwarsa suna, yanzu saika fad'a wani suna kakeso asamata me dadi? Samir ya d'anyi shiru can yace samira ummi tace Shikenan kuwa ga samir ga samira,  Abba yashafa kan samir yace to shikenan ya karbeta yamata hud'uba da suna samira.

    "Samir ya kasance yana son kanwarsa matuka bazaka tab'a ganin b'acin ransaba harsai inka tab'a kanwarsa ko ummi ce ta d'an bugeta saitaga ransa ya b'aci don haka kowa ke gudun ta b'ata.

     Samira nada shekara biyar a duniya a lokacin shikuma samir nada shekara shabiyu ya haddace qur'ani akayi musu sauka, mahaifinsa daman ya dad'e yana masa tanad'in inya yisauka yakuwayi bajinta matuka don saniya ya yanka masa aka hidima sosai samir ya kasance me alfahari da abbansa.

    "Bayan saukan samir da sati d'aya mahaifinsu malam aminu yakaanta rashin lafiya, abu kamarda wasa yasamo gaske ciwon cikene me tsanani yarufeshi, samir yaje bakin titi yanemo me taxi domin su kaishi asibiti.

   "Yana shigowa gidan yazo ya tararda ummi ta zuba tagumi akofar d'akin abban nasu hawayene kawai sukebin kuma tunsa d'aya bayan d'aya, samir ne ya karisa kusa da ita yasa hannu ya share mata hawaye yana fad'in ummi kibar kuka yanzu zamu kaishi asibiti zaisamu sauki Kinji.

    "Ummi cikin kuka ta d'ago rinannun idanunta dasu kayi jazir tace samir basai munkaishi asibiti ba kaje kakira liman kace yazo yanzu malam sa'i yayi saidaimu d'au.......... bata karisa maganarta ba samir ya shiga d'akin abban sa aguje yasameshi samb'al akan gadonsa ummi tarufeshi dawani zaninta,  a hankali yabud'e yaganshi fuskansa d'auke da murmushi fuskansa yayi haske, samir murmushi yayi yace alhamdulillah na tabbata abbana yanacikin rahamar ubangiji Allah yakai haske makwancinka abbana yarufeshi kamar yanda ya sameshi.

  "Yafito yasamu ummin su yanda yabarta tsugunawa yayi a gabanta yace ummi abba adduan mu yake bukata ba kuka ba malamin mu yace mamaci dakaganshi fuskansa tayi haske to asama sa ran yanada rabo a lahira.

  "Ummi tayi mamaki irinna karfin hali da laifin hankali na samir.

   "Samir yana fita waje ya sallami me motan daya d'auko ya isa gidan liman yayi sallama, bayan yafito ya shaida masa abinda yafaru, liman hankalinsa ya tashi sosai yashiga cikin gida ya fad'a ma iyalansa don haka suka d'unguma zuw a gidan malam aminu.

   "Bayan anmasa sutura aka masa sallah akusa da masallacin anguwar mutane harkan titi yaga jama'a harda malaman samir duksun hallara don mituwarsa tazaga anguwar cikin k'an k'anin lokaci, wannanne yakara tabbatar ma samir babansa nada rabo da izinin Allah.

SALIM ko SAMIRWhere stories live. Discover now