Page 4

553 44 2
                                        

*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*

    *SALIM ko SAMIR👬*


    *Story and writing*
                   *By*
*Aysha(momin twince)*

   *whattpad AishaApali*

_Wannan shafin nakune gaba d'ayan marubuta, kuna namijin kokari wajan isarda sakonni ga masu karatu Allah yakara basira, zakinhannu, karfin eyes ameen._

    *Inayinku irin sosai d'innan BRILIANT WRITER'S bazan gaji da mika muku jinjina ba innace ku inanufin ni innace ni ina nufinku Allah kara had'a kawunanmu ameen*

     *Soyayya dad'i tafizuma dad'i masoyan juna kuna burgeni amintarku tada bance I solute u👮 *Ummiexy  and emnoor*
Tagwayen juna Allah yabarku tare inamuku fatan alheri dear👌.

           Page 4

     Salim nakwance yanata sharara bacci hankalinsa akwance mujahid ya yashigo d'akin rik'eda sandansa yana dingisawa ya d'akama salim duka abaya yana fad'in tashi tashi kagawani abu.

   "Agigice salim yatashi donya razana da irin wannan tashin da mujahid kemasa.

    Yace kai meye haka inace lafiyanka kasanfa banaso ina bacci a tasheni ko balle kwana biyunnan nafad'a muku banajin dad'in jikina.

     "Mujahid yace yanzumma dolece tasa na tasheka ka kunna TV kagani tashan labarai, mtsss mekuma dangani akan haka daman katasheni nasan be wuce kaga anatakan nuna wannan fashin damukayi  a bank bane wannan ai anriga anwuce wajan kyaleni nayi baccina.

    "Mujahid cikeda rud'u yace to yanzu ansamu wanda yayi fashin shi ake nunawa.

   Salim ne yace whattt wani irin ansameshi bayan gani a gabanka?

   "Mujahid yace nima shine abinda yarazanani kunna kagani kafin sugama nunashi.

    Salim yakunna dasauri yana kunnawa samir ya bayyana akan TV yana durkushe akan guiwansa yatinda police ke gefe da gefensa kanaga ninshi kasan yabugu a hannunsu.

   Salim kara zaro ido yayi waje haryana murza idon don yana ganin kamar baccin ne yasashi yake ganin me kama dashi.

    Mujahid yakalleshi suka had'a ido yace salim kasan shine?  Salim da al'ajabi yaka yace bantab'a ganinsaba tunda nake gashi ba abinda ya banban tani dashi kuma, musty yace tunda nake bantaba ganin masu kama haka ba inba twince ba.

   Salim tashi yayi yaje gaban madubi yasake duban kansa dakyau yaga bega abinda ya rabashi da wanda yagani a TV ba yanda salim yakeda saje hakashima samir yakeda.

    Sunacikin wannan al'ajabinne saiga Mubarak da mustapa sunshigo a guje turus suka tsaya ganin salim,  Mubarak yace guy daman bakai mukagani ankama ba? Salim yace muma yanzu mukagani a labarai amma bani bane.

    Sukayi ta maganganu akaidai har baba yazo gidan dakanshi ganinsu duk suna nan yakuma tabbatar ba salim aka kamaba sai hankalinsa ya kwanta.

       "A b'an garen samir kuwa yahakura ya mikama Allah al'amuransa yasan shi kad'aine zai kub'u tar dashi.

   Ummi da samira sunfita ahayyacinsu tsananin tashin hankali,  bamasu ka d'aiba kusan anguwar gaba ki d'aya, kowani sallah akayi a masallacin anguwar nasu sai anyi masa addua, kowace rana kuwa sai anyi saukan qur'ani a masallacin wa samir Allah ya kub'u tar dashi.

      "Anmik'a case d'in samir kotu, yaune ake gabatar da me kara.

   "Bayan angama sauraran wani kara aka fara na samir.

Maga takarda yatashi yafara dacewa sai kara na gaba wanda ake tuhumar matashi mesuna samir da fashi a bank, sannan yajuya yamika takardan ma alkali.

   Alkali yakarb'a yaduba sannan yayi rubutu,  ya umurci lowyer na kowani b"angare ya gabatarda kansa.

      "Lowyer govnerty yatashi ya gabatar da kansa, alkali yanemi da lowyer samir ya gaba tarda kansa,  samir yace Yame shari'a banida lowyer ubangiji shine gatana.

 
         "Alkali yad'anyi rubuce rubucenshi yad'ago wata 'yar matashiyar  barister ce tamike tace ya me sharia sunana barister nana lowyer me zaman kanta inason zan kare samir da rokon kotu ta bamu daman tattaro shaidu kafin afara zama nagode tasamu waje tazauna.

        "Me sharia yace and'aga sharia zuwa sati nagaba sannan akai samir gidan kaso harzuwa satin daza adawo ba ayarda abada belin saba yabuga d'an sandansa kowa mike.

   Bayan kowa yafito ummi da mutanen unguwar  su samir dasuka halarci kotu suka d'unguma suka isa inda barister nana take tana kokarin bud'e motanta taji anmata sallama,  tajuyo da fara'a suka gaisa sannan sukayi ta mata godiya tace bakomai saidai zatazo tayi zama dasu saboda tasamu hujjojin dazata kareshi.

     Ahaka suka rabuda ita sukabata address d'in anguwar dasuke.

    "Kasancewar case d'in babban case ne 'yan gari kowa da abinda yake fad'a agari wasu na tausaya samir wanda sukasanshi wanda basusan shiba kuwa madallah suke cew suna Allah yatona asirin sauranma.

  
    **********************

Barister nana ce cikin shiganta na alfarma ta isa gidan yari office ne ogan tashiga ta masa bayani ta nemi izinin tattaunawa da samir akabata izinin haka,  yace amma brister wannan case d'in yaron nada d'aure kai saidai ince Allah yaba da sa'a tace ameen fa nagode.

     "Samir ne aka kariso dashi wajanta duk agala baice yazauna bece mata komaiba saidai yaga neta, sun d'auki lokaci bawanda yace makowa komai.

    Can brister tace sannufa malam sunana.... Yakatseta dacewa brister nana wacca ta d'auki alhakin kareni a kotu naganeki, saidai ince nagode da kulawarki amma batun zaki kareni karma kifara don bazaki iyaba wannan vedio d'in kawai insuka nuna ya ishi kowa shaidan cewar nine wannan d'an fashin.

   Allah gatan bawa me jarabtan bawansa alokacin dayaso akanwanda yaso shikad'ai zai kub'utar dani hardu niya sugane cewa bani bane wlh bani suke nemaba ya fashe da kuka.

     "Nana shiru tayi tashare kwallan da itama sukeson gangaro mata samir yamatu kar bata tausayi.

   "Cikin karfin hali tace zamuyi nasara samir da Allah muka dogara na tabbata ubangiji shiya turoni wannan kotun aranar donna temake ka donhaka inason ka nutsu kabani labarinka tundaga farko har karshe karka b'oye min komai.

SALIM ko SAMIRWhere stories live. Discover now