*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*
*SALIM ko SAMIR*
*Story and writing*
*by*
*Aysha(momin twince)*_This page is for you_
_BRILIANT FANS group,leema novels, surayyahm novel grp1, Alfahari novel group and ashmail novel_I great you all ❤❤
Page 9-10
Nana hankalinta yatashi dakalaman dadyn ta bata masan hanyar kofar gida ta nufaba, habib ne dayake kokarin shigowa ya tare ta yana fad'in "sister yaya dai ina zakije haka ko mayafi babu akan kifa.
Sai alokacin nana tadawo daga duniyar tunani data shiga.
Habib ya kamata suka shiga gida har d'akin ta yakaita ya bude ruwa yazuba mata ya bata tasha.
"Yace sister akan wanna case d'inne kikashiga wannan damuwar meya faru haka da kikaje asibitin daya sa kikeson kirasa tuna ninki?.
Nana tace habib bashine yasaniba dadyne yace bazan sake halartan kotuba akan wanna case d'in na samir.
"Habib yace whattttt akan me meyasa meye dalili?
Hmmm nana tace wanna tambayoyin mashi yakama ta muyi amman be bani daman hakanba.
Habib ne yatashi a fusace zaifita, nana tariko shi tace ina zakaje? Yace wajan dady don samun amso shinmu.
Nana tace a'a barni dashi yanzu yana cikin fushine saiya sauko nasan yanayine don tserardani daga hannun mugaye amman zan yi iya kokarina infahim tardashi harya gane, yanzu inkaje bazai fahimce kaba.
"Habib yace to shikenan gaskiya kiganar dashi tun kafin ma ya kafe akan maganarshi kinsan halin dady in ya kafe akan abu.
Washe gari da safe nana tashirya tsaf taje tagaida dadyn ta ya amsa bayabo ba fallasa, yace ina barrister zataje? tace dady zanje asibiti ne inda mahaifiyar samir haifeshi a inda nake tunanin zan samu hujjan cewar ba samir bane me laifi nafara tunanin kamarfa sud'in twince ne shine........... Da katar da ita yayi cikin wani irin kakkausar murya wanda bata tab'a jiba yace bakiji me nace bane jiya da ga yau na haramta miki fita koda kofar gidane.
Nana ta russunar dakai cikin sassanyar murya tace dady ammmmm......... Bari wajan yayi ya haura sama yajuyo yace indai nine ubanki to wannan itace hukuncina amma Inkinga dama zaki iya karyawa bejira amsar taba yashige d'akinsa.
***********************
Abufa wasa da gaske yacitura sunkasa shawo kan dadyn su, harta hajiya babba da hajiya karama sai da suka shiga cikin maganar amman kam ya kafe akan umurninsa ba wanda ya isa ya canza masa
Duk da haka nana bata karayaba tasa habib yaje asibiti tamasa kwatancen office d'in doctor d'in dayace zai taimaketa akan shiya je yadubo file d'in.
Abin mamaki da habib yaje likitannan yanuna bema tab'a sanin labarin wata barrister nana tazo wurin shiba yace sam bashi bane kuma bawani taimako da zai iya yimusu bama shiba kowama garama su hakura..
Hankalin su yakara tashi don yanzu basuda wani makaman dafawa.
"Habib beyi kasa a guiwaba yaje yasanar dasu ummi halin da akeciki, hankalinsu ya tashi matuka gashi saura kwana uku akoma kotu, Nana ko kofar gida dadyn ta ya hanata zuwa balle tasamu tayi wani abin kobe saniba.
Ranar Monday ranar ma'aikata yaune kuma ranar da alkali ya bayar da umurnin akara gaba tarmasa da samir aga bansa don karasa case d'in.
Sun isa kotu habib da ummi da samira da mutanen unguwa kowa jikinsa asanyaye.
Nana datake gida waya na kunnenta don tinda habib ya isa kotu yakira ta kamar yanda ta bukata tanason tasan komai akan abinda ake guda narwa.
Alkali yafara shari'a inda akasamu wanda ake kara wato samir bashida lowyer, kuma babu wani hujja da aka gabatar da rashin zuwan ta.
Hakan yasa lowyer govn yasamu daman dazai kawo suka akanta, yace ya keshari'a batazo bane don tasan basuda wata hujja dazai wanke samir duniya ta tabbar shine saidai yaki fad'an 'yan uwansa saboda taurin kai irin na d'an fashi.
Wannan d'an fashin da ake kira samir dashi yafi komai kona masa rai in aka fad'a yakan jishi harcikin kirjinsa zuciyarsa tana nasa suya.
Alkali yayi gyaran murya yace to la'akari da hujjojin da kotu tayi gameda hujjojin da aka gabatar a gabanta zata zartarda hukuncinta yanzu.
Kotu tayi tsit kamar ba bil'adama aciki kowa yanaso yaji hukuncin da alkali zai zartar.
"Wannan kotu me alfarma tayanke ma samir hukuncin shekara ashirin agidan yari, sannan samir zai dawoma alhaji kid'insa da yasata a bank, tareda tara na dubu d'ari biyu na wahalar da kotu da yayi nakim amsa laifinsa..
In masu karya basu gamsu da hukuncin ba zasu iya d'aukaka kara.
Kafin kace me kotu ya rud'e da hayaniya wasu na kuka wasu nacewa Allah shikara.
Samir zubewa yayi awajan yana wani irin kuka me bantausayi.
Ummi kam kasa motsi tayi, habib kuma yana tafaman neman metaima konsa da ruwa don samira tasuma.
Kotu kowa ya watse saura 'yan anguwan su samir ne dasu ummi anata faman ba masu ummi hakuri, suna kallo aka wuce da samir yana kuka yanace wa ummi bani bane zasu hukumta akan abinda ban aikata ba.
Kowa kuka kalamsa yasashi habib dayake ta daurewa yanzukam ya kasa zama yayi a gefen wata bishiya yaci kuka yatashi ya share hawayensa yace bazamu ta b'a yadda da wannan hukun cinba wlh sai mun d'auka ka kara.
Dakyar yasamu ya lallab'a samira da ummi suka shiga mota ya kaisu gida, yayi alkawarin daga yanzu shizai d'auki d'awai niyarsu tun dama yanason taima konsu samir ne bayaso..
Barrister nana sanda taji anyanke ma samir hukuncin sake wayar tayi akasa ya tarwatse wani irin sarawa taji kanta yayi tarike tana fad'in impossible...
Hankalinta atashe ta nufi site d'in dadyn su harzata tura kofa sai tayi turus donjin yana wata waya...........
_Allah sarki samir nikaina saida yasani kuka😭😭_
*Fans ya bana ganin ruwan coment ne, gaskiya inbakwa comment bazanji dad'in cigaba ba*
YOU ARE READING
SALIM ko SAMIR
Mystery / ThrillerLabarine akan rayuwan wasu samari biyu masu kama, mecike da tausayi, da shiga kunci arayuwa.