Page 3

568 52 1
                                    

*⚜BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION 🖊*

     *SALIM ko SAMIR👬*

      *story and writing*
                  *by*
*Aysha(momin twince)*

   *whattpad AishaApali*

                  Page 3

    "Aka d'auki state ment d'in samir duk da dai sunajinsa ne kawai bawai don suna yarda da bayanan nasaba.

    Kamar yanda yamusu musu kwatance basukuwa sha wahalaba suka gane gidansu don anguwar ba babban anguwa bane kuma kowa yasan waye samir kasancewar shi mutumin kirki ne.

      "Wani tsukeken gida ne aka nuna musu akace nanne gidansu, suka tsaya daga kofa sukayi sallama aka amsa musu,  wata budurwa ce tafito tana tambayar ananne ake sallama?  Sukace mata eh nanne,  ganin su da kayan 'yan sanda dasauri tace lafiya?  Sukace nanne gidansu wani yaro samir? tace eh nanne officer me yasamu yaya samir d'in?  Yace kimana magana da megidan kwaji koma meyene.

   Da gudu tashiga ciki tana kiran ummi ummi kifito 'yan sandane sukazo maganar yaya samir,  a bayangida take jin 'yan sanda tafito dasauri tajanyo mayafinta akan kofa tace muje maza meyasamu samir d'in kuma innalillahi.

     "Tace sannunku dai officer meyasamu d'ana don Allah?  Basu amsa mataba sukace da dai zaifi kyau muyi magana da mahaifinshi,  ummi tace mahaifinsu yarasu nine uwa nine ubansu kafad'amin meyafaru.

    Sajent sani yace to hajiya d'ankidai d'an fashine sunje sunyi fashi a banki fuskansa  ne kawai aka gane saiyau Allag yasa shi d'inma akasamu kamashi shine yaki yafad'i inda sauran suke gashi........be karisa magana ba ummi tace karyane karya kukeyi d'ana ba b'arawo bane d'ana mutumin kirki ne baya d'aukan kayan wani inba nasaba yanada sana'arsa daya dogara dashi kowa yasani,  wlh ba samir d'ina bane kuje kinemi b'arawon ku awani waje saita fashe da kuka.

    Samira dake gefe sai faman kuka takeyi tunsanda akafara bayanin.

   Yace mufa hajiya munzone mutanba yeki ranar 5/11/2018 da misakin karfe goma na safe yaronki yana ina?  Tayi shiru tana tunani samira ce tayi saurin cewa ranar dana dawo daga makaranta ne kuma wannan ranar tunda yaya samir yaje tasha ya d'aukoni besake fitaba.  Ummi tace kwarai kuwa officer wannan ranar samir ko aikinsa na taxi be fitaba.

     Bayansun gamajin jawabin su samira sukace to suzasu koma kuma hajiya daga yau kisani d'ankin d'an fashine sun saci kud'a d'en mutane dayawa sai yau dubunsu yacika.

   "Ummi tace office d'ana baya sata nina haifeshi nafikowa sanin halinsa karku d"auki alhakinmu Allah bazai barkuba kuji tsoron Allah kusakemin d'a,  sajent besakece da ita komaiba yabar su awajan,  kaf anguwar suka zaga suna tambayar halin samir abinda yabasu mamaki kowa baya fad'in wani mummunan hali akansa mutane dayawa sunyi kuka dasukaji halinda yake ciki.

    " Samira da ummi sunkasa zama saboda basusan halinda yake ciki ba gashi basusan wani police aka kaishiba.

   Sallama sukaji suka amsa wani nakocin sune yazo yana musu jajen abinda yafaru yace wa ummi tazo suje taga samir d'in yabi bayan officers d'in yaga inda aka kulle samir,  ummi ta masa godiya sosai yace haba samir ai d'an mune duk abinda yasameshi mu yasama irin d'awainiyar dayake yi da yaranmu yana koyamusu karatu batareda muna biyansa ko sisi ba.


    "Sun d'un guma zuwa police station dattawan anguwan da matasa haka suka cika police station  duk saboda mutum d'aya, d.p.o yana cikin office d"insa yaji hayaniya tayi yawa yafito ganin station d'innasu acike yatsaya yana mamaki,  yaransa ya tambaya ko lafiya suwaye wa d'annan?  Sani ne yace yallab'ai mahaifiyar samir ne da mutanen unguwar su,  duk sunzo suncika mana kunne kuma sutafi sunki tafiya.

    D.p.o yasamu waje yazauna yace duk su nutsu sumasa bayanin abinda yakawosu,  wacece mahaifiyar bashi?  Ummi tace ganinan wannanfa yanuna samira tace ni kanwarsace.

    "Ya gyara zama yace kunsan meyasa aka kamashi ko?  Wani daga cikin dattawannan yace yallab'ai mundai samu labari, d.p.o yace kaikuma waye?  Wannan dattijon yace nine me unguwa yallab'ai munason kusani sam bashi ya aikata ba kusake manashi.

    D.p.o yace wannan kuma bincike ne zai tabbatar.

    Ummi cikin disashshiyan murya tace yallab'ai kutaimaka muganshi zamu masa magana inma ya d'aukan zaidawo dashi duk da munsan ba halinsa bane,  d.p.o yace kai copur musa d'au komusu vedio d'innan sugani nan aka d'auko akasaka musu sukaga yanda akayi fashin sukaga kuma lokacin da salim ya bud'e fuska me kama da samir.

    "Jikinsu gaba d'aya yayi sanni ummi hankakinta ne yakara tashi tabbas a vedio d'in data gani samir ne to tayaya ma hakan zata kasance?.

   Me unguwa beyi kasa a guiwaba yace "officer tabbas munga vedio amma wannan bazai zama mana hujja dazamu yarda samir d'inmu ne ya aikata ba akwai masu kama dayawa a duniya.

    D.p.o shikanshi yanzu yafara kokwanto dayake mutumin kirki ne yace kuyi hakuri zamuyita bincike har Allah yasa agano gaskiyan nikaina jikina yana bani akwai wani abu, amma bincike ne zaitabbatar mana da gaskiyan sa yanzu zamu mika case d'in kotune acan za'a karisa sharian saikuyi kokari kunema masa lowyer me kareshi.

   "Ummi tace bamuda kowa bamuda komai Allah ne gatanmu samir shine gatanmu,  Allah natare dashi koda lowyer koba lowyer.

   "Kutaimaka muganshi yanzu, d.p.o yace afito musu dashi, anfito da samir arirrike ko tsatuwa baya iyayi jikinsa duk jini fuskansa akunbure, yanda suka ganshi yasa hankalinsu ya tashi kowa sai share kwalla yakeyi samira tarungume yayanta tana kuka tace yaya meka musu wlh kaiba b'arawo bane baka taba ciyardamu da haramba hasalima ka tsani mecin haram wannan wani irin jarabawa ne yasame mu.

    Samir kallonsu kawai yakeyi baya ko iya magana,  da k'yar yabud'e baki yace ummi bani bane wallahi bani bane kifa d'amusu ban aikata abinda suke zarginaba.

    Alokacin kowa yaji tausayin samir saidai wanda bayida imani

SALIM ko SAMIRWhere stories live. Discover now