Page 2

783 50 3
                                        

*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*   

 
*SALIM KO SAMIR👬*

       *Story and writing*
                  *By*
*Aysha(momin twince)*

  *Whattpad AishaApali*

           Page 2
Seema tana shirin kiransu kawai sai tagansu sun shigo,  ana ganinsu kowa ya kwakwkwanta sunduba  basuga alhajin ba seema ce ta d'an d'ago kai ahankali ta kallesu tanuna musu wani office da ido alaman yana ciki.

    Salim da mujaheed  Suka bankad'e kofan mujahid ne yafara shiga aikuwa aka harbe shi a k'afa,  dasauri duk sukayi baya salim ahankali yasake bud'e k'ofan ansake d'aga bindiga za ayi harbi ya buge bindigan daga hannun alhajin,  yasaita bindigan a makogoron alhajin yace kana magana zakaji alburushi a mak'ogoronka.

    Mit yayi salim yasa hannu ya d'auki jakukkunan ya kwace wayoyin hannunsu wayan office d'in manager d'in kuma ya yanketa tayanda bazasu iya kiraba yana fitowa yasa key a kofan.

Yana fitowa suka ja mujahid suka fice daga bank d'in a daidai wajan fita salim ya d'aga bakin fuskan sa sai yatuno ashe basu fitaba saikuma yayi sauri ya sauke. ahanyarsu takomawa suka cikaro da motan 'yan sanda da gudu sukeyi saisu ka rage gudun donkar su ganesu.

    Direct gidan baba sukayi,  suna isa baba yakira likitan sa cikin gaggawa yazo yayima mujahid aiki aka cire bulet d'in dake kafansa,  doctor din yace anci sa'a be shiga jikinsa sosaiba da kafansa bazata sake takawa ba.

     Baba ya dubesu d'aya bayan d'aya yace gaskiyan kune dole na nemo malam tun kafin abin yayi yawa yasan me akeciki,  salim yace gaskiya nima saura kiris nasha alburushi don shegene alhajin nan da bindigansa yake tafiya.

    "Wani mutum ne yashigo cikin falon tsohone saidai ba tsoho sosaiba,  dasauri baba yatar beshi yana fad'in yanzukuwa muke batunka ina shirin kiranka kuma saigaka kazo.

  Murmushi yayi yasamu waje yazauna yace nasan kuna neman nawa shiyasa nakariso.

  Bayansun gaggaisa yamike ya isa d'akinda mujahid yake kwance yashafa masa wani magani a inda aka harbeshi,  yace anjima nan zaitashi karkudamu.

 
    "Wannan malamin yad'auko wata gora da garin magani yamik'a masu salim yace kuyi wanka da wannan nakwana uku sannan daga yau karku sake bu fita sai bayan sati biyu.

    "Bayan sungama tattaunawar dazasuyi da baba sannan  yatafi.

    Tundaga wannan ranar basu fitaba kamar yanda malaminsu ya umurcesu.

     Acan b'angaren bank kuma alhaji hankalinsa yamatu kar tashi don asume aka kaishi asibiti.

  Police sunata bincike amma ba wata shaida dasuka bari, sai sukace akunna musu CCTV  camera na bank d'in,  hakan kuwa akayi aka kunna sunga duk yanda abin yafaru amma basuga fuskan suba.

     Harsun kama hanya zasu fita dasuri wani d'an sandan yajuyo yace sake kunna wa kugani wajan dazasu fita kamar naso naga fuskan wani.

   Aka kunna aikuwa sukaga fiskansa,  aka tambayi mutanen wajan ko akwai wanda yasan wannan fuskan kowa yace be saniba, sukace badamuwa zasuyi bincike indai suka sameshi zasu samu sauran ma.

    "Aka watsasu a labarai gari duk ya d'auka sannan ansa kud'ime tsoka akan duk wanda yasamo su.

   Salim da mustapa ne suke kallon news suka cikaro da labaran suka kalli juna cikin tsoro,  mustapa yace salim garin yaya haka ta faru? Salim yace nima kaina bansaniba alokacin kawai naga nabude fuska namanta munaciki.

    "Aikuwa yazama dole musan abinyi acewar mustapa.

   Kiran oga ne ya katsesu wato baba,  salim ya d'aga cikin girma mawa, baba ne yafara masa fad'a saboda abinda yagani a news,  salim yace baba muma yanzu maganar damuke yi kenan da musty bansan ya akayi haka tafaruba.

  Baba yace to yazama dole daga yanzu kazauna agida harsai kurannan talafa donkuwa kudin dasukasa duk wanda yaganka zainuna ka don haka kakiyaye,  ko satin da malam yad'iba muku yacika kaikam bazaka fitaba saikoma yazama normal, salim yace ba damuwa baba.

     *************************

      Tafe yake cikin motarsa na taxi yad'ibo fasinja matane su biyu a baya ya ajiyesu ya wuce.
  Yana kara gaba kad'an wani ya tsareshi da uniform na 'yansanda ajikinsa ya tsaya yace officer ina za'a kaika?, officer yakare masa kallo tsaf yafitoda waya a aljihunsa yayi d'an danne danne yamaida ta aljihu yace malam kaini office d'inmu na nan unguwar kasa yabude yashiga.

   Suna tafiya driver d'in yanata laziminsa don al'adarsa ce inyana tuki toyana tafe yana lazumi.


   Wannan d'ansan dan saikallonsa yakeyi acikin ransa kuma yace jibeshi saikace mutumin kirki yau aidubun ka tacika.

    "Saida suka iso wajan d'an sandan yafita yace masa Inazuwa banida canji ajikina yace masa to yallab'ai.

   Yana zaune cikin motarsa yaga police kusan biyar sunfito beko razana ba saboda yasan yanada gaskiya,  yaga sun iso wajan motansa kowannensu sai muzurai yakemasa,  yace yallab'ai lafiya dai?  Wanda ya d'sukoshi a taxi d'insane ya bud'e motar yajawoshi yace bawani rainin hankali daza kamana yaukam Allah ya toni asirinka b'arawon banza.

     Cikin tashin hankali kasancewar begane mesuke son fad'amasa ba yace waime kuke nufine daga kawoka saiku kamani mena muku kuke kirana b'arawo?.

     Tusa keyansa sukayi cikin office d'in nasu daduka akasashi a cell,  dukansa suke babu ko tausayi,  tunyana cemusu besan komaiba harya kasa magana salati kawai yakeyi yana allahumma ajirni fimusibati.

    "D. P. O ne yashigo cikin offic d'in yace lafiya wa kuka kama haka laifin me yayi?,  sukace yallab'ai wannan b'arawon ne dasukayi fashi a banki,  whattt yafad'a yanufi cell d'in yace kudakata da dukansa haka.

    "Kamanninsa harsun sauya saboda duka,  d. P. O yace kai meye sunanka? Dak'yar yabude baki don bakin yamasa nauyi yace SAMIR  sunana,  d.p.o yasake tambayarsa yace meye sana'ar ka?  Yace ni d'an taxi ne shine sana'a ta.

  D. P. O yace samir karkamin karya kafad'amin gaskiya kaida suwaye kuka shiga banki ranar 5/11/2018 inka fad'i sauran kaisai musake ka kayi tafiyan ka?  Samir yad'ago fuskansa yakalli d.p.o yace wallahi wallahi narantse dawanda raina yake hannunsa nibansan komai game da laifin dakuke tuhuma taba awannan ranarma da kuke fad'a banje ko inaba ina gida saboda ranar kanwata tadawo daga makaranta inba kuyar daba kuje gidanmu kutambaya.

   "D.p.o yakarewa cikin idon samir kallo ajikinsa saiyaji kamar samir gaskiya yake fad'a masa,  to inhar ba shibane waye tunda dai cctv camera shita nuna,  kai yaronnan Yanason yayi wasa da hankalinmu ne amma koma meye yanzukam ai yashigo hannu inyaji azaba zai fad'a gaskiyan.

     "Suka fito daga cikin cell d'in d.p.o yace kud'au bayanan sa da address d'in gidan nasu inaso kuje kutabbatar mana da abin da ya fad'a.

   Daya daga cikin officers d'in mesuna sajen sani yace haba yallab'ai karyace fa kawai dason ya wahalar damu gazahiri ai muta gana masa azaba harsai ya fad'a.

   "D.p.o yace haba sani ai inbaka iya kama b'arawoba saishi yaka maka kuje kuyi kawai yanda nace harsaimun kure masa karya,  sani yace ok sir.

SALIM ko SAMIRWhere stories live. Discover now