*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*
*SALIM ko SAMIR**story and writing*
*by*
*Aysha(momin twince)**whattpad AishaAPali*
Page 7-8
Barrister Nana asibiti tawuce kanta tsaye asibitin govn ne tayi tambaya aka kaita wajan wani gerni doctor.
Tasameshi ta masa bayanin abinda yakawota, hmmm nisawa yayi yace gaskiya barrister aikinkin babbane bazance bazan iya taimakon kiba amma shekarun ne dayawa alokacin ma banfara aiki a asibitin nanba.
Nana tace yallab'ai kataimaka wannan hanyarce kawai zata fiddamu daga wani tashin hankali da akasanya wani bawan Allah da bejiba be ganiba.
Suna cikin wannan zancenne aka nuno yanda akayi a kotu ashe har gidan TV sun baza shi.
Nana tace yauwa doctor kaga case d'in damukeyi kuma bashi bane.
Doctor d'in yayi shiru yace nikuwa kamar nata b'a ganin wannan mutumin, nana tace a ina ka ganshi? Yace eh to bana ceba naje wajan wani friend d'ina ne naganshi awata mota yazo wucewa sai motarsa ta gogi nawa ya lek'o yaban hakuri harmuka gaisa shiyasa ma na gane fuskansa duk da abin ya d'an kwanbiyu gaskiya.
Nana tace acikin mota na taxi kenan, yace a'a tab motar dana gansa aciki ai takai million biyu da kaganshi kasan hutu yazauna masa amman anan naganshi duk a rarrame ko wahalan hannun 'yan sandane yasashi zama haka.
Nana tace don Allah koza kamin kwatancen anguwar? yace ah bada muwa tunda kina neman hujjan dazaki kareshine.
Yabata address na anguwan yace ammafa belura da gidan da yashiga ba, tace ah ba damuwa zannema.
Dasauri tamike takama hanyar fita, likitanne ya dakatar da ita dacewan kidawo gobe sai inga dawa zan had'aki ya tayaki duba file d'in dakike neman, Nana tace ok to nagode.
A gaggauce take tafiyan sai sula gudu takeyi a mota mutane bata hanya kawai sukeyi wasu suna binta da zagi itakuwa ko ajikinta.Sai kiran wayanta akeyi amma bata d'agaba, batayi birki ako inaba sai a unguwar, tun daga kan titi tafara tambaya tana nuna hotonsa awaya amma harta kare anguwar tsaf bata samu Wanda tasanshiba.
Zama tayi shiru ta bugikan motanta shitttt..
Karan dawayanta keyi yasa ta d'aga taga ashe dadyn tane dasauri ta d'aga takara s kunnenta tana fad'in my dady yanaga kakira da number Nigeria kardai kicemin kadawo? Yace yes my daughter nadawo ina tajiranki baki dawoba, don haka kizo yanzu inajiranki, tace yes dady suka kashe wayan.
Ta tada motanta cikeda jin haushin rashin samun Wanda take nema tanufi hanyar gida.
Da gudu takarisa b'angaren dadyn nasu tana oyoyo da dady kusa dashi ta zauna, ya kalleta yayi dariya, tace I miss u somuch, yace kai banfa jimaba dis time banfi 1weak ba, tace eh hakane amma ai ko kwana d'aya kayi mu awajanmu shekarane.
Dariyan yake kawai yayi, nana tace dady ya kamar bakacikin walwala? Yace eh daughter naga wani case da kike yine yanzu a labarai amman bakisanar dani kina yiba bayan kinsaba duk sanda zakiyi case saikin fad'amin kice in miki adduan samun nasara, nana tace sorry dady wlh wannan d'in daga sama case d'in yasa meni kuma kaga number ka sai atakira baya shiga sai inkai kaneme mu."Yace eh amman aida innakira saiki sanardani ko balle irin wannan case me had'arin gaske d'anfashi nefa, bakya tsoron 'yan uwansa su bibiyeki? Nana tace dady nasaba yanzu da irin wannan case d'in kamanta watanni baya wani case d'in danayi akan wani yaron d'an siyasa wani irin barazana ne basu minba daga karshe nayi nasara, wanna ma Insha Allahu zanyi nasara da goyon bayanka.
Mike wa tsaye yayi ranshi a b'ace idonsa sunkad'a harta jijiyoyin jikinsa saida suka tattashi alamun tsananin tashin hankali da b'acin rai.
"Cikin kakkausar murya yace khadija banyarda ba inason ki ajiye wannan case d'in banyarda kisake wata bincike akaiba kibarsu sukarita a hikuntashi akan abinda ya aikata.
Nana cike da mamaki take kallon mahaifin nata be tab'akiran sunan taba saboda ita d'in mesunar mahaifitan sane amman saigashi yau yakira tasan lallai abin babbane.Cikin raunanennan murya tace meyasa dadyna meyasa bakaso inyi aikin lada kuma zarginsa akeyi amman bashi bane.
"Tsawa ya daka mata yace wannan umurni nake baki ba shawara ba a matsayina na mahaifinki banison karajin komai ficemin daga d'aki yanuna mata kofan fita.
"Nana jikinta har bari yakeyi don tunda take dadyn ta betab'ayi mata irin wannan tsawanba mawani ma bata tab'ajin yayiba.
YOU ARE READING
SALIM ko SAMIR
Mystery / ThrillerLabarine akan rayuwan wasu samari biyu masu kama, mecike da tausayi, da shiga kunci arayuwa.