*⚜BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*
*SALIM ko SAMIR*
*story and writing*
*by*
*Aysha(momin twince)**whattpad AishaApali*
*Ya Ubangiji!*
*Ka karbi tubanmu,*
*Ka wanke zunubanmu,*
*Ka amshi addu'o in mu,*
*Ka tabbatar da hujjojin mu,*
*Ka shiryar da zukatan mu,*
*Ka tsayar da harshen mu akan gaskiya, Ka yaye damuwar mu da duk wani mugun tunani daga zukatanmu.*
*Mun sani, kuma munyi imani, shiriya, kariya da rahama duk daga gare Ka suke*
*Ya Allah Ka samu acikin Inuwa aranar da babu wata Inuwa sai ta Ka*
_jinjina da gaisuwa gareku masoyana aduk inda kuke Wanda na sani sa Wanda bansansuba kune ni nine ku inba donkuba dabankak hakaba ina godiya masoya nima inasonku irin sosai d'innan_Page 6
bariter nana sai yamma takoma gida don tanata tattaro shaidan ta akan case din, gaba d'aya tagaji ta koma gida tasamu habib ma yadawo daga tafiyan dayayi.
"Bayan ta huta shima habib d'in ya huta tazaunar dashi ta bashi labarin halinda akeciki, hankalinsa yayi matukan tashi, yace sister nana wlh ba samir bane bashibane samir bazai taba aikata yakanba.
" hmmm nana tanisa tace habib kowa amsan dayake bani kenan kamar yanda kaima kabani yanzu, bashi bane..... Bashi bane..... Bashi bane to wayene? Wannan amsan shisuka kasa samu.
"Nana abin yafara d'aure mata kai takuma fara karaya da al'amarin.
*Wacece barrister nana*
Alhaji ado meyadi shine sunan mahaifinsu,yana da kamfanine na yadi shiyasa ake kiransa da me yadi.
Sai mahaifiyarsu mesuna hajiya habiba saikuma amaryansa rashida, yaransa biyarne, Nana itace babban 'yansa kasancewar basusamu haihuwa da wuriba sai habib da shamsu dukansu 'ya'yan hajiya habiba ne, yayinda itakuma hajiya rashida take da yara biyu surayyah da basma.
Suntaso yaran kansu a had'e iyayenma suna zaman lfy a tsakaninsu alhamdulillah.
*************************Barrister nana ne ta zuba takardu agaba sai faman dube dube takeyi saiga mahaifiyarsu ta fito Wanda suke kira da hajiya baba takariso har gabanta amman nana bata ma lura da mutumba, hajiyane tace barrister kenan inkina aiki mantawa ma kike da abinci ko breakfast d'in kirki bakiyiba yau gashi lunch d'inma yanda kika sa aka kawomiki haka kika barshi, in ciki da yunwa ai ba fahimtan komai zakiyiba.
Nana ta dago kanta takalli flate d'in abincin nata tace hajiya babba ai kwata kwatama namanta ankawo min abinci gashi har yayi sanyi.
Hajiya tace ba doleba tunda batsoronki yake jiba saiki tashi kije kid'ibi me d'umi, nana ta d'anyi mika tace hajiya bana jin yunwar nemafa da dai zan d'an samu tea dinki me da d'innan yaji kayan yaji to dashi zaifimin dad'in sha, hajiya ta kalleta yace iyeee kice dai kinason sani aiki, nana ta d'an sosa keys tace ah ni na insa insa big hajiya aiki ina nufin kifad'a ma larai me aiki yanda akeyi ta had'amin, hajiya tace hmmmm barina had'omiki tunda inason inga kinci wani abu, nana ce ta ce Yauwa sweet hajjaju hajiyana tafina kowa love you, hajiya ne takama hanyar fita a d'akin tana fad'in kyaji dashi dai kuma kitabbatar kinsha in aka kawo miki, nana tace angama hajiyata nagode.
Yace ranar dawowa kotu, kotu yacika tam wasu ma basu samu wajan shigowaba saboda yanzu labari ya zaga ko ina, harta mate d'in samir dasuka gama makaranta tare sun hallara kowa yanason yaga inda wannan shari'a zata kaya.
"Bayan alkali yashigo ya zauna kotu tayi tsit kamar ba mutane, saida alkali yayi 'yan rubuce-rubucensa yace a bayyanar da me laifi agaban kotu, kafin yace lawyoyi sugaba tarda kansu, duka b'an garen biyun suntashi sungabatar dakansu.
Lowyer govn ne yafara tambayoyi kamar haka.
Munaso muji menene sunan ka dakuma sana'arka, samir Wanda yagaba fita a hayyacinsa muryansa adashe yace sunana samir aminu, sana'ata shine koyarwa a wata islamiyya saikuma taxi danakeyi.
Barrister ne ya gyara rigansa yace to samir kace kai d'an taxi ne hakan yana nufin kayi amfani da wannan damanne don karinka ganin gidajen mutane kana bin bayansu ko? Barrister nana ce tamike tana fad'in ubjection my lord lowyer govn ti yanason nuna cewar samir b'arawo ne kai tsaye batareda wata kwararn shaidaba wanna kuma ba huruminsa bane, me shariya yace barister akiyaye.
"Barrister ne yace my lord wani kwakwaran shaidane da yawuce wannan vedio d'in dasukayi fashi a bank, ya mika flat d'in aka mikawa me shari'a.
Lowyer yabada umurnin ashigo a abinkallo asamasa flatet d'in, aka kunna kowa yana gani.
"Barrister nana ce tayi murmushi kome tagani oho, bayan angama kallon ta mike tace Yame shari'a inason abani daman yima samir wani tambaya, yace anbaki dama.
"Cikin takunta na kasaita Wanda bakajin sautinsa ta isa gaban samir ta karamasa kallo tace awannan ranar kana ina da karfe 10am na safe yace ina gida saboda tunda kanwata ta dawo saida nayi kwana biyu kafin nafita daga area anguwarmu kuma, nana tace samir kozaka iya nuna ma kotu damtsen hannunka na dama, barrister govn ne yatashi yace objection my lord me yakawo maganar damtse kuma awannan shari'an? Me sharia yace brister nana me kike so kinuna ma kotu?....
Nana tace glyame sharia bayan ganin wanna. vedio danayi na ga wani tabo baki ahannun damar Wanda sukayi fashin Wanda ake tunani samir ne shine nakeson samir ya nuna mana mugani.
Samir ya bud'e hannunsa na dama babu komai, lowyer govn yamike yace objection my lord wannan ba hujja bace watakila shafawa yayi yanzukuma ya goge donkar a ganeshi.
Me shari'a yayi shiru yayi rubutu sannan ya d'ago kai yace barrister nana kina da wata shedan bayan wannan? Nana tace ina dasu yame sharia in anban dama zan gabatar ma dasu me sharia yace anbata dama.
"Barrister nana tarinka shigo da mutanen unguwar su samir daya bayan daya ana musu tambayoyi duk amsan su d'ayane harda abokinshi habib shima yaba da shaida akan abokin nasa.
Me sharia yayi dogon nazari nawasu 'yan mintuna sannan yace ya d'aga sharia sai bayan sati biyu bawannan ranan yanason duk kansu bangare biyun su tattaro hujjojinsu do za ayanke hukunci aranar ahaka kotu ta watse.
Bayan anfito a kotune ummi sukayi wa barrister nana godiya habib ne yace tambayar da kikayi akan bakin tabo a hannun wancan mutumin akwai irin tabon a kafan samir na dama shikuma, ummi da samira sukace tabbasa samir na dashi amman shinasa akafa.
"Nana me tayi shiru tace ummi nifa inaji ajikina akwai alaka me karfi tsaknin samir da wannan d'an fashin don kamar tasu tayi yawa nima dana kura idone sosai ina neman hujjan kamawa shine Allah yanuna min wanna bakin tabom bayan wanna tabon bawani ban banci dana gani atsaka ninsu.
Ummi ce tayi shiru, nana tace ummi sanda kika haifi samir shikad'ai kika haifeshine, ummi tace shika d'aine na ahifeshi a asibiti, nana tace ummi zaki iya tuna asibitin donkuwa tabbas akwan abinda yake rufe nikuma Insha Allahu saina bankad'oshi.
Ummi tace kwarai don samira ma acan nahaifeta ummi ta fad'amata komai na asibitin nana tagirgiza kai tace yanzu ma kuwa zan wuce can, kushiga motan habib yamaida ku gida duk abinda akeciki zakiji ummi tace to mungode.
Habib ya kalleta yace sister all the best saikin dawo.
YOU ARE READING
SALIM ko SAMIR
Misterio / SuspensoLabarine akan rayuwan wasu samari biyu masu kama, mecike da tausayi, da shiga kunci arayuwa.