Once again salamu alaikumu habibties... I'm really enjoying Dix strike ooo at least nayi qiba. Here is anoda short in shaa Allah buh lovely story, I had d idea of this particular book years ago during my secondary school days.well it's not exactly buh definitely much better ma shaa Allah. Every picture I use in this book is not in relationship with the book, it's totally a fiction gaskia nothing is real about it and any coincidental resemblance to any true life story I apologise.the fiction is dedicated to ASMAH and WALEED for the everlasting love.
Mind u wAllah ur votes and comments will definitely encourage me.
Gaskia ***PG17***Note:Not edited
***Am finally home.... Iskan garin Kaduna daban yake a wuri na. Ina gaban mota Bala driver na gefe Yana tuqa wa don shi na sa ya dauko ni kasancewar nasan Ameer na office I don't want to distract him.
Mun iso gidan mu dake Yahyah road aka bude gate muka shiga. Kusan a guje na shiga side din Amma don ita nafi son gani a yanxu. Ban ganta a falo ba hakan yasa na shige can cikin dakin ta inda na ganta Kan sallayar ta tana sallah. Ji nayi ance
" ya waleed, sannu da zuwa"
Juyawa nayi naga wannan shedaniyar yarinyar suwaiba qanwa ta Kuma autar Amma nade Kan gado cikin bargo
"Ke Kuma Yaya haka? Ba scul ne?"
"Bani da lafia ne fa. Zazzabi Nike tun jiya"
Bayan na samu guri na zauna gefen Amma na qara kollon ta na ce
"Allah sauwake"
"Amin,Ina tsarabar Casablanca"
Ko kallon ta ban qara yi ba hakan kuwa yasa ita ma tayi shiru abinta.Amma na idar da sallah na rungume ta ta baya kamar ta goye Nike ji. I missed her alot.
"Ni fa waleed irin yarantar Kan Nan ba dariya yake bani ba" ta fada aikuwa tana dariyar
"Ammmmmaaaaa" na qara qanqame ta
"Kai tashi, dalla kamar jariri" ta fada tana yunqurin tashi sannan na sake ta.
Muka gaisa irin gaisuwar yaushe gamo ita ma fara'ar ta ya nuna cewa lallai tayi kewa ta. Muna zaune muna Yar Hira tana tambaya ta abubuwa Ina Bata amsa naji an daka min duka a baya da sauri na juya duk da nasan duk fadin duniya ba Mai min haka sai shi Amma ya akayi ya dawo daga office bayan ban Gaya mishi na dawo ba
"Shashasha munafuki to an Gaya min ka dawo tunda Kai bazaka fada ba"
Ban bashi amsa ba kawai rungumar sa nayi Ina dariya shima dariyar ya fara.
"Sorry twin brother wallahi I don't want to distract u from work" na fada bayan na sake shi
"Welcome home toh, amma u should have called bana komai yau"
A haka dai muka je side din Hajiyar sa Wanda ba yabo ba fallasa ta min maraba. Kishin da ke tsakanin iyayen mu Mata Bai taba shiga tsakanin mu ba.
Chalet din mu muka wuce Sanin Papa baya Nan Yana umrah shi da yayan shi. Nan nayi wanka na sa jallabiya sannan nayi azahar muka wuce dinning na ci abinci don Amma ta sa anyi setting table tuwo ne miyar kubewa my favorite da man shanu ga kunun gyada. I just love home. Muna hiran office da Ameer.
"Waleed ka dawo da result din ne?"
"Eh ai jiya ma na karba, kasan u should give masters a try it's fun a Casablanca" na qarashe Ina dariya
"Naaahhhh akwai wani program CFA da Zan fara a Abj next month exams din shi every June ko July ake yi a Dubai for three yrs,Ni I prefer professional courses u know,the one I regret is this iCan stuff,is too boring not like MBA gaskia. MBA is still my best very intelligent wallahi"
Nasan halin Ameer in aka fara maganar karatu ban San inda zai tsaya ba.muka koma daki na Kwanta nayi bacci zuwa la'asar na tashi.Rayuwar da nayi zuwa satin biyun da Papa ya dawo daga umrah ya mun dadi bani da aikin komai sai na raka Ameer office na dawo na kwanta nayi bacci na je wurin Amma muyi Hira sannan na dauko Ameer a office mu dawo mu hau Doki ko mu je chicken repeublic muci shawarma mu dawo aikin kenan
Sunana Abubakar Waleed, the second son of Alhaji Bilyaminu Dagash. Am 28.mu Yan garin maiduguri ne Amma aikin banki ya kawo Papa garin Kaduna. Bayan ya bar banki ya bude nashi kamfanin kayan gini inda ake order daga producer a bawa jama'a small retailers. Kasuwancin kuwa ya samu karbuwa don a qarqashin shi duk muke aiki.mu shida nee gidan mu amma a yanxu saura mu uku don Allah ya karbi ran babban yayan mu tun muna yara dalilin shocking na igiyar wuta sai qannen mu biyu Mata da suka Yi aure Fanna da khadija dukan su yayan Amma na ne don Ameer shi kadai ya rage wa Hajiyar shi bayan rasuwar yayan mu AbdAllah. Suwaiba ita ce last born din mu tana SS2 a Uncle Bado,don haka Papa ke shagwabata Ni Kuma hakan baya burge ni don Ni kadai ke iya dukan ta ba Kuma abunda zai faru.mahaifiyata Hajiya Aisha wato Amma ita ce amarya a wurin mahaifin mu inda Hajiya Falmata wato Hajiya ta kasance uwargidan mu. Wata biyu ne tsakanina da Ameer Wanda ya zama min Amini domin komai tare mahaifin mu yake Mana duk da rashin jituwar iyayen mu Mata Wanda watarana ke sa su nuna bambanci a tsakanin mu mu kuwa kamar ba don mu ake yi ba domin a yanxu hatta tsarabar da na yo wa Amma na irin ta sak nayo wa Hajiya. Ni computer engineer nee inda na dawo daga masters Dina a halin yanxu on the other hand Ameer ya kasance Accountant.
YOU ARE READING
Life Person💞 -Hausa Story
RomanceAllah kadai ya San jiya ya San Yau ya Kuma san gobe. A love story with a simple setting. Each and every swt story has a certain rough instance let's see what happens here. Alhamdulillah