To my good friends all over the world I love u all
💋💋💋Note: not edited
***Bayan shekara biyar
Na zama very busy yanxu Cox Ameer ya koma branch office din mu a Abuja Kuma Papa ba kullum yake zuwa office dinba. Kullum Ina koma wa gida to my beautiful resourceful wife and lovely kids. Asmah ta haifi twins daga Nan doctor ya tabbatar Mana da cewa ta samu matsala zata Sha wuya in aka ce zata qara haihuwa saboda wahalar da ta Sha wurin haihuwan twins din mu kamar bazata rayu ba. Ina tuna wa Ina office kawai Sammani Mai gadi ya kirani hankalin shi baya jikinshi
"Yallabai kazo gida madam ta Fadi"
Ji nayi Kai na ya Sara. Ba shiri kamar Zan fire na taho gida na tsinci Asmah cikin jini a falon Qasa a bakin stairs Sammani ya Rasa yadda zaiyi da ita da qyar take numfashi. Na ciccibe ta sai nearest hospital. Da qyar suka Hana Ni shiga theater room din. Hankali na in yayi million wallahi ya bar jiki na kuka nake kamar yaro. Nayi Dana sanin gidan sama a rayuwa ta. Nayi Allah wadai da barin mace mai tsohon ciki ita kadai a gida. A qasa na zauna Ina sambatun Allah ya tseratar min da matata Kar ya raba Ni da ita bazan iya rayuwa ba ita ba. An kusa awa biyu sannan doctors biyu suka fito suka yi congratulating Dina Akan an samu twins,Ni ba wannan bane damuwa ta matata. Itama suka sanar Dani tananan lafiya but akwai complication.Ranar Asmah tayi baccin da yaban tsoro don har na jira kowa na fada musu suka zo suka samu maza twins masu Kama da Papa dama nun niyyan ba zamu Gaya ma kowa ba Akan twins ne surprise kawai aikuwa sun Sha mamaki sai Hajiya take cewa ai dama taga alama. Kowa ya Gama abunda yake dai Asmah Bata tashi ba. Na tsorita na je wurin doctor ya sanar Dani cewa mahaifar ta ta ji ciwo sosai don a halin ake ciki da badin cikin ya Kai 9 months ba da za'ayi loosing baby sannan Kuma itan ma ba lallai ta sake haihuwan ba. Ni dai na ce toh Bata tashi ba yace min in kwantar da hankali na zata tashi. Aikuwa sai da tayi awa 18 lafiyayyu sannan ta tashi. I was proud of her, very proud. Sai da tayi sati biyu sannan aka sallame mu. Hamshaqin suna akayi a yahya road lokacin cikin Jidda Bai wuce wata biyu ba. Sunan Yara dai Bilyamin da Abubakar amma an musu laqani da fawaz da fauz.
Bayan Nan su twins sunyi 1 Asmah ta samu DE a KASU Business management. Har ta Gama three years sannan fauz da fawaz suka shiga nursery one a Mary Travis.
First day dinsu in school tare muka Kai su. I had to tek picture or them and AsmahSannan muka wuce nakai Asmah NNDC din anan tayi serving Ni Kuma na wuce office.
Yanxu haka NNDC sunyi retaining Asmah saboda First class student ce
amma three highest ta tashi sannan ta wuce gida a motar ta da na Bata Matrix. Fauz da Fawaz Kuma anty lami ke dauko su Cosin din Amma ce da auren ta ya mutu Amma ta dawo da ita kaduna don ba Nisa za'a iya taka wa zuwa scul din. Islamiya ma Yahya road na sa su saboda duk ba Nisa da gida so sai sun tashi direban Amma ya dawo da su. Yanxu yaran Ameer uku da Hafida Da Hamida sai jaririya Haneeda. A gwarinpa suke a Abj. I really miss him . Yanxu gida na ya koma unguwan sarki a Jabi west na samu wani flat Mai 3 bedrooms da parlor biyu sai BQ. Yanxu munyi Four years a can don wancan gidan ban qara renewing rent ba.
Yawanci yanxu sai past six nake dawowa gida. In na dawo already boys Dina sunyi wanka suna jira na muyi sallah Asmah ma ta ci kwalliya duk sai nayi hugging din su kafun na shiga gida. Ba laifi am richer than da amma Kuma wahalar ta ninka na da don yanxu ko gida na dawo in ba kashe wayata nayi ba an ringa Kira na kenan don yanxu mun fara contract din ginin hotels a estates da sauran su.
YOU ARE READING
Life Person💞 -Hausa Story
RomanceAllah kadai ya San jiya ya San Yau ya Kuma san gobe. A love story with a simple setting. Each and every swt story has a certain rough instance let's see what happens here. Alhamdulillah