💗9💗

38 2 0
                                    

To all my family and friends 💖💖💖

Note: note edited

Ansa ranar operation din mijina bayan likitocin sun Bani 15% survival assurance saboda a nasu tsarin akwai 85% mortality rate. Bani da aiki ko a office Sai nafilfilu da addu'ah. Kowa na Taya Ni azumi hatta amaryar baba na. Khalifa a gida na yake yanxu Yana SS1 a capital scul sai inyi dropping twins shima na Kai shi kafun na wuce office. Kowa in ya ganni sai ya ce na rame.

Ranar da aka yi operation din ranar jum'ah ce ba inda na iya fita don yaran ma ko scul na kasa Kai su. Waya Kan waya ko ya tashi Amma shiru. Sai da yayi kusan 72 hours sannan ranar Sunday da Rana ya Ameer ya Kira Ni cewar ya tashi. Nayi hamdala har da hawaye domin Ni ce na auna babban rabo. A hankali ya fara recovering. Kalmar shi ta farko ita ce ruwa da Haka dai har ya fara magana jifa jifa. Ko video call din da muka yi Yana ganin mu Ni da yaran ya fara smiling. Ya Allah it's a total different feeling.

Sai da akayi 6 weeks after aikin Yana karban kulawa ta musamman sannan suka sa ranar dawowa. Lahadin da suka dawo ta kasan ce Rana mafi tsayi ta a rayuwata. Bayan girkin da nayi muka dunguma muka tafi yahya road na ci kwalliya ta sosai leshi na sa ruwan toka da yellow din flowers sai na sa yellow din gyale da takalmi. Su Jidda ma sun iso daga Abuja. Motar office ce zata taho da su gida kowa na farin ciki Kai ka ce sallah ake.
Sai da la'asar suka landing Nigeria haka suka taho kaduna kusan magriba don daga airport suka taho.
Raina kamar zai fita tsabar dadi Yau ga mijina Yana dariya har Yana nuna ya gane mutane. Yana gani na ya tsaya Yana ta kallo na kamar zai tuna wani Abu ban San sadda na fashe da kuka ba ya rungume Ni shima kukan ya fara wadda bansan na shi dalilin ba. Haquri da hamdala kowa a wurin yake bamu sai a lokacin na tuna gaban surukai na nake. Sisters din shi ma kuka suke haka muka shiga falon Papa bayan an gaisa muka koma side din Amma mazajen mu suka nufi chalet din su domin wanka da shirya wa da sallah don yau a tsakar gida aka yi shimfidi ga fitilu da timtim qanshi na tashi wannan aikin anty fanna ne akwai da son abubuwan larabawa. Mu muka fara fito wa Ni da anty fanna muka jera abinci jidda suna can tana shirya Yara da anty ummi Hajia ma Yau ta shiga kicin don wani abinci da ta girka Ni ban taba ganin shi ba na San dai da garin shinkafa ne da kifi da Kuma veggies sai wasu spices na su na matan maiduguri. Sai da akayi Isha kowa ya fito. Mijina na fito wa a gefe na ya zauna Yana riqe da hanuna. Maganan dai babu murmushi kawai yake. Plate Daya muka ci abinci kowa na harkar shi Jidda ma na ga amarci ta ke ji da shi.
Har wurin 9 sannan aka fara watsewa daga qarshe dai mu kadai aka Bari don hatta kwanuka masu aikin sun tattare. A hankali na rungume shi Kai na Akan qirshin shi shi ma ya qanqame Ni. Mun Kai minti biyar a haka sannan ya ce min
"I miss u" maganar da ya fara kenan tun isowar su.
Ban San sanda na qanqame shi ba Nima na ce
"I miss u more"
Mun Dan dauki lokaci sannan ya raka Ni har falon Amma sannan muka Yi Sai da safe ya juya ya tafi. Na dade Ina tsaye a wurin kafun na shiga dakin na tadda Jidda ta na faman waya.
Wanka na shiga na fito sannan na canja Kaya zuwa marasa nauyi na sa hijabi na shiga side din Hajia don yi wa su anty fanna sai da safe don a can zasu kwana mu an bar mu a side din Amma da yara. Bayan na fito na nufi dakin anty lami don anan wasu yaran zasu kwana don yi wa twins addu'ah. Nan na samu anty lami na sallah twins da Mubarak da Salman din anty ummi a Kan gadon na tofa musu addu'ah na fita. Ban shiga gun Amma ba don nasan tayi bacci.

Bacci na so yi amma na kasa tunanin shi kawai nake wadda nake kyautata zaton shi ma Yana can Yana tunani na . A wannan Daren dai bacci barawo shi ya dauke Ni sai Kiran sallan assalatu ya tashe ni.

Da safe aka tashi da hidima don kusan  dukan mu a tare muka karya habeebee na Yana manne da ni Ina Dan tambayar shi a hankali Yana ansa min da eh ko a'ah. Har yamma in Banda sallah ba abun da yake raba mu har dare mijina ya kawo kan shi kusa da kunne na ya ce
"Me Sona... Mu dauki twins din mu mu tafi gida Koh?"
Kallon shi nayi na qara rungumar shishima ya qanqame Ni. Ai kuwa Kamar Amma ta Gane ta kalle mu ta ce
"Ku tashi ku tafi gida kafun dare ya muku sosai ko,ai yaran Kam gara su je makaranta. Sauran ma duk gobekowa zai watse ai Allah ya bada lafia"
Ba tare da na amsa ta ba na miqe na shige dakin anty lami na tarkato kan twins muka fito na dauko jaka ta mu ka tarar da sauran jama'an a waje inda na baro su. Sallama mukayi da kowa sannan ya Ameer ya qara nuna min kan magungunan mijina muka shiga motata bayan rakiyar kowa har bakin mota sai gidan mu OUR EMPIRE. A cikin mota kallo na yake Ina tuqi Nima hankali na na kanshi. Bayan bude gate ne me gadin ya iso har jikin mota ganin me gidan Suka gaisa sannan ya Taya mu shigar da kayan falo. A dakin twins muka fara yada zango inda muka Yi musu addu'ah na Kuma Basu tarihin sayyidna Umar (RA) Wanda ya kasance cikin tsarina tun bayan shigar su islamiya. Kallo na kawai habeebee na yake shi Yana murmushi in muka hada sai na ji kunya kamar wata sabuwar amarya. Har sukayi bacci ya ja hanuna sannan  muka wuce dakin mu ya zaunar da Ni a bakin gado ya tsuguna a gabana ya riqe hanuna wani tiririn qaunar shi na qara shiga ta. A hankali yayi maganar kamar me yi da kanshi
"Asmah thank you very much for everything. Allah ya saka Miki da aljannah"
Da qyar na iya cewa Ameen sakamakon wani kuka da naji ya tsaya min a wuya ga hawaye kwance cikin ido na. A hankali ya dawo kusa da Ni ya hada fuskokin mu numfashin mu na shiga na juna.ido na dago don in kalle shi hawaye suka gangaro min ba shiri naji ya lashe min su Wanda daga Kuma muka wata duniya wacce ban taba tsintar kaina a cikin ta ba.

Kwanci tashi yau mijina ya koma office bayan dogon hutun da ya samu Wanda da taimakon wani counseling psychologist ya samu duk wani guidance da yake needing bayan sessions 7. Rayuwa tafi da soyayyah ta ninka bana ma iya misalta girman alaqar tsakanin iyalina. Arziqi ya qara Albarka don mun bude foundation din mu Wanda muka sa wa WAFF foundation and charity Home.vwanda yake nufin Waleed Asmah Faux da Fahad . Kowa ya na zauna cikin rufin asiri a dangin mu cikin farin ciki da qaunar juna da zumunci Mai qarfi. Allah ya tabbatar da kowa cikin yalwa da annuri Ameen

Tammat bi hamdillah.
Yet another end
Who saw this coming?
Yeah we're done with ...
LIFE PERSON 💞

hey fellas!
I hope u enjoyed this book if no am sorry if yes all gratitude to God azza wa jal...
Watch out on yet another super story
ONLY PERSON 💞
I promise it will be better than personal person it self...
mmmuuAAh!!!😘😘😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 27, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Life Person💞 -Hausa StoryWhere stories live. Discover now