💗8💗

23 2 0
                                    


To every loving couple... Long live the love 💑💑💑

Note:not edited

Asmah's POV

***Kusan Awa hudu kenan banji habibi a waya ba, in hankali na yayi dubu toh ya tashi. Although ya ce min ba caji amma ai awa Hudu yayi yawa yasan dai bazan ji dadi ba. Juyawa kawai nayi Ina kallon su fauz da fawaz Wanda bacci ya dade da daukan su. Bacci nakeji amma bazan iya ba jira nake ya Kira Ni wallahi kukan da ya tsana shi Zan mishi. Kamar daga sama naji wayata na ringing na kalli wayar duk da nasan shine na kalli agogo qarfe 10 da minti 20. Sai da na Bari ta tsinke don nasan meeting zai ce.qara Kira yayi na dauka. Muryar da naji da ba nashi ba shi ya katse min sallamar da zanyi a shagwabe. Gabana naji ya Fadi,Kai na ya Sara a hankali na fara Kiran Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.
"Sannu fa. Don Allah meye alaqar ki da Mai wayar?" Shine maganar da naji kamar a mafarki I don't know wat to think
"Matar sa ce" shi ne amsar da naji na fada ban Ankara ba.
"Toh gaskia sunyi accident...." Daga Nan gaskia ban qara jiran me aka ce ba kawai tashin su fauz na fara numfashi na Yana neman dauke wa da suka tashi na fito da su fallo na shiga dauko hijabi kuka nake Ina Kiran sunan Allah da ya taimake Ni ya taimaki mijina. Mota muka shiga suna tambaya na Ina zamu ban Basu ansa ba. Ko kulle gidan ban tuna yi ba malam sammani ya bude min gate na fita ban San a wani speed nake tafiya ba kawai Naga na iso yahya road. Mai gadi ya bude na shiga. Da gudu nayi hanyar sashin Amma na ringa kwankwasawa jinta a qarqame. Anty lami ce ta bude tana tambaya ta ko lafia kawai kuka nake. Nan da Nan kowa ya taru ana tambayata menene su fauz sun rungume Ni sun fara kuka. Hajiyar Ameer ce ta tambaye Ni
"Asma'u Waleed ne wani Abu ya same shi"
Kallon ta nayi na daga Kai alamar eh. Nan take Papa ya hau Kiran layin shi aikuwa aka dauka Nan dai suka yi bayani salati kawai naji yanayi gabana ya qara Fadi shikenan na rasa mijina.
"Yanxu Zan Kama hanya kawai Bari na Kira Development mu tafi tare, hatsari yayi a Nan jaji suna asibiti"
Abunda naji kenan ya fada ya fita wallahi ji nayi kamar na bishi da gudu amma nauyin shi nake ji. Amma ma kuka ta fara da salati Hajia dai zaune jugum jugum tayi tana
"Yanxu in na Kira Ameer ma wani tashin hankalin ne"
Anty lami kuwa sai haquri take bamu sauran masu aiki duk suna jaje.
Rungume Yara na nayi ba irin tunanin da banyi ba har naji Ido na Yana min zafi tsabar kuka. Muryata ta dashe. Har asuba muna zaune a wurin ba wani canji Sai Kiran wayan Hajia da akayi yadda take magana alamar Papa ne ji nayi tana
"Toh Allah sa muji alheri"
Sai da na zo sallah na kwantar da Yara na don a jiii na suka Yi bacci. nayi alwala na hau sallah. Addu'ah nake Ina kuka roqon Allah nake ya min rahma ya bawa mijina lafia. Har qarfe taqwas sannan Amma ta shigo ta lallaba ni nayi wanka. Jallabiya brown ta bani na sa da hijabi na ko shafa Mai banyi ba Allah Allah nake ace mu tafi Naga mijina. Amma ta shigo dakin ta ce na fito mi wuce Garkuwa don sun iso Nan. Na fita na samu Yara na suna cin abinci,bamu tafi da su ba don da Hajia zamu tafi. Ko da na iso asibitin jiri na fara ji. Motar Ameer na gani hakan ya tabbatar min da sun sami labari har sun iso. Reception muka hadu da Jidda. Ina ganin ta wani kuka ya qufce min. Rungume Ni tayi mukayi kuka tana bani haquri. Ameer ko magana baya yi kawai kallo na yake Yana Hawaye.
Ranar dai wunin qunci nayi Karo na farko tun bayan rasuwar mahaifiya ta. Har la'asar muna reception sallah kawai muke fita yi. Sai wurin 5 wani baturen likita ya fito daga scanning room din ya yi referring din mu zuwa crest hospital Abuja. Nayi kuka har hawaye na suka daina zuba. Ai kuwa akayi azama Ameer da Papa da Amma suka tafi a mota da driver sai Ni da Jidda muka bi ambulance din da aka saka Mijina. Ganin shi da nayi hankali na ya tashi Yau ga gwarzon namijin Nan Wanda yafi kowa jarumta a Ido na kwance Bai San inda yake ba kanshi gaba Daya a daure take da bandage in baka mishi kyakkyawan sani ba ba zaka gane shi ba don fuskarshi ma ta kumbura tayi baqi. Zuciyata tai nauyi amma na tattara nitsuwa ta wuri guda na zauna inda nurses din suka nuna Mana daf kusa da shi ne. Hanun shi na riqe na kifa kaina a gefen gadon hawaye ke zirya a idona kawai na rufe Ido na fara addu'ah,a lokacinnan duk addu'ar da na sani sai da nayi tsabar neman dauki. Mun iso Abuja gari yayi duhu wurin 8 muka Isa crest inda a saukar da shi na bishi da kallo jina nake kamar Zan Fadi Jidda na riqe da Ni. Su Papa sun iso har sun Gama komai. Nan fa technology tayi aikin ta don tunda aka shigar da shi wani daki mu dai an bamu daki anan mukayi sallah sukayi inci abinci amma na kasa don ko magana bazan iya ba. Ni dai so nake inji halin da mijina yake ciki. Ina kwance Kan babban darduma a dakin qarfe 11 amma shiru ba labari Ameer da Papa ke ta shiga da fita ban San sanda bacci ya sace Ni ba. Sai da aka Kira Asaalatu Amma ta tashe Ni na hau sallah har aka Kira sallah aka shiga har gari ya dan yi haske. Papa ne ya shigo bayan dawowar su daga sallah ya zauna ya ce
"Kuyi haquri ku tafi gidan Ameer, anjima sai ku dawo sabida har yanxu likitocin Basu Gama ba balle su bamu fit back"
Hukunci ne wannan don Haka da Ni da Jidda da Amma duka ya Ameer ya tafi damu gidan Jidda a gwarinpa. Yaran ta nanan da ya bintu Yar aikin da Hajia ta kawo musu daga maiduguri. Anan nayi wanka Jidda ta ban kayanta na sa Riga gown. Yawanci Amma kadai ke magana a cikin mu,nikam kuka na kawai nake Sha nayi addu'ah.
Haka muka kwana uku a Abuja kullum mu wuni a asibiti ko ganin shi ba'a barin mu muyi doctors sai cewa suke result din kaza Bai fito ba na Rasa gane Kan al'amarin.
A kwana na hudu ne bayan munyi sallan azahar doctors biyu suka shigo dakin namu. Juyo wa nayi Ina kallon su. Suka gaggaisa amma Ni ban lura ko mun gaisa ba sbda halinda mijina yake ciki kadai nake so na sani. Baturen ne ya fara bayani
"U know,it's a very complicated case. He badly needs surgery but d surgery is very risky. He can survive it and he might not. But if he is given time and if he can fight d battle in his head then I think only time will heal him"
Kallon juna muke Ameer ya ce
"What exactly do u mean?"
Dayan Doctor n ya cigaba
"Look he means The Best medication he needs is time. Cox frankly his brain is in a stop right now he can't think he can't do anything useful but with time he'll survive it if at all he can fight it. Alternatively there's a surgery which is very not advisable because mortality rate is 89%. So I think he just needs time"
Har a wannan lokacin ban gane abunda suke nufi ba Kai na nasa cikin gwiwa na na cigaba da kuka na.ji nayi Ameer ya ce
"So we gonna Tek him home or what? Time as in how long? A month or a week?"
Shiru doctors din sukayi kawai suna kallon juna sai dayan su yace
"U can see him, he looks and he walks and anything aside that he is just a picture am sorry"
Da haka suka bar dakin da Papa. Ji nayi qafofi na baza su dauke Ni ba da qyar Jidda da Amma suka riqe ni muka je dakin hawaye na sun qare.
Ga dai Shi Nan idon shi bude Yana kallon mu kamar Bai San mu ba. A hankali na Isa inda yake na riqo hanun shi. Kallo na yake yi kamar ba shi ba hakan yasa zuciyata karaya yau a ce Waleed dina ya ganni dai na riqe hanun shi amma Bai ma San me nake yi ba.kuka na ji ya taho min sosai da sauri na bar dakin don wannan ita ce jarrabawa mafi girma da wata mace zata iya shiga.
Sauran ma kuka suke hatta Papa dawowan sa daga wurin likitocin tun daga qofar dakin ya fara kuka. Ameer ya rungumi Papa suka Sha kukan su.
A kusa da Mijina nayi daren ranar da Ameer Yana Dan leqo mu. Babban abun tashin hankalin da ya tabbatar min lallai yanxu mijina Ido da qafa kadai gareshi shine sanda Naga alamar fitsari a jikin sa, dubawan da zanyi har da bayan gari.
Oh Allah ka tsare bawa da wahala.
A hankali na juya shi na gyara shi na gyara wurin. Ameer kuka ne yaci qarfin sa ya fita. Shiga toilet nayi na wanke bedsheet da wandon shi. Da bargo na lullube shi. Ameer Bai dawo ba sai kusan after 30 mins da Kaya set 5 sweat pants 5 sai tops ma 5 sai boxers da singlet guda uku.
Kaya na sa mishi saboda duk wannan abun duk yadda ka nuna mishi ido nee kawai nashi baya ya ma nuna ya gane. A sannan na nufi reception a can na Yi wa receptionist bayani Ina so na ga doctors din Waleed Dagash. Ai kuwa tayi directing Dina zuwa 4th floor. A can na shiga office din Dr Santiago baturen da yayi briefing din mu dazu. Wuri ya bani na zauna nayi shiru sannan na ce
"Am waleed's wife. I need u to give me a detail account of what is happening to his life please"
Kallo na yayi sosai sannan ya ce
"Mrs waleed please relax. He's suffering an injury to his head I mean his brain. There's a vein that connects the two parts of his brain that is injured. So for that he can have a surgery but, the surgery is risky because the position of the vein is deep into his mendola oblongata so close to d vein connected to his spinal cord. But wit time the vein will heal and become normal if he eats and do normal day to day activities. So please just do him d favor of giving him time he'll heal"
A hankali naji hankali na ya fara kwanciya na qara kallon shi
"Doctor please how long will he suffer dis? How long will it take to heal?"
"Madam u see the normal time for a brain vein to heal is 7 years but it can be less and also it can be more"
Ban qara cewa komai ba Ina tunanin halin da mijina zai shiga cikin shekaru har bakwai Wai ma har ya iya fi Kai SubhanAllah ba zai Kai ba da yardan Allah.
A dakin na tadda su kowa na fadan albarkacin bakin sa Akan daga Nan India za'a wuce da shi.ya Ameer ne ya fita don nema musu Visa shi da Waleed da Amma.
A Haka muka Yi ta zama Ina bawa mijina abinci in Mai tsarki in ya Bata jikin sa. Cikin kwana biyu ya fara canja wa ya Ameer ya samo musu Visa. Dr Santiago ba yadda Bai yi ba Akan haquri za'ayi amma bamu ko lura da maganar shi ba. Mun koma gida Papa da Amma suka koma kaduna don Amma ta shiryo tafiyar next week ce.
A daki Daya muke da mijina.na mishi wanka nayi mishi shaving sannan na jawo shi dakin na shirya shi tsaf cikin jallabiya. Falo muka fita don cin abinci. A hankali na bashi abinci na bashi ruwa shi dai Ido ne nashi amma dadin abun baya musu. Duk tashin hankalin da nake tattare da shi na neme shi na Rasa saboda ba inda yake ma mijina ciwo sannan gamu tare wani sanyi nake ji.ina kallon su Jidda suna ta Mana kallon tausayi ban nuna musu na lura ba. Ni kadai nake mishi magana inyi ta Hira na Ni kadai
"Habibi kasan fauz da fawaz sunyi missing din mu. Get well soon mu koma gida. Bazaka mun magana ba?"
Kallo na yake. Ameer ya tashi ya bar wurin Jidda ma da hawayen ta ta bishi. Mun dade a falo Ina mishi hiran rauyuwar mu wani wurin nayi kuka wani wurin nayi dariya
"Ka tuna Randa muka zo Abuja ganin gidan su Jidda? Ranar muka je ShopRite har kayi fada da security don ya taba Ni mistakenly. U were that furious like ka cika zafi da yawa a lokacin, kishin ka yayi yawa" na fada Ina dariya. Kallo na yake.
Fuskar shi na shafa nayi kissing din shi.jan shi nayi muka shiga daki don Naga ya fara Jin bacci ai kuwa muna kwanciya yayi bacci sai minsharin sa nake ji. Allah nayi wa godiya na mishi addu'ah sannan na kwanta bacci.
4 na tashi na hau sallah.sai da akayi sallah har wurin 7 na tashi Daga karatun qur'anin da nayi.
Da na Isa gadon na samu ya tashi na Kai shi toilet ai kuwa yayi fitsari.na mishi wanka na zo na shirya shi,mijina dai ya zama yaro qarami Wanda komai yi Masa ake yi.
A falo muka tarar da su Jidda da yaran su duka suna breakfast muka gaisa yaran ma suka gaishe mu sai Hafida ta zauna Kan cinyar Waleed da niyyar suyi wasan da suka Saba taga shiru sai ta kalle baban ta
"Dad wat's wrong wit 2nd daddy"
Cikin qarfin Hali ya ce
"Feeda baida lafiya ne shiyasa baya son stress ki bar shi"
Jikin ta a sanyaye ta tashi ta Koma wurin zaman ta. Abinci na ba shi a hankali sai da ya qoshi sannan na ci Nima.

Ranar da za'a tafi da Waleed ya zo ji nake kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Na hada mishi necessary kayan shi da nasan za'a masa anfani da su. Twins din mu sun taho daga kaduna don yin bankwana da mahaifin su ba don ba zai dawo ba sai dai don rashin sabo da zama babu shi har sun Dan rame don aikin hajji ce kadai ta taba raba dayan mu da su. Tausayin su ne ya sani kuka don yadda suka ga daddyn su Kuma suka gane Bai ma gane su ba kuka ya sa fauz, Fahad Kuma rude wa yayi kamar Bai aminta da halin da ake ciki ba.

Ranar laraba jirgin su ya tashi zuwa India tare da papa da ya Ameer. Mu Kuma muka dunguma muka koma kaduna. gidan mu muka koma bayan munyi kwana biyu a gidan Amma. Kusan kullum sai ya Ameer ya Kira Ni video call naga Waleed Dina

Vote
Share
Comment... It need dat pls
Fi Amanillah

Life Person💞 -Hausa StoryWhere stories live. Discover now