🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*😭 *CURDLE*🙂, *GIGGLES*😁,
*AND MARRIEGE THINKS.*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*AM BACK AGAIN😘*
*SABUWAR SHEKARA SABUWAR RAYUWA....Happy New year💃💃💃💃💃*
*01*
---------Da gudu wata motar kirar corrolla X kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital *S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL* Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku taimakamin kada yata ta mutu ku taimaka" Nurses suka biyota aguje da abun daukan marasa lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga cikin mota tareda wata dattijuwan mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya karfinta tareda wasu maganganu marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour room,Hajiya karima takalli Momma tace"To ai sai kira danki shafaffe da mai ya taho ya girbi abunda ya shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani abun ne ya tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zata magana kenan Kamshin turaren azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba sunsan mamallakin kamshin.
Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin shigar suit Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya Karisa yana Fadin"Momma Har kun iso"cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin daya katsesu kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu Harara,tace cikin kallon raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata nakeson nasan Halin data cike,tundazu anshiga da ita bawani labari"Tsam dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame Hannunta tana Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Hadin da *SAKINATU* take ciki,cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kena dogon bufullatani mai cikar zati da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya mallaka tareda madaidaitan dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf dashi,zagayayyen sajensa yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa goshinsa dauke da tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine mai karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan Namiji mai cikar zati da Haiba *DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda yashafi mata wanda ke tare dashi *DR TAHIR* kenan Abokine kuma Amini garesa kuma abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr safwan din.
Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da zuwa Haji......."wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga da ita tundazu naji shuru'takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin yamike cikin sanyin jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din kenan Wata murya cikin karaji"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin Haihuwa babu wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala kai babu abunda kasani sai ci🙈kamar tuwo wlh bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin ihun da sakina takeyi bane.....Ina ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga gurin.
Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga uku"kan ta isa kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin wulakancin da danki yayi ma yata ammh kin gagara mai magana,saboda yagama cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki kam tayi magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u sakina Zata Haihu lafy"yana gama fadar haka ya shiga labour room. din
Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma kansa shower ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti talati so yake yarage radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office din yafada yana maida Numfashi.
Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta ba,baisan yaushe sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci ba shida mahaifiyarsa ba,baisan sai yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai sani ba,bai sani ba,yafada da karfi idanuwansa sun canza launi.
Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya kafin komai ya dinga dawomai daki daki kamar yanzu akeyi.
commet
And
ShareJanaf✍
YOU ARE READING
TA TAFKA KUSKURE
ActionLabari ne daya kunshi wata mata wacce bata daraja minjinta da aureta ba, tafi fifita neman kudi fiye da aurenta,wanda daga karshe take shiga halin nadama da kuskure domin jikakken labarin kubiyoni