TA TAFKA KUSKURE 04

742 38 0
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*😭 *CURDLE*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔






*04*



-----Tura kofar office din akayi tareda shigowa,Dr tahir ya kariso yana mai karewa Dr safwan kallo wanda ke kwance ruwa nadiga ajikinsa duk ya jika kujeran kwaya dayan datake office din,cikin azama Dr Tahir ya isa garesa yana Fadin"Dr Safana wht wrong with u"yafada yana mai dafasa,ajiyar zuciya Dr safwan ya sauke yana mai sauke gwaron numfashi bayan tsawon lokacin daya dauka yana tuna iya tsawon lokacin daYa dauka yana kunsan bakincikin sakina da uwarta.


Ya dago idanunsa jajir kamar garwashi yana bin Dr Tahir da kallo,kallo daya Dr Tahir yama safwan yaji mugun tsausayinsa ya tsirgamasa hannu yasanya yana jijjiga kafadarsa yana fadin"Dr Safwan Dan Allah Dan Annabi kayi....."Nagaji Nagaji Tahir wlh Nagaji"ya katsesa cikin kunar rai da kosawa"koda yaushe kaida momma kalmarku daya inyi hakuri shin bakuda wani abunda zaku iya gayamin sai kalmar Hakuri eye"yafada yanawani zaremai ido idanunsa sun tara kwallah,cikin sanyin jiki tahir ya karisa kusa dashi yana riko hannunsa,yana fadin"Babu...Babu safwan babu wata kalma data dace dakai bayan Hakuri,nasanka kacigabada da hakurin daka saba Allah nasane dakai"shuru Dr safwan yamai yana kallonsa kamar yana karantan wani abu atareda shi,kara damke hannunsa yayi yana jijjigawa alamar lallashi cikin kasala ya zare hannunsa ya isa ga wata durowa dake cikin office akafe ya bude sai ga wasu jeren kayan sun bayyana kai tsaye ya ciro su yakama Hanyan toilet Dr Tahir yayi zuru yana kallonsa sai dayaga yana shirin shiga toilet kana yace"ta sauka an sami DR SALE SAFWAN SAFANA  Da sauri ya juyo yana kallonsa kan mirmishi ya subuce masa zaiyi mgana kenan Dr Tahir ya rigasa dacewa"Both momma da bby are in good Health yanxu ma zan basu sallama su koma gida" gyada kai yayi kafin yace"thanks so much Dr....."Zan maidasu gida"Abunda tahir ya katsesa dacewa kenan kafin yafice mirmishi kawai Dr safwan yayi kafin ya girgiza kai yafada toilet.









Dr Tahir ya tura kai Dakin da"a ka kawo sakina bayan angyarata,ita da bbyn nata,Momma ta amsa sallaman tana Fadin"Attahiru sannu da kokari "Yauwa mommanmu Barkanmu fa"Yafada shima yana mirmishi karisawa yayi yana mai kara kallon babyn wanda kamar Dr yayi kaki,momma tadago tana Fadin"kaga danku ko,kungirma yanxu inashi baban nawa yazo yaga dansa mana"Tahir yace zaizo yanxu momma bari nadubata in babu matsala inmai daku gida"Momma tace"Alhamdulillah..."Gurin sakina ya karisa wacce ka zaune kan gado tana shan ruwan shayi yayinda Hajiya kari ke gefenta tana faman buge bugen waya"cikin mirmishi yace"Sannu madam munfa gode"Kallon raini ta watsama Tahir kan tace"Dole kace kungode kun hadani da aiki kun gudu"Yasan da wanda take shiyasa yace mata"is ur duty ai madam kema kinsani Haihuwa na matane ba maza ba kuma meye ribar auren soyayyah,A Haifi ya'yan soyayyah"yakareshe  Fada yana dariya kasa kasa tunda yafara mgana Hajiya kari dake waya take zagmai Harara yana kallonta ta kasan ido aransa yace'oho dai bazan dakuba dai" kasa bashi amsa sakina tayi saboda tasan waye Tahir gurin maida magana kamar dan Hausa bakwai.

..Ya rubuta mata maganin karin jini kafin yabata sallama saboda ta haihu lafy ko kari ba'a mata tana haihuwa kaji kwakwazo tsit tamike ras kamar ba ita ba yana tsokananta yasan ya kunnota shiyasa yaketa dariya,ita kuwa Hajiya kari jitake kamar ta shakeshi yacika iyayi ga tsinannan tadi kamar wani aku,momma tana ta zunduma ma Tahir Albarka har suka fito,har mota yarakasu momma dai ita ke rike da jikanta,har sunshiga mota Hajiya kari ta lego tace"Shi wanchan fa koda dan shege aka Haifa ai yazo yaganshi balle dan Sunnah ne kuma shi yadigasa"Tafada kanta tsaye Dr Tahir yagyara tsayuwa sanin matan bata da kunya ko kadan yasa kai tsaye yace mata"Wlh aikine yarikesa ammh kema kinsa bakasha wahalar diga abu da kanka ba,kuma ka banzarta dashi ba"Yafada yana kallonta ido cikin ido kasa bashi amsa tayi har dereba yajasu suka bar asibitin yana kallon motan yana killer smile kafin yace'kunyan mara kunya asara.








**********************

Hajiya mama dake zaune a farfajiyar flat dinsu tana tsinkan zogalanta datazo dashi daga safana radio tane takure kara tana jin gidan radion freedom ansa wakar sangaya ta daddage, tana bin abinta Mallam Ilaya mai baWa fulawa ruwane agidan,shine aikinsa shike zaune kusa da Hajiya tana zubamai labarin zamanta a safana sukaji hon din motan Mallan Habu mai gadi yayi gaggawan zuwa ya wangale get motar tasu tasawo kai zuwa parking space Momma ce tafara fitowa rike da baby a hannunta kafin Hajiya da sakina wacce tafito tana wani hura hanci kamar wata sakarya,Hajiya mama tai galala tana kallonsu Tunda Hajiya kari tafito taga Hajiya mama tawani hade rai,momma cikin farinciki ta nufi Hajiya mama tana fadin"Hajiya kiyi barka kinyi sabon maigida"Tsuramata ido Hajiya tayi tana kallonta sama da kasa kafin tace"Au....Wai tasauka ne na"aza bazata iya Haihuwa da kanta ba"tafada tana bin sakinar dawani kallon raini"jikin Momma yayi sanyi kafin tayi mgana Hajiya mama taci gaba da cewa'au ke kika koma mai renon kuma saboda sunmaidake wata sha katafi ko"tafada ranta abace Momma tadago zatayi magana taga mallam iliyasu ya tsuramusu ido da sauri tace"Mallam ilaya kunyi da fa "yana washe baki yazo ya amasheshi yana sa masa albarka shima mallam Habu yakariso yana sa albarka.





Hajiya mama tamike tawuce tana fadin"bari naje naji ubanwa zai mata renon dan"tana fada tawuce fuu sashen sakina wacce tun fitowarsu suka shige ciki,koda ta isa basu afalo cikin bedroom ta samesu sakina kwance share share Akan gado Hajiya kari nagefen suna mgana Hajiya mama tafado dakin,sororo suke binta da kallon Hajiya kari tayi karfin halin cewa"Haba hajiya da girmanki kina shigowa guri babu sallama"tafada tawani cin mgani Hajiya mama ta kallesu a wulakance kan tace"Ana sallama inda akasan darajan sallamane ba inda ba'asan darajarta ba"Cikin kunan rai sakina tace"gaskiya hajiya wlh kija girmanki,kan mene gaskia kija girmanki tunkan na tunkudesa"takareshe fada da rashin kunya Hajiya mama tace"Kin ma uwarki bani ba wlh da ita kikeyi don banace kinma ubanki ba don Kabiru yaron arziki ne,  nikam nafi karfinki fitsararriya kawai,kuma wlh kinemi mai miki reno hadizar baiwar  uwarkice  dazaki barmata rikon jika tareni d'a kuma ta reni jika bazai yuyuba tunda kika iya bin miji kikai ciki to kin ko san yadda ake reno"Tana gama fadar haka ta buga musu tsaki tafice.



Hajiya kari takalli sakinar tana fadin"wai wannan tsohuwar anya kanta daya"Sakina tace"lafiyarta kalau  Hajiya tsabar iskanci ne wlh,kuma shi safwan  din ke dauremata gindi"Cikin takaichi Hajiya kari tace"shegiyar tsohuwa mai shisshigin bala'i"Sakina ta karbe da cewa"ta karshe wlh Hajiya tshohuwarnan tana shigan hanci wlh"Tafada tana bayyana takaichinta.


Hajiya tace"barta mugama da jikanta tukunnah ita karamar alhakice.


Koda Hajiya takoma ta iske momma na tsaye tana jiranta kallonta tayi tana rumgume da baby kan tace"sai ki wuce ki kaimusu dan'su saura kizauna kina musu bauta tunda nasan ki zuciyarki kamar ruwan sanyi take"tana fadar haka ta tattara shimfidanta ta shige ciki,koda momma takai shi itace tamasa wanka tasama sakina nata,ko wankanma saboda lalacewa dakanta tashiga hajiya na kallonta ko ajikinta momma taga abun mamaki ammh sanin halinsu yasa taja bakinta ta tsuke.









.Commet
And
Share






Janaf✍

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now