TA TAFKA KUSKURE 24

721 32 2
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔






_*Congratulation for u completing ur amrzing special and educating Novels Naja'atou and Anty sainah Ummi meenal, DUK TSUNTSUN DAYAJA RUWA DA MUHIBBAT ina fata abunda kuka fada dai dai Allah yasa albarka kuskuren dake ciki Allah ya yafemaku hakika kun zuba dukkan basirarku da hazakarku wurin ilimatar damu da nishadar damu harda ma fadakarwa.ina So kusani kowani bugawan Numfashi na kuna cikin kalbina janaf na muku son kauna*_



*24*




Sai kuma takoma ta zauna tana cewa"Haba yama za'ayi safwan yayi aure haba nasan waye safwan mutum ne mai ra'ayin kanshi mace fiye da daya bata cikin tsarinsa"dariya tayi tace"Haba ni nasani"Kamar wata mahaukaciya tajawo waya tana dannawa ammh abun mamaki kowani dakika zuciyarta na bugawa takasa yarda da abunda kunnanta yajimata karfin hali kawai take.




Sukuwa tawagar Amarya suna shiga kai tsaye gaban momma aka direta haj.Mama tace"Samata Albarka Hadiza samata albarka da bakinki mai daraja"Momma tayi mirmishi tadafa kan safeena dake durkushe gabanta cikin hijabi tace"ina miki barka da zuwa ya ke yata ubangiji yasa albarka arayuwar aurenku da safwan"Tafada idanunta sunkawo kwallah anata amsawa da Amin cikin tsausayawa haj.Mama tace"Bar kuka hadiza da izinin Allah safeena haskece agaremu"Iyami ta amsa da "Insha Allahu maryamu sai ance gwara da akayi"Nan fa akayita addu'an zaman lfy agaresu gabakidaya sai ga haj.Mama tadauko turare ta hau fesema amarya ana sakin guda guri ya dau sowa kowa na fadin Allah barna ke Hajiya mama.

Sun dan jima ashashen su momma kafin hajiya ta musu jagora zuwa shashen Amarya suna tafe ana guda sakina na zaune taji hayaniyar na ta karuwa kuma kamar shashenta ake dosowa bata gama mamaki ba suka shigo haj.Mama agaba tana kwarara sallama Amarya da tawagarta suna baya Sakina dake rike da waya batasan sanda wayar ta subuce ba ta fadi kasan tayels din dake falon ba mike idanunta sun fito jikinta na rawa tana kallon jama'a dake shigowa da guda bata gama mamaki ba taga hajiya mama ta nufi dayan bedroom din dake kusa da nata tasa makulli zata bude Sakina bakinta na rawa tace"Am....Am....Nace ba'Tafada murya na rawa hajiya ta dakata ta juyo tana kallonta kan tace"oh...Na manta iyami ku fara isa da ita gun uwargida ku mika amana yadda ake na al'ada"Tafada harda dariya iyami tace"hakane tako ja hannu safeena dake rike da kawarta Aisha sai gaban sakina dake tsaye kamar mutum mutum aka dukar da ita inna husai ce tace"uwargida ga Amanar kanwarki nan ku hade kai ku zauna lpy da juna shine kwanciyar hankalin mijinku"tafada tana kallon Sakina,Sakina ta zura ma safeena dake durkushe gabanta ido tana so tababbatar da ba mafarki take ba Hajiya mama tace"Ta karba Allah ya tayamu rikewa ku karasa da ita ciki kunsan uwargidan akwai mulki"Tafada harda shewa jikin wasu yayi sanyi domin sudan fahimci cewa sakina bata cikin hayyacinta,haka suka mike suka rankaya dakin safeena iyami tace"Kishiga da kafar dama safeena kiyi addu"an mutuwa ce zata fitar dake"Gyada mata kai Safeena tayi hawaye na kwaranyomata.



Hajiya mama data tsaya abaya saida taga kowa yashige kana ta kalli sakina dake tsaye dafe da kirji tace"Ahayyyye....Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,nasan kina tunanin mafarki kikeyi ko? to kibude idanunki da kyau ba mafarki kikeyi ba da gaske Safiyanu yayi aure da Amaryarsa safeena itace aka kawota yanzu wannan shine amsa abunda kika taba fadamun watannin baya,kin manta ko? to bari in tuna miki kince in zan iya yima jikana maganin matsalarsa nace miki bani da ikon yayesa masa mtsalarsa ammh ina da ikon kawo masa wacce zata iya yayemasa"Hajiya mama ta dakata kan tacigaba da cewa"To yau shine ya tabbata....Ni maryama duk wanda yaci tuwo  dani miya sha Nasan ko ahaka na barki kingane kuranki"

Tana gama fadar haka tayi shigewarta dakin safeena tana fadin"ya banji guda na tashi bane kudaina daga kafa fa" Ai sakina lokaci daya taji wani abu ya dira bisa kirjinta ya gangara har sassan jikinta kafafunta suka hau rawa lokaci dayata zube akasa tana dafe kirji cikin karaji tace"Na shiga uku nalalace ni sakina aure"Tafada da karfi to dayake hayaniya yayi yawa ba wanda yajita sai yan aikinta dake kichen suka rugo suna tambayata lafiya abun mamaki sakina ce ke hawaye idanu biyu tana girgiza kai tace"Never wlh it can happen...Kai haba bazai yuyuba wlh sam"tana fadi hawaye na kwaranyomata masu zafi da radadi so take ta karyata abunda taji kuma ta ganine ammh saboda dakiyar zuciya takasa yarda din.

Suna ta mata sannu ko kallonsu batayi ba tamike dakyar tana dafa bango tashige daki tana fadin"Ina never 4ever wlh...Ni din kishiya tab wlh badai niba"tana fada tabuga kanta agaru ta fashe da kuka mai tsuma rai tana bubbuga hannunta agaru tana ta surutai"Na shiga uku ni sakina kardai ace da gaske ne sai kuma tayi shuru sai chan tace'kodai wasane wanine adanginsu yayi aure"Sai kuma chan tace'to ai hajiya bazata min karya ba "Sai kuma chan tace"Wlh da gaskene wayyo ni sakina na mutu na lalace tafada tana sulalewa akasa tana kuka mai cin rai.

_Ho ho chai chai diz girl kinada hauka taurin kan sakina na burgeni don ubanki kiga amarya da idanunki kiki yarda saboda muguwar taurin kai zaki yarda in kika ga Dr ya shige dakin amarya Addabun Arab inji mrs ibrahim_


Adakin amarya kuwa anata yaba dakin sabida yadda ya tsaru kowa sai san barka yake nan fa aka shiga shigowa da abinci kala kala da abunsha aka baje ana dibar girki ana hira safeena dai ko kadan bata ciba domin har yanzu kuka take muryanta ya dishe sai wuraren sha daya suka baro shashen safeena aka bar safeena da kawayenta sukuma iyaye suka koma barayin su momma.


Su kuwa su Dr tahir suna ijiye tawagar amarya suka juya gidansu tahir suka wuce domin chan suke daman suka iske ango na jiran dawowarsu sun tabbatar mai da amarya ta iso cikin aminci da salama ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Ina ta kiran wayarta tana ringing but no answer tahir ne yace"To sai kayi hakuri gobe in mun kaika domin amarya harmuka zo kuka take"Kuka safwan yafada yananuna damuwa Tahir yace"Eh...kukan rabuwa da gidamana Dr safwan yakoma ya kwanta yana cewa"Allah yasa tabar kukan nan cos bani son ciwon kai yakamamin ita'!shekewa sukayi dadariya Gaddafi yace"Shege nawa karka wani damu gobe zaka fanshe kaji abokina"Kara fashewa sukayi dadariya shikuwa banza yayi dasu kusan kwana sukayi suna mai shakiyanci.



abangaren su hajiya mama sunkwana cikin farinciki da Annushuwa haka bangaren ango da abokansa bangaren Amarya ma sai dai muce Alhamdulillah domin kowa yakwana cikin murna safeena ce ta kwana da ciwon kai saboda kukan data sha bangaren Sakina kuwa kwanan zaune tayi domin barci sai da kwanciyar hankali gashi wayarta taki tashi balle takira hajiya kari a idanunta aka kira sallah asuba idanunta sunyi ja sun kumbura saboda kuka ana shiga sallar asuba tazare key din mota ko mayafi bata saba tafice tanajin hayaniya adakin amarya ammh ko kallon gurin batayi ba tafice da sauri motarta tafada ta bata wuta afusace take dannah hon habu megadi dake sallah sai da ya sallame saboda firgici ai yana ganin Sakina cikin halin kamar mahaukaciya yayi saurin budemata tafice dawani mahaukacin gudu tsaye yayi yana dafe kai kafin yarufe yakoma yakara tada sallah.





.Katsina ta nufa da asubahin nan tana ta zuga gudu ahanya domin sam bata cikin hayyaacinta itadai burinta ta isa ga mahaifiyarta ko ta fada mata cewa karyane safwa baiyi Aure ba.



Koda gari ya waye ba wanda yabi takan sakina balle yasan bata nan abun kari mai rai da lafiya akayima bakin zurmi dakyar inna husai ta mtsama safeena taci abinci tasha magani ta kwanta don ta huta karfe biyu nayi masu kidan kwaryan da hajiya ta hayo suka iso tuni suka baje atsakar wuri suka fara sakin kida nan wuri ta hautsine hajiya mama ta shge fili tana tikar rawa ana mata manni tayi shar cikin leshinta ciki da alaku🤣🤣🤣kai yan zurmi sunga rawan banjo ai hajiya da chashe iya chashewa momma na gefe tana dariya domin tasan yau ranar farincikin hajiya safeena da Aisha kadai aka bari adaki su kuwa sauran suna wurin kidan kwarya ana cikin kidan ne saiga motar Dr Safwan tasawo kai cikin gidan shida tahir wanda tunda suka doso get din gidan sukaji kida na tashi .

Da mamaki Dr Safwan ya bude murfin mota ya fito wuri ko yadau sowan ga ango nan ga ango nan jin haka yasa hajiya mama tafito cikin fili ta nufi Safwan tanamai dariya.










Commet
And
Share






*Janaf*✍

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now