TA TAFKA KUSKURE 23

571 29 0
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔

_ina kike kawata kawar arziki kawar mutumci kawar anguwace mai matukar muhimmanci,kunsan me kullum sai mun hadu ammh ji muke kamar bama haduwa,kinsan kanki maryam muhammd ce kisani jamila na miki son kauna_





*23*



------Kai tsaye dakin Abbanta aka kaita wanda yake ciki domin anfadamai za'a tafi da safeena ita kadai aka bari dashi tana durkushe agabanshi sanye cikin dogon farin hijabinta tana kuka.

Abbah yayi gyaran murya Yace"Safeena kibar kukan nan hakan ki saurari nasiha mafi daraja da tsada daga mahaifinki wanda rashin sauraran zai sa kirasa abubuwa dadama arayuwarki"Yadakata cak kuwa kukan safeena yadauke Abbah yacigaba da cewa"Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya hakika yau ranar da amanarki zai fita ahannunmu yakoma ahannun mijinki to nasihata agareki yake yata shine na farko kiyi biyayyah zuwa ga mijinki ki kasance baiwa agaresa shikuma yazammiki ubangida kibisa sau da kafa domin aljannarki tana karkashin kafansa ne yake yata kada kizama mai bijirema bukatar mijinki akoda yaushe kisance mai goyamasa baya aduk abunda yasa gaba kada kisance mai gardama agaresa kuma kar ki kasance mai saurin fushi agaresa ki koyi mu"amala da kowa ki kyautatama yan'uwa sai kema ya kyautata naki ki girrmama abokiyar zamanki sai itama ta girmamaki domin keki ka auran mata miji kina kasa da ita sannan abu na karshe ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa kamar yadda zaki giramamu Safeena ki kaunaci Safwan da duk abunda yadanganceshi to inkikayi haka kin rabauta duniya wa lahira yata'yafada muryasa tayi rauni safeena ta fashe da kuka tace"insha Allahu Abbah namaka alkwarin baza kasameni mai saba umarninka ba'Abbah yace"Nasani Safeena bazaki bani kunya ba tashi tashi asada ki da dakin aureki na har abada"Yafada yana mikar da ita tana mikewa ta rumgumesa kam tana kuka hannunta yakama ya sanya mata karamin al'qur'ani izu sitti kafin ya kira iyami yace suzo su fita da ita shikanshi hawayene ya gangaromai na rabuwa da yarsa mafi soyuwa agaresu su iyami suka banbareta jikin Abbah da kyar sunkusa fita yadaga murya cikin rauni yace"abunda na baki ki rikesa da kyau duk halin kuncin dazaki shiga to karki manta dashi domin shi din haske da warakane ga duk wanda ya rikesa ku tafi ubangiji ya kaiku lpy yakuma sanya Albarka arayuwar rayuwanki"Yanagama fadar haka yajuya baya hawaye sun gangaro masa haka aka fice da ita tana kuka gun Ummi aka kaita wanda tun shigowarsu take kuka ana bata hakuri iyami tace',zainabu lokaci na tafiya kisama yarki albarka "Ummi tace cikin kuka tana dafa kan Safeena dake durkurkushe gabanta tace"Duk nasihar da zan miki yan uwana da mahaifinki sun miki nidai abu daya zan gayamiki kibi mijinki kibi mijinki ki mai biyayyah kada daga karshe ki kasance mai tsafta da kamshi akoda yaushe sannan ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa in kika kuskura kika saba musu Safeena ban yafe miki"Maman Aisha tace"Ashsha maman Safeena"Ummi tatashi tadago safeena ta rumgumeta suka kamkame juna Ummi tace"ku tafi yata Allah yabaku zaman lpy yasa i gidanki kenan har mutuwa Allah ya miki albarka na yafemiki duniya da lahira"Allah sarki rayuwa duk mai tsausayi sai da yayi kwallah dakyar aka rabasu ummi na kuka safeena na yi haka Usman dakyar aka bambare ajikin safeenar aka sanyata cikin motar tahir wanda iyami da inna husai da maman Aisha suka sata a tsakiya sauran motocin kuma jama'a sukai ta shiga abu  mamaki chan naga zugan Janaf novels and fans sunci ankosu na perper less blue and pick sundaura head pick su mom khadija mom Amira my xee Abi my juree name sake sahiba gun shiga mota harda faduwa😂😂😂 hakika sun bada kala domin kaf dinsu sun halarta ba wanda aka bari gadin gida wow.. Chan naga yan Na tafka kuskure fans suma sun kame awata jeep chan kuma na yan kungiyata Interlligent writers association suma da nasu gayyar suna sun kame awata bakar corrolla x hadaddiya na rike baki nace"Tab.  To yaushe suka zo nibanma san zuwansu ba nima dai na lallaba na shige motar kawayen Amarya kada atafi bani.

Karfe 4:00 dai dai muka dau hanya sai fatan Allah yakaimu lpy.


_KADUNA_

Karfe 8:39 da muka shigo kaduna domin dai ba'ayi wani gudu ba domin Dr ya tsawartar yace"Kada ajamai asarar da baiyi niyya ba dole aka lallaba dasu ahankali ammh ina kallon yan janaf fans sai da suka ce atsula gudu dasu domin motarsuce akan gaba nidai nace to Allah yasa kada haj.Mama tace nayomata zuga😛.


Magadi najin hon yabude get motoci suka dunga sulalawa jiki aikuwa kikaji guda na tashi domin haj.Mama najin hon tayi waje matar kawu bala kuwa ta dinga sakin guda abun sai wanda yaji haj.Mama ta bude murfin motar amarya iyami ta fito da ita haj.Mama ta waiga tace wai ina matan ne banji guda na tashi bane ai kan hajiya tace me kuda ya kacame gidan domin yan janaf ma ba'a barsu abaya mussaman murya mom khadija data Name sake tafikowa murya sahiba kuwa muryanta kadai akeji  gida ya hautsine da murnan isowar amarya hajiya ta rike Amarya tana fadin"Aminiya kin biyashe ni domin kin kawomin safeena har gida ina kara godiya"iyami tayi dariya tace"hajiya duk mu godema Allah domin shine abun godiya"Haj.Mama tace hakane kam bari tashiga shashen hadiza tukun kafin taje barayinta tako amarsu kinzo gidan karamci gidan mutumci da amana tako da bismillah Amaryan Safiyanu tako da izinin Allah aifa nan aka dau sowa da guda anayi har shashensu momma itadai Safeena tana dunkule cikin hijabi tana kukan rabuwa da iyayenta.

SAKINA Na daki taji dirin motoci zuwanchan kuma sai guda ta ko'ina taji abun yawuce misali shiyasa ta fito ta isa ga windon falo ta leka sai ko taga tawaga guda ga haj.Mama rike da wata lullube cikin hijabi ana ta guda gabanta yafadi ras'ras lokaci na farko tareda rawan jiki a idonta aka wuce shashen su mommah jikinta asanyaye ta saki labule takoma kan kujera ta fada yaraf tana auna abubuwa akwanyarta ta tuna kalaman Dr _kudinki ne aure zanyi nabaki ki siyi ra'ayinki_ tatuna kuma abubuwan da ake tayi daga jiya zuwa yau ana shagalin biki ta tuna sanda taji wata nacewa"Brka da zuwa amarsu ta ango"zuciyarta ta buga lokaci daya tareda mikewa tana dafe kirji tace afili"Kardai da gaske auren Safwan yayi..........




_topha karakara ga akuya ga kura.....Koya zata kasance muhadu a shafi na gaba_







commet
And
Share








*Janaf*✍

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now