TA TAFKA KUSKURE 22

645 29 1
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔







_*Sahiba ina kike wannan page din kacokan nakine Hafsart Almustapha Hafnan wlh soyayyarki araina tawuce duk kan tunaninki inaso kisani kowani bugawan Numfashina kina kokon qalbina*_





*22*


Koda Dr yadawo yaga Sakeena bai wani yi mamaki ba cos shiyanzu bata gabansa kokarin yadda zuwan amarya zai zama ready yake.

BaDa wuri yadawo ba shiyasa sai da yayi wanka yayi sallah kana yadauki check din daya rubatama sakina kudi yanufi dakinta da sallama abakinsa ya shiga illai kuwa Yar mulkin kwance kan gado tana zuba selfie tana daukan yanayin dakin dariya takusa kubcemai,saboda ganin yadda take wani ji dakai ita adole miji ya biyota dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tacigaba  abunda tajeyi mirmishi yayi kan ya isa ya zauna gefen gado yana fadin"Ashe andawo....Andawo lpy"kamar baza tayi mgana ba sai chan tace"Lafiya kalau aka dawo duk da akwai wanda  baiso mutafi ba"Tafada tana wani girgiza dariya yayi har hakoransa suka fito yace"Ai wani baice kar mutum yaje ba iyaka yace mutum yaje da kudinsa ne hakan da yayi laifi ne"Yafada yana kallonta basarwa tayi domin tagane yagasa mata mganane mikamata check din yayi takalleshi a wulankance tace'Na miye kuma mallam"Yace"Ki karba nakine"amsa tayi awulakance tana dubawa check din 2000hud thousand ne arubuce dagowa  tayi ta mika mai tana fadin"Kamakara ai ka rike tsiyarka domin ni yanzu nafi karfin taimakonka kodama tsautsayi ya kaini"bude baki yayi kan yace"Ke...abunda kike tunani kenan"Yafada hannunsa a haba Sakina tace"Bangane ba"Yace"Kudin nan hakkinkine fa aure zan kara shine nafita hakkinki na baki kudin saboda kisai Abunda kikeso ko"yafada yana kallonta kallonsa takeyi kan tasheke da dariya harda faduwa kasa kallonta yakeyi aranshi yana auna dabbancin sakina.

Mikewa yayi ya ijiyemata check din yanufi hanyar kofa yana cewa'Ki bar dariyarnan ina jiyemiki ranar da zaya koma kuka"Saurin mikewa tayi tasha gabansa tana cewa cikin shakiyanci"Tab...Wai aure zakayi kai bakaji kunya ba,ni zaka razana to ai bari kaji ni Sakina matar kaddarace mutuwace kadai zaisa kayi aure kai ko mutuwar nayi sai na ga dama balle da raina'Tafada tana nuna kanta kan takara shekewa dadariya,kallonta yayi kan ya girgiza kai yace"Kin Tafka kuskure sakina shiyasa har yanzu yake dawainiya dake kinyi kuskuren sawa aranki zan dauwama dake ke daya....watch and see"Yafada yana kada mata hannu kafin ya fice.



check din ta dauka kan tace"raba mugu da makami....Ibadane'tafada tareda fadawa kan gadon tana fadin"ji shi wai aure kamar auren banzane"Daga haka tajawo wayarta tacigaba daga inda ta tsaya

*Chai chai wlh kedai sakina anyi dabba wlh kin tabajin inda akayi wasan kishiya mtsssss mai kwakwalwar kifi kawai*😡




ko washegari tun safe Abuja tatafi saboda isar kayanta kotakan mganar Dr bata bi ba gani takeyi bazai taba iya kara aure ba sai da ta fito zata tafi yaganta shima zashi aiki yake cemata"Madam business sai ina kuma"Tayi mamaki ammh saita danganta haka da neman shiri yake a yatsine tacemai Abuja Mirmshi yayi mai kayatarwa yace"Allah ya kiyaye hanya madam busuness"Daga haka ya fice shashen momma ya barta nan itama daga nan tahaye motarta tayi gaba.

Ashashen momma daru suka sha da haj.Mama don yace tabari abincin sha'anin bikin yayimusu odar haj.Mama tace"Ina bazai yuyu ba tuka tuwon ne akafi su iyawa kokuwa miyar ne za'a nuna musu kukowa dafa shinkafanne za'a nuna musu to maza karya ya sake wannan ai barnan kudi ne yan'uwa zasu zo suzasu yi kada inji ka gayyatomana wasu kedararru suna bamu abinci"Dole ya hakura ammh yana jinjina karfin halin hajiya na fadar abunda bamai sauki bane gareta.

Tun aranar bakin Safana suka fara zuwa matar kawu bala uwani da abokiyar zamanta sai makotansu hakika haj.Mama tayi farincikin ganin baki sun fara hallata mussamman Haj.Mama tasa aka gayyatomata masu kidan kwarya daga zaria dushi  _wayyo za'a tuka tuwon babban gida_ momma kuwa farinciki yagama cikata duk inda ka ganta bakin nan har kunni goye da bawan Allah Adil.

Washegari kuwa sai ga mota  tahau sauke musu drinks kala kala da ruwa abun sai wanda yagani baki kuwa suncika gida harda yan garinsu momma Allah sarki aikin haj.Mama ce tace kowa yazo ataru anuna farinciki domin yanzu safiyanu yayi aure,koda Sakina tadawo daga Abuja taji hayaniya ashashen su momma ammh bata leka ba tunaninta yan kauyen nanne suka zo sucika ma mutane gida da hayaniya ko kallon shashen batayi ba tayi shigewarta shashenta agajiye take shiyasa wanka kawai tayi tafada gado sai barci yan aikinta naso suyi mata tsegumi domin gunsu habu maigadi sukaji yallabai zaiyi aure ammh ganin ba fuska yasa suka ja bakinsu sukayi shuru.


_ZURMI_

Sai ana gobe tarewar Safeena tadawo duk wanda ya ganta sai yakara kallonta saboda wani sheki data keyi kamar daren goma sha biyar Kda tadawo tayi gyaran kanta da lallenta kawayensu na mkranta sunyi mamakin jin tarewar safeena kuma wai andaura tuni harta Mallam yahuza takaimawa ya amsa yana sama mata albarka da aurenta gabadaya _Allah sarki loser_ batada wasu kawaye shiyasa daga ita sai Aisha suke gudanar da komai gashi daman Dr yace"Su zama cikin shiri karfe biyu za'a zo atafi dasu saboda kada suyi dare ahanya.

mganar kaya kuma hajiya ita tayi mgana Da Abbah tace kadama ya wahalar da kansa domin ko sunkawo zatasa amaidamai saboda safeena da safwan duk dayane agurinta ba bambamci to bbu yadda ya iya domin hajiya nada wata kima a idanunsa bbu abunda zaice sai godiya domin iyalan justice habule safana sun gamamai komai.





_YININ BIKIN TAREWA_
_*Both kaduna and zurmi*_

Tabbas inda ake dashi nan akeyi domin tuni takowani bangare shagali yakachame bari mu leka kaduna.

Haj.Mama tun asuba tasa aka dora tunkunya lamba talatin🤣🤣na tuwo da na miya aka shiga sha'ani atsakar gidan masu yanka alaiyahu nayi masu yanka albasa nayi wuri yahade sai hira ake ana shewa.

.Itakuwa momma tana ciki ita da bakinta mommy na tare da ita ga dan Amanar Adil shima yaci gayunsa yau takefa ranar itama momma taci gayunta cikin swice less dinta tadau dauri momna ta fito ras da ita ita kuwa hajiya mama doguwar rigar shadda taci taji aiki abunta harda daurin gwagwaro🤣🤣kan kice kwabo am kammallah tuwo an kwashe aleda an zuba a kuloli miyama tuni ta sauka wacce taji naman rago zubu zubu aciki ga jallop din shinkafa itama an kammallah ansa a kuloli ga alalen leda shima an kammallah  abun gwanin sha'awa tuni aka tsabtace wurin kamar ba'ayi komai ba.


Itakuwa sakina sai wajen 12 tatashi tayi wanka tafito falo koda ta fito taji hayaniya ta leka har sungama komai sun shige ciki sai hayaniyarsu kawai takeji tabe baki tayi takoma tasanya tashar bollowood tana kallo ko ajikinta shidaman Dr tun Safe yayi wanka yafice suna chan suna tsara yadda za'a tafi dauko amarsu ta ango.


Azurmi ma shima abunda ya gudana kenan domin ana hada hadan saukewa da dorawa ita kuma Amarya Safeena tana gidansu Aisha ita da kawayenta suna sitting cirewa kawai take tana zurawa chan bayan sallar azahar iyami tazo tatafi da ita gidan baffanta usuhu aka kaita yamata nasiha wanda tuni Safeena tafara kuka sun kawo kofar gidansu kenan sai ga motocin daukan amarya guda goma sha biyu hadaddu domin ba motar banza tahir da taufiq da jabir da Gidado,da sauran abokansu dai sukazo Tahir ne shugabansu.

Cikin gida akayi da Safeena domin kaita gun Abbanta yamata Nasihan zuwa gidan miji.







Commet
And
share

*Janaf*✍

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now