TA TAFKA KUSKURE 21

782 33 0
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔







_Hakika jiya naga kauna da soyayyah ta har abada janaf novels and fans jiya kunsani kukan farinciki wlh sonku azuciyata yayi girma da reshe matsayinku mai girmane inaso kusani janaf namuku son kauna_💞💞💞💞💞💞



*21*

_KATSINA_

-----koda kwamishina yadawo ya tarar da Sakina agida fada yahau yi yace meya kawota sai ta shirgamasa karya da cewa da izinin Dr Safwan tataho aikuwa baiyi kasa agwiwa ba yakirashi yake tambayansa abun mamaki Dr ya amsa masa da hakane cos bayaso ta dalilin sa Sakina tarasa albarkar mahaifinta.

******************

Babu yarda Safwan ya iya da mganar haj.Mama domin ko momma bata tsallake umarninta daya fadama Tahir shima yayi na'am da batun na hajiya domin yace abunda  babba ya hango yaro ko yahau rimi bazai hangoshiba.

kullum sai sunkusa raba dare suna waya sun maida abu kamar ibada shakuwarsu na kara ninkuwa atare da juna koda Dr Safwan bai budi baki yayi mgana ba shikansa yasani Safeena tana kokarin jan ragamar rayuwarsa agida ko office cikin waya suke kamar wasu tantabaru😛acikin satin yace tasa ido yana tafe saboda shirye shiryen Tarewarta.

Kamar wanchan xuwan wannan tare da Tahir suka tafi Ranar Asabar wanda tun adaren da Dr yafada mata suna tafe takasa zaune gari na wayewa taje akamata kitso dama tun adaren tasanyama kafarta sajen yayi ja sosai tana dawowa dama ta aikama Aisha suka zage suka musu alalan hanta da lemion kankana wanda Safeena tahada shi da hannunta,suna kamnallawa suka share gidan suka gyara dakuna Safeena tashiga wanka itakuma Aisha takoma gida ta shiryo.

Karfe 12 tamusu kofar gidansu Safeena wanda suna isowa yadaga waya Yakirata lokacin tagama shirywa cikin wata doguwar shadda light green taji aiki da Sallah Abbanta ya dinkamata turaren ta Wanda Humrace kanwar Abbah inna husai ta aikomata dashi ta shafa tuni tadau kamshi ba make up tayi ba hoda ta sanya liptick ammh ta fito ras da ita fitowa tayi tana sanya hijabi tace"Ummi sun iso"Ummi dake dakin Abbah tace"To Alhamdulillah...Ki shigo dasu".

Cikin takunta na natsuwa ta isa kofar gidan dukkansu suna jingine jikin motar Idanunta suka fara sauka kan Haskenta Yau kam sanye yake cikin wani farin yadi mai stantsi da yarari yana da ligo ligon zane a jikinshi ammh shararane domin hatta farar vest dinsa ana gani kafarsa sanye cikin bakin buddaden takalmin na fatar damisa hannunsa sanye da agogo na kamfanin rado,hularsa kansa kubece bakace idanunsa boye cikin gilashin dake karamasa kyau,cikin mutuwar jiki yake kallonta itama shi take kallo kasa kasa tana jifanshi da mirmIshi Dr Tahir ne yayi gyaran murya tace"To mr and mrs love kunbarni atsaye fa"Da sauri Safeena tace"La...ya Tahir yi hakuri barkanku da zuwa ku shigo"Tana fadar haka tajuyawa suka take mata baya da sallama suka shiga cikin gidan Ummi ta fito tana amsawa zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa ta amsa cikin farin ciki tana tambayansu mutanen gida sukace suna gaishesu.

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now