TA TAFKA KUSKURE 19

790 43 1
                                    

🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

*NA TAFKA KUSKURE!!*

🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀🙆🏽‍♀



          *NA*
   *Janaf ce*✍✍



DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍


*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""

*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂,  *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔







*19*

------Karfe sha biyu na rana ta musu akaduna,duk Da sun sharara gudu ko ahanyama haka Dr Safwan yake sukuku dashi bayi da kuzari lokaci bayan lokaci yana sakin ajiyar zuciya shikadai daga karshe kuma yayi mirmishi shi kadai,Dr Tahir yayita kallonsa yana girgiza kai cos yasani tunda yacemai bayasan damu ko ya mai mgana tsiya zasu tafka dat why yakyalesa akwai lokaci.


Asibiti suka wuce saboda sunsan aikwai tarin aiyuka illai kuwa aiki ya rike su sai dare kana,yamaida Dr Tahir gida yamasa godiya da bangajiya,kana ya Nufo gida hon yayima habu maigadi yataso da gudu ya budemai yana mai maraba Abun mamaki yana sulala motar tasa parking space kawai yaga Hajiya mama tafito da sauri zani ahannu tana Fadin"Oyoyo....Safiyanu angon Safeenatu"tafada tana budemasa murfin mota cikin kasala da mamaki ya fito fuskarsa na nuna almar gajiya yace"Hajiya...Wai baki kwanta ba",ta rike hannunsa tana fadin"inkwanta banga dan jikalle na guda daya aduniya ba,to ina lbrin Amarya Safeena yaka ganta tayi ko"Tafada harda dagamai gira😂😂dariya takusa kubcemai yace"oh...My god hajiya dawowata fa kenan wlh am tired"yafada yana yamutsa fuska rikosa tayi tana fadin"Koma u taya ne😂wlh alqur"an baka isa ba sai kabani lbri daga farko har karshe karyan tsiya ke dawani turancinka na karya'tana fada tana jansa shi saboda mamaki ma yasa yakasa kwatar kansa jaye dashi har falo tana kwalama momma kira"Ke Hadiza ki fito ga danki yadawo dan nasan shigewa cikin duk na kewarsa ne"tafada tana dankwarar dashi akan kujera.

Momma tafito sabe da Adil tana Fadin"Oyoyo....Babana mutanen Zurmi andawo"Ya sauko yana gaida momma ta amsa da fara'a tana tambayan ya ya barosu da kuma Safeenar ya amsa da suna lpy Allah sarki hajiya ashe kichen ta shiga ta  zubomai sauran alqubus din da momma ta musu dazu da miyar alaiyahu taji naman rago da man shanu,tahadomai da furarsa masoyiyarsa tana kawowa Adil na hannunsa tace"Maza ijiye yaron nan kazo kaci abinci dan nasan ka kwaso yunwa'baiyi gaddama ba ya mikama momma shi ammh kiri kiri Adil ya noke shi yasan ubanshi Haj.Mama tace"Kai kaci batar ubanka zonan...Inbanda kana butulu Hadizar zakayima kiyawa"Tafada tana rikosa harda dunkurinsa yayi nakwa nakwa yana kallon babansa zai yi kuka Haj.Mama tace"kul kamin kuka wlh in ci ballagazar uwarka"Ashhh....Dr Ya furta kan yace"plz hajiya stop it....Adil iz juzt 6 month fa mai yasani"yafada yananuna rashin jin dadinsa"Haj.Mama tagyara zama ta sunkuyar da kanta tace"Gani dakeni habule ko in kwantama ne"tafada harda rusunawa,banza da ita yayi kan yayi bismillah yafara cin abincinsa Haj.Mama Tace"Au dan batan uba kawai wlh sufiyanu kafita idona wai tun yaushe nake cema kadaina zagina da wannan yaren eye"tafada da karfi,banza yayi da ita cos baisan hayaniya sam itakuwa ta kulu tadinga masifa tanayi tana hadawa da Adil oh ni jami ko meye ruwan Adil anan oho.



yana kammalla ci ya wanke hannu ya mike yadauko kwanon furar yana cewa"momma zan je na kwanta wlh gabadaya agajiye nake..But tomorrow zan yi mgana daku"Daga haka yafice momma tanamishi fatan tashi lpy ita kuwa Haj.Mama binsa tayi da tsaki mteswwww tace"Aikin banza da wofi yo harni za'a ma gorin da'  dan ubanka inda ban haifi ubanka ba za'a haifekane kuma in kayi zuciya zo kadauki dan kamaida ma uwarsa dama mungaji da reno wlh"Tafada tana dunkurar da Adil akasa ta mike tawuce fuu tana fadin"Ni za'ayima iskanci da bura uba.muda mukaga jiya mukaga yau muna shirin ganin gobe kuma da izinin Allah🤣🤣🤣

TA TAFKA KUSKUREWhere stories live. Discover now