🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*😭 *CURDLE*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔Mom khadija kema ga Naki hakika commet dinki na sumar dani dear,irin sai an samin ruwa na farfado😛😛😛😛
ina godiya matuka da kauna ubangiji Allah ya barmu tare Nima bari na ara Son so💞💞💞*wannan shafin nakune my hafnan,my Anty,my beeba...I so much care abount u bbys*💞💞💞💞
*11*
-----Ai Hajiya saboda farincki har dare ya tsala basu fargaba nan ta kwana suna hirar yadda hadin zai kasance sai washegari takoma gidan kawu bala take fadamai yadda sukayi da Iyami.
Mirmishin jin dadi yayi yace"Ba shakkah iyami tacika kawa tagari domin azahirin gaskiya indai yarinyar kanwanta din nan dake zuwa ne to hakika yarinyace natsatsiya mai hankali da alkunya" Haj.Mama tace cikin washe baki"kwarai kuwa uwa uba ga ilimi ai tunjiya farincki yaki gushewa araina tunda iyami tafadamun wannan mganar Allah dai ya tabbatarmana da alheri"Ya amsa mata da Amin ya Allah.
**********************
*ZURMI*
Safina ta fito daga daki tana fadin"Ummi...Na shirya zan wuce"Ummi ta fito daga kichen tana fadin"Har kin fito Safina tace eh Ummi kinsan yau itace ranar karke sati mai zuwa ne tafiyar
Ummi tace"eh...Kinko fadamun to ubangiji Allah ya kiyaye hanya yakuma bada sa"a ta amsa da fara"a Amin Ummi na,ina usman,Ummi tace"yanzu na barshi anan yanzu haka ya fice.
Safina tace"ummi kudaina barin Usman na zuwa wasan bazan nan fa "UMMI Tace"inbanda abunki Safina kin fa san Halin Usman ba zama yake ba"takada kai tace"Bari naje Ummi Allah sa in hadu dashi yasin sai yasha rankwashi"Ummi tayi dariya tace"bazan shiga ba kunfi kusa.
Har takai waje tadawo tana kwalama Ummi kira Ummi ta fito a sukwane tana Fadin"Safina...Lafiya kuwa? ta rausayar dakai agabanta tace"Dama...Da....Ma Ummmi"Tayi tsam tana kallonta kan tace"Dama mene...? Safina tadago tana kallonta kafin ta dukar dakai tace"Ummi har kin manta yau fa sati ya zagayo"Ummi tagane metake Nufi ammh sai ta share tace"Eh...Nasani meya faru"Safina ta fahimci zolayarta Ummin keyi shiyasa ta hau buga kafa tana cewa"Kai Ummi....Kinfa gane...ShI...Shine kike zolayata"Ummi tasha mur tace"Kinga ni kam ban gane mikeke Nufi ba ki bude baki kiyi mgana"Safina tace"To shikenan Ummi tajuya tafara tafiya sai takai gabda zaure kana tace"Ummi karfa ki manta yau ce Ranar zuwan mallam yahuza fa"Tana gama fadar haka tayi waje da sauri.
Ummi ta murmusa tace"Oh ni Zainabu ya'yan Zamani....Allah ya nuna mana wannan Auren dai kowa ya huta,ta tuna sati uku daya wuce Abbanta ya bashi damar zuwa yafara ganawa da ita ammh a dan wannan tsakanin ta fahimci yarta na cikin Annushuwa matuka da alamu yaron yatafi da imaninta,dama kuma Abbanta yace datadawo daga musabaqan zai fada masa ya fito ya bashi ita kawai,ita dai tai Fatan Allah yasa alkhairi.
Fitan Safina ba dadewa,tana wanke wanke taji sallama dagowar da zatayi taci karo da iyami da Hajiya da hanzari ta saki kwanuka ta mike tana Fadin"yaya....Hajiya kune tafe"Iyami tayi dariya tace"Abun kamar amafarki ko zainabu'Ummi ta karisa ta amshi jakar hannun iyami tana Fadin"Wlh yaya sannunku da zuwa,Hajiyarmu yaushe agari"Iyami ta amsa da cewa'ta kwana biyu da zuwa ita tama daddakoni kinganta nan"Ummi taDauko musu tabarma ta shimfida musu takawo musu ruwa tazo ta zauna suna kara gaisawa.
Haj.Mama tace"Ni banga yata bane"Ummi tace"Yanzu kuwa ta fita zuwa islamiyansu kinsan ranar sati ne zasu wuce gasar"Haj mama tace"Allah sarki to Allah ya taimaka"suka amsa da Amin Ummi takara dacewa"kuma Hajiya wlh jiyan nan Safina ke cemin in tadawo tana so taje Safana Allah yasa Hajiya tadawo daga kadunar take cemata"Dawowa ai Safina sai dai ganin gida da ziyara ai ta koma dindin gun jikanta"Haj.Mama tace"Kidai barni da takaichi wlh bani kaunar garin nan kullum mutum a kuntace a anguwa baka ganin gilmawar kowa sai haushin kare"Ummi tayi dariya tace"Ai Hajiya kinsan birni tafita dabam ba irin nan bane"Iyami ta amshe da cewa"ina ma za'a hada bayan ance bariki ce chan!Haj.Mama tace"mugum bariki ma kuwa ai ni dan Safiyanu da Hadiza bazasuji dadi bane da tuni na kama kaina"Iyami tace"Yo dama Hajiya ina zaki ki barsu ai shine sanyin idanunwanki yanzu "Ummi tace"Wlh.. Kuwa ina fata dai suna lpy Haj.Mama tace"Lpyrsu kalau suna gaisheku.
Nan dai sukaita hira har Ummi ta barsu tatafi dora Sanwa har ta kammallah lokacin su Hajiya sun shiga daki suna sallar Safina tayo sallama ta shigo cikin dogon hijabinta harda safa da nikabinta hannunta rike da littafai Ummi ta amsa mata tana mata lalle marhaba Safina ta kalli takalman dake zube kofar dakin Ummi ta tace"Ummi baki mukayi "Ummi tace"Manyan bakima kuwa Innarki iyami ce Da Hajiyar Safina ce"Ai da gudu Safina ta fada dakin tana fadin"oyoyo innata oyoyo Hajiyata"Hajiya ce ta idar da sallah tace cikin farin cki"Yata Safina sannu da dawowa"Tafada jikin Hajiyar tana Fadin"hajiyata shine kika gudu kaduna kika barni ko"Haj.Mama tace"ayy yi hakuri yata ai yanzu kafata kafarki yata ba inda zani sai da ke"Iyami ta sallame sallah tana Fadin"ai ni fushi nake dake tunda Hajiya takoma kaduna kika gujeni"Safina ta isa kusa da Iyami ta rumgumeta tana fadin"Ayya innata wlh inanan zuwa in miki wata biyu har sai kin gaji dani"Iyami tayi dariya tace"bakomai yata sai kinzo.
Ummi ta zubo musu abinci suka ci suna hira Usman ma daya dawo yai ta tsalle yana murna sai bayan isha'i mallam Aliyu yadawo daga kasuwa ya tararda su Hajiya hakika yayi farincikin ganinsu matuka sai da ya kammallah cin abinci kana Ummi ta sanar dashi cewa suna son mgana dashi yace'To bismillah.
Bayan sun kara gaisawa Haj.Mama tafara dacewa"da farko dai mallam Aliyu munzo ne ziyara kuma da Neman iri"Mallam Aliyu yace"to masha Allahu Tacigaba da cewa"Nazo neman ma jikana auren diyarka Safinatu in dai za"a bashi'Mallam Aliyu yace"ikon Allah....yayi shuru kafin yace""Alhamdulillah Hajiya tabbas kina da kima ko ince zuru'arku zuru"ace mai nagarta kowa zai so hada zuru"a daku,bazan iya hanaku Safina ba sai dai akwai wani yaron dake Nemanta ne"Haj.Mama tace"Ai indai Bai turo mgabatansa ba,Mallam abamu dama"yayi shuri yace"babu komai hajiya shi zan mai bayani,Allah ya tabbatar da alheri kin wuce haka awurin mu",
Haj.Mama tace cikn farinciki "Nagode sosai in nakoma magabatansa zasu zo"Mallam Aliyu yace"to masha Allah Hajiya lokacin ni kuma na sanar da yan'uwana.Hajiya mama ta fahimci cewa safina nason mallam yahuza ko ganin murnan datayi lokacin daya aiko gashi yazo aranta take fadamin"Nasan safiyanu yafishi komai da komai na tabbata bazan yi nadamar wannan Hadin ba.
Hajita taita godiya itada iyami shikuma kunyar hajiya yakeji bazai iya kallon idanunta ba yace bazai bawa jikanta auren diyarsa ba.Ammh aransa yana jin tsoro kar yan"uwansa suce kwadayi yabi.
Sai washegari su Haj..Mama suka koma Safana taje ta fadama kawu abunda ke faruwa shima yayi murna yace"Ranar sati zasu je su samu mallam Aliyu ayi komai agama.
Hajiya mama tagyara zama tace sai anyi komai angama ko zata koma kaduna.
Commet
And
Share*Janaf*✍
YOU ARE READING
TA TAFKA KUSKURE
ActionLabari ne daya kunshi wata mata wacce bata daraja minjinta da aureta ba, tafi fifita neman kudi fiye da aurenta,wanda daga karshe take shiga halin nadama da kuskure domin jikakken labarin kubiyoni