*HANYAR BAUCHI* 🚎
©by *😘Um Nass 🏇🏼*
® *NAGARTA WRI. ASSOCIATION*
Page 1
Bissmillahir rahmanir rahim
Godiya ta tabbata ga Allah s.w.a wanda ya bani ikon rubuta wanan labarin, ina kuma roƙonsa da ya kare ni da dukkanin wani mummunan abu.
Wanan labarin ba ƙirƙira bane da gaske ne ya faru, sai dai ɗan ƙari da ba'a rasa ba dan bama labarin armashi.
__________
Ɗebo kaya take tana ƙara danna su acikin jaka, ko ina aɗakin ahargitse yake da kayayyakin da take zubowa daga cikin wadrof nata.
Danna jakar tayi saboda kayan da ta cika, sanan ta rufe ta da ƙyar, duk ta haɗa uban gumi, kamar da tayi gagarumin aiki.Shigowa ɗakin yayi da sallama abakin sa, turus ya ja ya tsaya ganin tulun kayan da ta barbaza akan gadon, ga kuma lokar kayanta awangale duk an hargitsa su.
Kallonta yayi yaga tana dai-daita zaman mayafinta ajikin ta "Wai ina zaki je ne haka?" ya tambaye ta cike da mamaki.
Ɗagowa tayi ta aika masa da wani kallo mai kama da na ban haushi "Ban gane ina zani ba? Bayan kuma kana sane da yau ne ake sadakar ukun Baffa nah."
Sassauta muryar sa yayi cikin lallashi ya fara magana "Amma ai nace kiyi haƙuri mu tafi tare nan da kwana uku, saboda aiki na da bazai barni na tafi ayau ɗin ba, kinga Allah basshi sai mu samu sadakar bakwai."
Afusace ta fara magana kamar da yake mata magana da zafi "Tabɗi jam! Lallai ma Abdul ɗin nan, har na tsaya sai anyi kwanaki shida sanan xanje gaisuwar Baffa nah. Ko dan ba naka kawun bane ya rasu shi yasa kake so na tsaya jinkiri anan bayan ga duka ƴan uwa da abokan arziƙi na can suna zuba idon ganina."
Kai ya dafe har yanzu muryarsa akwai rauni da nuna lallashi atare da ita "Ko kaɗan Mubarakatu, sanin kanki ne kin san badan tarin aiyukan da ke gabana ba da tuni mun tafi tare, amma duk da haka kiyi haƙuri ai gaisuwa ɗaya ce, ko nan da shekara ce bata tsufa, balle kuma acikin kwanaki shida dayin mutuwar, Addu'a kaɗai yake buƙata, kuma aduk inda kike zata isa gareshi."
Baki ta saki cikin mamaki da alhinin maganar Abdul ɗin "Shekara fa kace Abdul? Magana nake maka akan Baffa na ne daya rasu har Alhajin mu ya kiraka ya sanar da kai."
Baki ta ciza sanan taja jakar data shirya kayanta ta fara tafiya, har sai da ta ƙaraso kusa da shi tana kallon sa "Kai ne kake buƙatar ɓata lokaci dan zuwa yin gaisuwar, kake kuma da zaɓi akan kaje ko kuma ka tsaya, ni dai kam bazan ƙara koda mintuna goma anan gidan nan ba."
Tana ƙarasa faɗar haka taja jakarta ta wuce shi, da sauri ya bita yana kiran sunan ta, gabanta ya sha "Shikenan naji kiyi haƙuri ki zo na kaiki tasha ki hau mota, nima ba na faɗa da wata manufa ba, kiyi haƙuri."
kai ta girgiza ba tare da tayi magana ba, haka ya kinkimi jakar kayan duk da uban nauyin da take da shi, shi dai mamaki ne ya ƙi barin sa yayi shuru, bayan ya ajiye jakar a bot ɗin motar ya juyo da kallonsa gareta "Nikam wanan uban kayan da kika loda kamar mai barin gari gaba ɗaya, kuma duk wai axuwa gaisuwar mutuwa ne hakan?"
Bata ce masa komiba saboda har yanzu acike take, tafiyar da ya kamata ace tun ƙarfe shida tayi ta gashi yanzu bakwai na safiya har ta gota, amma kuma yana ƙara so ya ɓata mata wasu lokutan da surutun sa.
Motar ta shiga tana ƙara kallon agogon da yake maƙale ahannunta."Abdul mana! Kamar na takura ka ne akan kaini tashar nan, gashi kuma kai ka roƙi alfarmar zaka kai nin, ba wai tilastaka nayi dole ba."
Bakin sa ya rufe da hannunsa sanan ya tada motar "Yi haƙuri Madam Mubarakatu, bana so nayi kewarki ne."
Daga haka suka fice agidan bayan mai gadi ya wangale musu get haɗe da musu Addu'ar sauqa lafiya.
Tafiya suke babu mai cema kowa komi, jefi-jefi tana ƙara kallon agogon da yake saƙale ahannun ta tana buga tsaki musamman da ake samun yawaitar go slow ahanyar.
ƙarfe 7:30 suka shigo tasha, wata ajiyar zuciya ta sauƙe mai nauyin gaske, cikin jin daɗin dan wani nauyi take ji kamar an sauƙe mata.
Kallon tashar yayi ya fara yamutsa fuska, dan ko kaɗan baya sha'awar shiga motar haya akaran kansa balle kuma ga matar sa.Kuɗi ya zaro acikin aljihun sa ƴan dubu duba, ya ƙirga dubu Ashirin ya miƙa mata "Gashi wanan ko zakiyi wata hidimar da su, duk da nasan nima zaki ganni acikin kwanaki uku in sha Allah."
murmushi ta ɗanyi wanda iyakarsa laɓɓan ta "Na gode sosai, Allah ya ƙara arziƙi."
"Ameen"Sanan ya fito acikin motar, kai tsaye motar da yaji ana kiran Bauchi yayi anan ya biya kuɗin motar, sanan ya ɗauko jakarta aka saka abut ɗin motar, duka motar babu mata maza ne, abin da ya tsana kenan.
"Kinyi sa'a mutum ɗaya ya rage motar ta cika." ya faɗa cikin ƙarfin hali, amma azuciyar sa haushi ne cacir.
Fitowa tayi ta shiga motar tana faman rakuɓewa agefe, wanan shine karo na farko da ta taɓa shiga motar haya, gashi kuma duk maza ne babu mace ko ɗaya.Leƙowa yayi ta jikin window ya fara mata magana "Hankali na bai kwanta akan wanan tafiyar taku ba, amma ganin kin dage yasa bani da zaɓin da ya wuce na biki da Addu'ar sauƙa lafiya, ki kular min da kanki."
Ɗagowa tayi tana kallon sa, karo na farko arayuwar ta da zata yi tafiya mai nisa ba tare da shi ba, tun bayan auren su, so take tace ta fasa, amma kuma tayi yaya da dubbanin mutanen da suke jiran gaisuwar ta.
"In sha Allah." ta faɗa tana murmushi, dai-dai lokacin da motar su ta fara tafiya, hannu yake ɗaga mata har sai da yaga fitar su acikin tashar, sanan ya sauƙe wata nannauyar ajiyar xuciya.
Cikin sanyin jiki ya shiga motar sa ya nufi wajan aikin sa..
🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Tafiya maganin gari mai nisa, ban sani ba ko kun hasaso sauqin da ke cikin tafiyar Mubarakatu.
#TAURIN KAI MAFARIN WUYA
#NWA
#CMNTS, LIKE AND SHARE
#GIRMAMAWA©Um Nass
VOCÊ ESTÁ LENDO
HANYAR BAUCHI Completed
Conto'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin tau...