BAUCHI

461 60 2
                                    

HANYAR BAUCHI 🚎

Wattpad @UmNass

  Page 7/8

Sai da suka sake tafiyar awa guda sanan suka shigo cikin garin bauchi, wanda kowa acikin su sai da ya sauƙe ajiyar zuciya.
Da ji kasan dama sun riga da sun ƙosa, kana hankulansu gaba ɗaya ya kwanta. Sai Mubarakatu da take duƙuƙuna bakinta na karkawa da haɗuwar haƙoranta awaje guda, saboda zazzaɓin da ya fara galabaita ta.

  11:30 na dare suka tsaya atashayar Bauchi, garin tsit babu ya waitar mutane, sai fa ƴan tsirarun motocin da suke giftawa.

  Motar tana tsayawa kowa y Sauƙo yana hamdala abakin sa, babu kuma wanda ya ƙara ɓata lokaci acikin su ya kama gaban sa, bayan ƴar taƙaitacciyar sallamar da sukayi wa junansu.

Da ƙyar Mubarakatu ta iya fitowa, idanuwan ta duk sun ƙanƙance saboda kuka da zazzaɓin daya gama ratsata, sai faman tattara jikin ta take tana tsukewa waje ɗaya, hakan yasa ta fito ta fara jan jakarta wadda har an fito mata da ita.

  Da ƙyar take iya janta, haka kuma ƙafafuwan ta duk sun mata nauyi, saboda azaba. Bakin titi taja ta tsaya tana kuma jin darurawa da kuma alhinin inda zata samu abin hawan da zai kaita unguwar su. Dan titin tayau yake kamar anyi shara, asalima babu giftawar ko wani abun hawa.

Wani tsoro ne ya ƙara kamata jin haushin karnuka na kusantowa gareta, waiwaye ta farayi tana lalimen inda sauti da haushin yake fitowa, amma bata ganshi ba, bata kuma ji daga inda yake fitowar ba.

  "Ya Allah ka dube ni, ka sassauta min, kada ka barni da iyawata ka kawo min ɗauki daga wanan matsin da nake ciki." ta ƙarasa faɗa hawaye na zuba daga idonta. Ga wata iska da ta kaɗa mai  ratsa jiki.
  Tafiya ta farayi tana nufar hanyar da take ganin zata ɓullu da ita, wata mota ce ƙarama mai launin ruwan ƙasa ta tsaya agaban ta.
  Tsayawa tayi tana tasbihi aranta da duk wata Addu'ar da tazo daga bakin ta gudun kada ace masu satar mutane ne suka tsaya agaban ta.

  Glass ɗin motar aka zuge cikin mamaki sai taga matashi sarkin shisshigin motarsu agefen direba yana leƙowa da mata magana "Hajiya shigo muje mu ƙarasar da ke gida, dan na tabbata yanzu ba zaki samu abin hawa ba."

Ajiyar zuciya ta sauƙe ahankali, ba tare da musu ko fargaba ba ta buɗe gidan baya na motar ta shiga. Aranta kuma tana girmama mutunci da kawaicin Matashin duk da wulaƙanci da gwaliyar data sha yi masa amma bai ƙyale taba ya sake taimaka mata akaro na biyu. Wanan ya zame mata wani sabon karatu, ta kuma ƙara shiga taitayinta acikin rayuwarta ta gaba.

Tana shiga suka Jaa motar suka fara tafiya, sai anan ta kula ashe karnuka ne har guda huɗu aɗan gaba da ita suke haushi 'Lallai Allah ya auna mata arziƙi, da ace ta ƙara ɓata lokaci to ko shakka babu da karnukan nan sunyi fata-fata da naman jikin ta.' maganar da Mubarakatu tayi azuciyar ta tana kuma sauƙe ajiyar zuciya.

"Hajiya wata unguwar zamu kai ki?" Matashin saurayin ya tambaye ta ba tare daya juyo ya kalleta ba.

  "Unguwar Zango"  ta faɗa cikin sanyin murya, wanda ya sashi juyowa ya kalleta, dan bai ɗauka ta iya magana ahankali ba, shi yasa yake tunanin ko ba ita ta faɗi unguwar ba.

  "Ina kika ce?"

"Unguwar Zango nace maka." ta sake mai-maitawa tana tattarawa waje ɗaya.
Kai ya jinjina sanan yace "Ashe ma bamu da tazara sosai."

"Allah sarki." ta faɗa tana ƙara takurewa waje ɗaya.

Daga nan ya juya suka ci gaba da hira shi da abokin sa sai alokacin taji sunansa Abbakar saddiƙ.

  Har ƙofar gida suka kawota, da sauri ya fito ya buɗe mata ƙofa ya kawo mata sauran kayan nata, kana ya tsaya ya bubbuga ƙofar gidan, sai da yaji alamun kamar magana sanan ya shige mota.
  "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi." Mubarakatu ta masa godiya cikin sanyin muryar ta.

  "Ameen, Allah huta gajiya." ya faɗa gami da mata fatan samin sauƙin wahalar hanyar da suka shawo.

  Saida suka tafi sanan taci gaba da ƙwan-ƙwasa ƙofar gidan.

  "Wai waye ne cikin daren nan?" ta tsinkayi sautin muryar Yaya Surajo ta daki kunnenta.

Cikin rawar murya ta fara magana "Nice Mubarakatu daga kano yaya Surajo."

  "Mubarakatu kuma?" Yaya surajo ya faɗa cikin mamaki, sanan da rawar jikin sa ya buɗe ƙofar gidan.

  Tabbass Mubarakatun Inna ce, dube-dube ya fara yi can kuma ya sake kallon ta "Mubarakatu lafiya da tsohon daren nan? Ina mijin naki yake?"

"Ni kaɗai na taho Yaya." ta faɗa tana son rakuɓewa ta jikin sa ta wuce.

"Ke kaɗai kuma? Wata matsala ce ta haɗoki ke da mijin naki?" ya sake aika mata da tambaya saitin ta, dan tun bayan auren ta bata taɓa yin bulaguro ba tare da shi ba.

Gefen Mubarakatu kuma ayanzu ta fara jin jiri, da ganin duhu-duhu, sosai take ƙoƙarin aro dauriya da juriya dan ganin ta iya tsayawa da ƙafafuwan ta. Amma ina jikin ta ya ɗauki rawa na sosai.
  Kallon ta Yaya Surajo ya sake yi, tabbas bata cikin yanayin jin daɗi, amma kuma banda abin Abdul komi zai haɗasu ai bai kamata ya koro musu ita da wanan daren ba.

Ran sa ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci ya bata hanya ta shige gidan, sai da ta shiga tsakar gida ta yanke jiki ta faɗi.

Da sauri saurin mutanen da ke gidan suka iyo kanta, dan tunda suka ji ana bugun ƙofa suka san ba bugun lafiya bane, jin kuma an ambaci Mubarakatu daga kano ya sake jefasu cikin firgici da tsoron abin da ke tafe da ita.

Arikice suka ɗauke ta suka sakata amotar Yaya Surajo suka nufi asibiti da ita, tuni likitoci sunyi kanta kasancewar Asibitin kuɗi suka kaita.
  Ruwa da allurai aka mata barci ya ɗauketa.
Sai kaiwa da kawowa yaya Suraj yake, azuciyar sa kuma yana hararo girman rashin adalcin da Abdul yayima ƙanwar su, na barinta ta taho acikin tsohon daren nan.
Abban su kuma yana gefe azaune ya rafka tagumi, shi bai ma san ta ina zai fara bayyana damuwar sa ba.
So yake yaga Mubarakatun sa ta farfaɗo ya tambayeta abin da yayi silar barin ta gidan mijinta, da kuma ƙuncin data ƙunsa aranar yau.

Likitan ne ya musu alamu da su shigo office ɗinsa, cikin sauri suka bishi atare sun tadda yana ƴan rubuce-rubuce kana ya ɗago da kallonsa ga Abban.

  "Ya akayi kuka barta ta zauna da yunwa har taci jikin ta? Ga jikin ta baya son ruwa amma da alamu ruwan yau ya daketa sosai, wanda shi ya haddasar mata da zazzaɓin da ke jikin ta."

Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Abba da Yaya Surajo da kuma su Inna da suka kasa fahimtar bayanin likitan.

"Yau ɗin nan tazo daga Kano likita, bamu da masaniyar abin da ke damunta."

Kai likitan ya jinjina sanan ya zare gilashin dake idon sa "To gaskiya nayi mamakin ciwon daya kamata atsakanin wanan lokacin, Ulcer ta mata kyakkyawan kamu, kana zazzaɓi ya rufeta da ciwon kai mai tsanani, abu na gaba wanda yafi ɗaga mana hankali shine Zuciyar ta data tsinke alokaci ɗaya, sakamakon ganin wani abu daya tsorata ta ko kuma ya firgita ta. Lallai akula da hakan, idan irin hakan ta sake faruwa to zuciyarta ba zata iya ɗauka ba."

  "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un." kalmar da suka shiga mai-maita wa kenan cikin haɗuwar baki.

Gumi tuni ya jiƙe jikin Abba da Inna, yaya surajo kuma sai faman fifita rigarsa yake a jikinsa.
Wanan wani irin tashin hankali ne yarinya ƙarama tayi karo da shi? Tambayar da sukewa Mubarakatu da kuma tausayawa halin da suke cikin.

  "Karku damu, abin yazo da sauƙi ma da kuka kawota akan lokaci, yanzu ruwan da aka sa mata yana ƙarewa zaku iya tafiya." daga nan ya miƙo musu takarda magani da musu kwatancan inda pharmacy ɗin su yake da zasu siya mata.

Jikin su asanyaye suka tashi suka nufi ɗakin Mubarakatu bayan likitan ya basu tabbacin zasu iya ganin ta.

  Inna harda hawayen tausayin Mubarakatu sai da ya zuba akan fuskarta, ganin lokaci ɗaya fuskar ta tayi wasai.

"Abdul bai kyauta mana ba, wani irin zama suke shi da Yarinyar nan da ya koro mana ita da dare?" Inna ta faɗa tana matsar ƙwalla acikin idonta.

  Numfasawa Abba yayi "Yanzu dole sai dai mun jira ta tashi, sanan zamu san abin da ke faruwa tsakani ta
da shi mijin nata."

  Ahaka suka shafe fiye da awanni Uku har ruwan ya ƙare ta huta sanan suka nufi gida....

🥀🥀🥀🥀🥀

#TKMW
#NWA
#Cmnts, like and share
#GIRMAMAWA

HANYAR BAUCHI CompletedWhere stories live. Discover now