HANYAR BAUCHI 🚎
©BY Um_Nass 🏇Page 2
Gudu sosai direban motar yake wanda har suka fita acikin garin kano, ya kuma ƙure waƙa na tashi amotar.
Shuru mubarakatu tayi tana kallon gefen window ga kuma abin haushi duk sun cikata da surutu, baka jin sautin komi saina muryoyin gardawan dake motar, da kuma sautin waƙar da ba'a fahimtarta.Har tsakiyar kanta take jin sautin hirar tasu, wanda take fita kamar an buɗe bututun radio marar yi 'Nikam wata ƙaddara ce ta kawo ni shigowa motar haya?' tambayar da tayima kanta kafin kuma ta ɗora da ɗan ƙaramin tsaki. Wanda ya janyo hankalin wanda ke kusa da ita.
"Hajiya lafiya dai kike ta faman tsaki ke ɗaya?"
Harara ta aika masa da shi kafin ta juyar da kanta ba tare da ta tanka masa ba.Gyaɗar dake hannunsa ya miƙa mata "Bissmillah gyaɗa amaro hajiya, tafiya ana ɗan motsa baki tafi armashi."
Kallonsa tayi aƙalla bazai wuce sa'anta ba amma yanda yake magana kamar wanda ya yankema ƙasa cibiya, kai ta kawar tana mai gwaɓe baki "Nagode"
Kai ya jinjina, sanan ya maida hankalin sa ga sauran abokan tafiyar, nan suka ci gaba da hirarsu kamar dama can sun san juna.
"Ya Allah!" Mubarakatu ta faɗa tana dafe da kanta da ya fara juya mata.
Sanan ta kai kallonta ga mutanen da basu damu da shiga lamarin ta ba "Haba bayin Allah, ku ko gajiya bakwayi da surutu kamar da kuka samu wajan cin kasuwa."
Kallonta sukayi sanan suka kwashe da dariya, kafin wani ɗan dattijo yayi magana "Haba yarinya, ya Allah zai tsaga mana bakin magana kuma ace muyi shiru, duk nan da kike ganinmu yau muka taɓa haɗuwa, amma kasancewar mu musulmi da kuma zama amota guda yasa mun san juna."
Tsaki tayi ahankali "Amma kuma ai kwayi fatan mu sauƙa lafiya dai, akan wanan surutun naku da ba amfanar damu zaiyi ba.""Yo fata na nawa kuma, tun fitowarmu gida muke Addu'a har kawo tashin motar, bakinmu baiyi shuru ba." ɗaya daga cikin mutanen mota ya bata amsa.
"Sanan batun rashin amfanin hirarmu ke ce dai bakiga amfaninta ba, amma mu da mukeyi mu zamu bada labarin amfaninta." Dattijon ya faɗa yana jefa goro abakin sa.Shiru tayi bata ƙara magana ba, sanin cewar ko tayi ba fahimtar abin da take nufi zasuyi ba.
Ci gaba sukayi da tafiya yayin da aka zo tsakiyar hanya, ga gargada da kuma hawa da sauƙa, gefe guda kuma direban sai raraka gudu yake abinsa.
Ƙuuuuuuuu kakeji motar ta bada wani sautin ƙara, nan kan Mubarakatu ya haɗu da jikin Windon motar ya bada sautin Ƙuuummmm.
"Wayyo Allah kaina!" ta faɗa tana dafe da saitin kanta, wanda azaba ta sata furta hakan ba tare da ta sani ba.
Haba mi mutanen motar za suyi inba dariya ba, yanda tayi maganar da kuma salon yanda take buƙatar agaji kaɗai ya isa ya sheda zun-zurutun azabar da taji ajikinta.
"Sannu kinji Hajiya." na kusa da ita ya faɗa yana ƙoƙarin ƙunshe dariyarsa.
Ko ta kansa bata biba saboda azabar da ke saitin kanta ta ishe ta. Kafin wani lokacin kuma goshinta ya ɗan cure saboda tanan ta samu buguwar.Basu ƙara wata tafiya mai nisa ba motar su ta tsaya cak, bayan ta bada wani sauti mai ƙaran gaske.
Ido Mubarakatu ta fiddo waje cikin firgici da tsoro "Mi kuma ya faru Direba?"Juyowa yayi ya kallesu "Wallahi nima ban saniba hajiya, sai dai naje na duba."
Fita yayi ba tare da ya jira abin da zasu ƙara faɗaba ya buɗe gaban motar.
Wani hayaƙi ne ya masa Sallama wanda saida ya matsar da kansa ya gama ficewa."Turƙashi!" ya faɗa yana sharce gumin da ke zubo masa, kasancewar yanayin damina da ake ciki, idan ba'ayi ruwa ba to akwai zafin rana mai ratsa mutane.
Ɗan taɓe-taɓen sa yayi ya rufe motar, sanan ya koma ya tada motar, amma firr taƙi tashi, yayi hakan kusan sau goma amma babu abin daya sauya.
Ƙarshe ya ƙara fita ya duba injin da kuma ƙasanta, ba abin da ya iya sai tsayawar da yayi yana aika kallonsa ga motar da mutanen cikinta.Leƙa motar yayi ya kallesu "Akwai matsalafa sosai, dan motar nan ta ɗauki zafi da yawa. Sai mun jira ta huta."
Fitowa sauran mutanen sukayi suna miƙa da wara hannunsu. Sukam ko ajikinsu saima cewa da suke "Mun samu rarar lokacin da zamuyi taɗi awaje."Afusace Mubarakatu ta fito ta kalli Direban motar "Wata irin mota gareka da har take buƙatar hutu acikin tafiyar da ko awa guda bamuyi ba?"
Kallonta yayi sanan ya karyar da kai "Wallahi bata taɓa yin hakan ba Hajiya sai wanan lokacin, amma kuma nafi kyautata zaton rashin service ɗin da ba'a mata bane ya kawo haka, sai kuma rashin juyen mai da aka samu tsaikon yinsa shima."
Ido ta fiddo waje cikin firgici kafin ta ɗora da salati "Bakwa yima motarku service kuke doguwar tafiya da ita? Ya Allah!" ta faɗa tana shafa fuskarta, idanuwanta tuni sun sauya kala zuwa jajaye.
"A'a munayi Hajiya, dan duk bayan wata biyu muke yiwa mota service, shi kansa juyen bayan wata ɗaya muke yinsa, kinga yau ne ya kamata ayi, amma kuma sai ga tafiya ta taso, babu ta yanda zan iya yin sa."
"Hasbunallahu wani imal wakil!" ta faɗa tana tafa hannayenta.
Sanan ta kalli direban sosai "Amma kuwa kuna zalintar mutane da ita kanta motar, ace sai wata ake mata juyen mai, bayan duk mako ɗaya biyu ya kamaata ace ta samu hakan, gashi kuma service ɗin da shima ya kamata ace anayinsa asati ɗaya shine sai bayan wata biyu shima kukeyin sa. Wata irin rayuwa ce wanan ta cutar kai-da-kai?"
"A'a hajiya muna yi mata dai-dai ƙarfinmu, karki manta mu kasuwanci muke da ita, idan muka tsauwala da zafafa hidimar yi mata juye da service tofa zamu rasa har uwar kuɗi balle kuma riba."
"Ba shakka." ta faɗa tana jinjina kanta da rintse idonta.
Dan wani takaici ne yake kamata, ga ɗacin da ya riƙe maƙoshinta, tsab zata zagi direban motar idan taci gaba da tsayawa akusa dashi."To ki ɗanyi haƙuri ki koma gefe kema ki zauna. Nan da muntuna talatin sai mu hau mu tafi."
Ɗagowa tayi da niyar aika masa baƙar magana, amma kuma sai ƙaran wayarta ya katsar da ita, tayi saurin zaro wayar ta duba.
Sunan Abdul ne wanda ta sakayashi da Zumar Ƙauna ajiki, ɗagawa tayi kafin yayi magana ta fara masa magana hawaye na sauƙa akan idonta "Abdul ni kam yau naga gararin motar haya, da nasani nayi haƙuri min tafi tare, gamu atsakiyar jejin Allah sai mun jira mota ta huta kamar basarakiya. Sanan muci gaba da tafiya."Dariya yasa daga ɗaya ɓamgaran saboda yanda yaji muryarta ko ba'a faɗa masa ba yasan kuka take "Ai abin da nake ƙoƙarin nuna miki kenan. Amma wata mota ce haka?"
Baki ta taɓe sanan ta masa bayanin da direban motar ya mata, habawa nan ya fara dariya harda riƙe ciki.
Haushi, takaici suka sata kashe wayar sanan ta samu waje ta zauna tana rafka uban tagumi.🥀🥀🥀🥀
Ɗit-ɗitt maza ku matso ku kimanta kimantawarku, dan hanyar Bauchi ta ɗauko zafi da gargadar dakan sauƙa ahanya.
#HanyarBauchi
#NWA
#CMNTS, LIKE, VOTE
#GIRMAMAWA
ESTÁS LEYENDO
HANYAR BAUCHI Completed
Historia Corta'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin tau...