HANYAR BAUCHI 🚎
Wattpad @UmNass
Page 5
Shuru ne ya biyo baya atsakanin su, sai kuma tarin fargaba da tsoron da yake sauƙa azukatan su.
"Kaddai ace Ƴan fashi ne suka kashe hanyar? Idan haka ne gara tun wuri mu juya salin alin mu nemi wata hanyar." Dattijo Habu ya faɗa cikin fargaba da rawar murya.
Wanda ya janyo sauran mutanen cikin motar suka fara cece-ku-ce.
"Inna lillahi wa inna ilaihirrji'u. Nikam na shiga uku nah!" Mubarakatu ta faɗa tana ɗora hannunta abisa kanta.Juyowa Mutanen sukayi suna kallon ta, duk da kasancewar su cikin tsoro da ruɗani, amma ko kaɗan bai kai koda kwatar nata tsoron ba.
"Ba ke kaɗai kika shiga uku ba yarinya harda mu, dan yanzu bamu san mi kuma zamu tadda ba." Dattijo Habu ya faɗa yana sharce gumi akan fuskar sa, duk da uban ruwan da ake tsugawa, amma saboda tsoro da fargaba ya sashi jiƙewa.
Hakan ba ɗan ƙaramin tashin hankali ya ƙara jefa Mubarakatu ba. Hawaye kuma sai fama silala yake akan fuskarta, zuwa yanzu bata damu da kowa yaga damuwa da hawayen da yake zuba a idonta ba.
Kai Direba ya girgiza cikin sanyin Murya ya fara magana "Bana jin cewar ɓarayi ne ahanyar gaskiya, domin da ace ɓarayi ne ahanyar da babu wanda za'aga haka atsattsaye. Nafi tunanin wata matsala ce ta faru ahanyar."
Kai Sarkin Kinibibi ya jinjina "Ƙwarai nima haka nake Hasashe. Amma kuma da wanan muhawarar tamu ai gara muje muji abin da yake faruwa inaga zai fi, tunda ruwan ya ɗan tsagaita zuba, idan mukaci gaba da zama ba tare da motsiba muna ƙara ɓatawa kanmu lokaci ne, duk da yanzu ma almuru ta shigo."
"Gaskiya kam da yafi dai." sauran fasinjojin motar suka faɗa.
Anan direban ya buɗe motar ya fita, suma suka bi bayansa ɗuuu kamar haɗuwar baki.Yayyafin ruwa na sauƙa ajikin su, amma basu damu da haka ba, haka aɓangaran Mubarakatu hawaye ne ke faman zuba a idonta, dana sani kam tayi ta yafi aƙirga awanan lokacin.
Wajan wasu mutane suka ƙarasa wanda suke ta magana akan matsalar da ta kawo cunkushewar mutane awajen.
"Assalama alaikum."
Suka aika kusu da Sallama, wanda suma suka amsa musu gami da ɗan sakin Fuska agaresu."Lafiya kuwa muka ganku duk atsaye awaje ɗaya?"
Tambayar da direban su Mubarakatu yayi musu cikin fargabar amsar da zasu basu."Lafiya kam da sauƙi, dan gadar da zamu bi mu ci gaba da tafiya ita ta karye, sanadin ruwan daya ɓalle daga sauran hanyoyi da kuma wanda akayi yanzu."
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" suka faɗa atare.
Sai mubarakatu data ɗora hannu bibbiyu akai, tana razkar kuka."To amma ai akwai wata hanyar daga baya, sai dai ita zagaye ce akan wanan." Direban su Mubarakatu ya faɗa, cike da nema musu mafita.
"Ita ɗinma ta karye, dan muma da fari ita muka fara bi, ƙarshe sai dawowa mukayi ta nan, saboda wanan har tafi dama-dama tunda mota zata iya wucewa ta jikin ta ba tare da mutane da kaya ban."
"Kamar yaya kenan ?" Suka sake aika musu da tambaya cikin ƙaguwa da son jin zaren labarin.
"Eh ita gadar zaka iya wucewa ta kanta, amma fa kai ɗaya tal acikin ta, dan sauran fasinjojin ciki sai sun sauƙa su da kayansu, akwai masu iyo da fidda mutum sai su tsallakar da su. Amma idan ba haka ba kuna hawa to zata ƙarasa tsinkewa ku faɗo gaba ɗaya. Ko kai ɗinma hasashe ake akan wucewar ta ka, ba wai tabbaci garemu ba."
Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da kuma direban motar, idan aka ɗauke Mubarakatu da ta ɗora hannunta aka, tana runtuma kuka da hawaye.
YOU ARE READING
HANYAR BAUCHI Completed
Short Story'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin tau...