HANYAR BAUCHI 🚎
WATTPAD @UmNass
Last page 9/10
Koda suka je gida abinci inna ta kawo mata cikin faranti sai nono kindirmo da aka dama mata shi da zuma, ta ajiye mata agabanta.
Ai ganin abincin da Mubarakatu tayi ya taso mata da yunwar da ke maƙale acikin ta, nan ta shiga ci hannu baka hannu ƙwarya. Kafin wani lokacin ta cinye abincin tass, sanan ta janyo kwanon da aka dama mata furar itama ta shanyeta.
Tsoro da Al'ajabi ya kusan kashe su anan, mamaki na sosai ya kamasu ganin yanda Mubarakatu ta cinye abincin da ƙartai uku zasu ci su ƙoshi.
Kowa kallonta yake sai alokacin ta kula da aikin da tayi, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana goge bakin ta da hannu.
"Sannu Mubarakatu, lallai Abdul ya cuceki, ya rasa horon da zai miki sai na Yunwa." Inna ta faɗa tana matsar ƙwalla a idon ta.
Da mamaki Mubarakatu ta kalli Inna "Abdul kuma? Wa ya faɗa muku horon yunwa yake min?" ta aika mata da tambayar cikin mamaki.
"Haba kowa ya ganki ai ya san kina cikin wani hali, kinga yanda idonki yayi zuru-zuru, ga kuma likita ya tabbatar mana da ulcer data miki mugun kamu, sanan abu mafi tsoratarwa zuciyarki data tsinke. Mubarakatu magana tazo ƙarshe ki sanar mana da abin da Abdul ya ke miki, mukuma zamu nemar miki hakkin ki." Surajo ya faɗa yana huci kamar kumurcin zaki.
"Tabɗijam!" Mubarakatu ta faɗa tana kallon su ɗaya bayan ɗaya. 'Kenan su Abdul ma suke Zargi da zaman sa sila acikin wahalar ta, Allah sarki bawan Allah da sun san ƙoƙarin sa akanta da basu fara wanan tunanin ba.
"Ko kaɗan Abdul bashi da hannu acikin lalurata ta yau, asalima da ace zai san hakan zata faru dani to da ya bani kariyar da zata sa hakan bata faru da ni ba."
Harara Adda Fatima ta aika mata "Karki raina mana hankali, idan ba namiji ba babu wanda zaiyi silar haɗaki da tsinkewar zuciya, har kuma ya koreki atsakiyar daren nan."
Baki ta riƙe sanan ta girgiza kai "A'a wallahi kadama ku sa Abdul acikin maganar nan, dan koma miye ni na janyowa kaina shi... Daga nan ta basu labarin abin da ya faru tun farkon fitowar ta gida da hanata zuwan da Abdul yasha yi, har kawo tasku wahala da shiga ruwan da tayi kawo zuwanta duk saida ta faɗa.
Salati suka shiga rafkawa hannu bibbiyu suke tafawa, takaici ya hana Abba magana sai Yaya Surajo ne ya fara magana kamar ya kwaɗeta da mari "Amma da nasan abin da kikayi da kanki shi ya janyo miki rashin lafiya wallahi da ban ɓata lokacina na hana idanuwa barci saboda ke ba. Har yanzu kina nan da tsinanan taurin kanki da kafiyar tsiya wadda babu komi acikinta sai zunzurutun wahala. Allah sarki ni mai ƴar uwa na fara zargin bawan Allah Abdul akan shi ya kore ki ashe ke kika siyima kanki wahala da kuɗin ki. Wanan kaɗan ma kika gani mutuƙar zaki ci gaba da Taurin kai wata rana sai dai awuce da ke maƙabarta." yana gama faɗar haka ya wuce fuuu kamar kububuwa ya shige ɓangaran sa.
Kallonta Abba yayi anutse kafin nan yayi gyaran murya "Mubarakatu!" ya faɗa cikin tausasawa wanda ya sata saurin ɗagowa ta kalleshi, idonsa yayi ja ainin wanda da gani na ɓacin rai ne tsantsa, saurin sauƙe kanta tayi ƙasa dan ba zata iya jure kallon da Abban ta yake mata ba.
"Na ɗauka zuwa yanzu kinyi hankali kin sauya, na ɗauka duk abin da na faɗa miki abaya kin musu kyakkyawan ruƙo da hannu bibiyu, ashe ni nake nawa kiɗan da rawa, duk kuma sanda na faɗa miki magana yana shiga kina fiddashi ta ɗaya kunnun naki ne. Amma bazan ƙara ce miki komi ba, ba kuma zan ƙara tausasa muryata dan na lallasheki akan abun da ya zama halayya da ɗabi'un da kika ara kika yafama rayuwar ki ba. Idan kina da hankali abin da ya sameki yau ya zama Iznah agareki anan gaba. Gashi dai saurinki ya zame miki nawa, babu kuma abin da kika tadda wanda akace sai an jirayi zuwanki kafin ayi shi. Haka lokaci yake zuwa ya ruga da gudu ko ka amfane shi ko kuma ka barshi ya tafi."

YOU ARE READING
HANYAR BAUCHI Completed
Short Story'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin tau...