HANYAR BAUCHI 🚎
WATTPAD @UmNass
Page 3
Tagumi tayi hannu bibiyu tana kallon inda suke, jeji ne na sosai, su kaɗai ne awajan sai ƴan tsirarun motocin da suke wucewa jifa-jifa, acikin su da sun gansu sukan tsaya su tambaya ko lafiya?
Amsa ɗaya Direban ke basu "Zafi ta ɗauka suka jiran ta huce ne."
Daga haka sai su su wuce su barsu ba tare da sun sake wata maganar ba, sai ta fatan hucewarta lafiya.Gefe guda kuma sauran mutanen motar ne suka baje suna rattaba hirarsu kamar sun samu gida. Takaicin su sosai ke kama Mubarakatu, haka kuma akai-akai takan duba agogon da ke saƙale ahannunta.
12:30 har yanzu basu Isah bauchi ba, gashi tun 8:30 motarsu ta fito daga Kano, shima dan sun samu tsaikon go slow ɗin da ke garin.
Tashi tayi ta nufi wajan direban daya saje da sauran ƴan tafiyar suna Rattaba Hirarsu "Umm Nace ba, har yanzu Mintuna talatin ɗin basuyi ba ne?"
Da sauri Direban ya duba Agogon yaga lokaci ya ja, cikin sauri ya miƙe "Yi haƙuri Hajiya, shaf hira ta mantar dani.""Ai naga alamun hakan, duka acikinku babu wanda ya matsu da ya isah Bauchi."
Kallonta sukayi sanin dasu take, amma babu wanda ya tanka mata, sai shiga motar da sukayi. Ganin hakan yasa itama taje ta ƙume amazaunin ta tana dudduba wayar ta.Bayan shigar su motar Direban yayi ta ƙoƙarin tada motar, amma furr motar taƙi taduwa, yayi hakan yafi sau goma har ya haɗa uban gumi.
"Ya dai?" Suka tambaya cikin haɗuwar baki.
Gumin Fuskarsa ya sharce saboda zafin da motar ta haɗa masa "Wallahi taƙi tashi duk ƙoƙarina akan hakan."
"Kamar ya taƙi tashi direba?" Mubarakatu ta faɗa tana wara manyan idanuwanta, zuciyar ta kamar ta faso saboda takaici da zafi.
Fita Direban yake ƙoƙarin yi yana bata amsa "Matsalar ba daga zafin data ɗauka bane, dole akwai abin da yake buƙatar dai-daituwa acikin ta, gashi ni ba wai na san komi dake da alaƙa da motar bane." yana ƙarasa maganar ya fita waje, suma sauran mutanen suka fice.
Zufa ke fitowa daga ko ina na jikin Mubarakatu, ga wani takaicin daya gama Lulluɓai ko wani sashi na zuciyar ta. Hawayen da bata san da wanzuwarsu ba suka farar ankarar da ita sauƙarsu.
Gogewa tayi ta fito cikin jin haushi ta kalli Direban "Amma kasan ka cuce mu ko? Tunda kasan motar ka bata da lafiya Fisabilillahi ai bazaka ɗauki fasinjan nesa ba. Yanzu gashi ka katsema kowa hanzarin sa da uzurin sa, abin da nake ta fatan sauri naje na samu gashi da alama bazan same shiba. Wai ma waya baka shawarar fara tuƙin mota bayan babu abin da ka sani akanta? Acikin wanan ƙungurumin jeji taya yane zamu jure zafin rana da kuma muggan abubuwan da bamu san ta ina zasu ɓillo mana ba?"
Duka kallon ta mutanen suke baki sake, musamman yanda ta tasa direba agaba da faɗa kamar ta kwaɗeshi.
Shikam yasan yau komi za'ace masa shi ya siya, Addu'a yake akan kada suma sauran fasinjojin su masa tijara kamar ta Jarabatun macen nan, daya lura ko kaɗan bata da haƙuri.
Kai ya risinar ƙasa yana sassauta murayar sa "Kiyi haƙuri ƙanwata, ni kaina da nasan motar bata da lafiya da ko kaɗan bazan fara ganganci ɗaukan fasinja ba. Haka kuma acikin ko wani abu na rayuwa kin san mutum baya rasa inda Allah baya jarrabarsa, to wanan itace ƙaddarar mu, amma in sha Allah zamu samu mai taimaka mana ko acikin masu wucewa ne."Kai ta jinjina tana ƙara aika masa da harara "Haka ko wani mutum yake faɗa ai, da abu ya samu sai yace Jarrabawa ko kuma ya liƙawa ƙaddara, bayan shi ya janyo hakan da kansa, yanzu da ace kana ma motarka service da juyen Mai da hakan bata faru ba ai."
"Ke kam yarinya baki da haƙuri ko kaɗan, kinaga dai agirme ya girme miki amma kinzo kina ta masa magana marar daɗi, ai ko ba komi tunda yace kiyi haƙuri ki barma Allah komi kya haƙura ai. Haka kuma ki kyautata zato da tsammani na alkhairi aduk inda kike, amma kinzo nan kina mana fatan mungwayen abubuwa." Dattijon cikin motar wanda zuwa yanzu kowa yasan sunansa Baba Habu ya mata magana.
"Haba Baba! kaima nasan ranka ya ɓaci akan rufa-rufar da yayi mana, haka nan sai an gama cutar mutum ake tsirar bashi haƙuri, yanzu ina ranar hakan?" ta faɗa cikin ƙara jin haushin sa, da ya shiga kare direban akan maganar da ta shefesu duka."Eh koma naji haushi na masa uzuri, amatsayinsa na ɗan Adam wanda yake da ajizanci arayuwa, to kema kiyi haƙuri ki ƙara jira zuwa anjima muga abin da Allah zaiyi."
Kai ta gyaɗa ta koma gefe ta zauna 'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina da ban haƙurin data gagara yi su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin taurin kan da ya zame mata sila na ƙin haƙura da tausasawar da Abdul keyi mata, da yanzu tana gidanta. Gashi ita ba'a Bauchi ba ita ba a Kano ba. Abanza kuma tazo tana haƙuri da shanyuwa atsakiyar ranar da babu girgije ko kuma gajimaren da zai tare mata sauƙaƙa jin sauƙar zafinta atsakiyar kanta.' tarin ƙiyasin maganar da take yi kenan azuciyar ta, tana kuma nadama akan tafiyar data farayi, wanda aciki bata san kuma mi zata tadda agaba ba.
Wanan zai iya zama mabuɗi ko mafari na buɗe shimfiɗaɗɗiyar wahalar da take cikin tafiyar da Taurin kanta ya zame mata sila da kuma tsani na shan wuya acikinta.Wayarta ce tayi ƙara alamun shigowa kira, ɗauka tayi ba tare data ce komi ba ganin sunan Abdul ajiki "Motar taku ta tashi kuwa?"
Tambayar da ya aika mata asaitin ta cikin muryar tausasawa agareta.Ajiyar zuciya ta sauƙe wanda har saida yaji "Har yanzu bata tashiba Abdul, asalima ba daga zafin data ɗauka matsalar take ba?"
"Kamar ya kenan?"
"Nikam ina zan sani Abdul, bayan shima kansa direban janta yake ba tare da ya san asalin rayuwar ta da kuma abin da take so ko kuma bata soba." ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.
Hakan yasa Abdul kwashewa da dariya sosai "Sai kace wani mutum har zai san komi na rayuwarta, wai ko tun yanzu kin fara gajiya?" dariya yaci gaba da yi, dan bai wani maida maganar ta gasken gaske ba.
"Abdul mana! Kabar batun dariya da gaske bai iya gyara motar ba."
Yana dariyar ya bata amsa "Ai dama ba duka direbobi ne suka iya gyara mota ba, idan da gari akusa ya ɗauko muku mai gyara, ko kuma ku jira wani yazo zai taimaka muku."
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana fuzgar da iskar dake bakinta, wanda ayanzu tana cike da jin ƙishi na ruwa "Abar wanan batun, yanzu kana shan A.c abinka da shan ruwa mai raɓar ƙanƙara hankalinka kwance, ni kuma gani atsakiyar raɓawar zafi da kaɗawar iskar dake tafiya da hucin gashin rana."
Wata dariya ce ta zoma Abdul sosai "Ki bari Hajiya, saima kin ganni, yanzu na gama cin dambun naman da kika min na kora da ruwan lemo."
Muƙuttt ta haɗiyi yawu wanda yasa Abdul ƙara sakin dariya "Minene wanan kamar faɗuwar abu?"
"Yau baka aikin komi kenan sai na ci da sha?" ta katse masa maganar cikin jin haushin abin daya faɗa mata, shi yasafa akace wani lokacin maza basu da adalci, yanzu da shi wani ne ai yasa mata lemo aƙunshin kayanta, sai ya haɗata da kuɗin da basu da amfani awanan lokacin.
"Aiki kai! Yanzuma na dakata naji yanda kike ne, ina kewarki sosai."
Baki ta taɓe "Banga alama ba tunda kana ci kasha mai sanyi abinka."Dariya ya kwashe da ita sosai "Kefa kika tanadar min hakan kafin ki tafi, kuma miye laifina dan naci."
"Babu" ta faɗa kafin ta datse kiran wayar.
Da kallo yabi wayar yana ƙara sakin dariya abinsa, "Mubarakatu tawa" idan da abin da zaiyi kewa bai wuce shirme da fushin da take da shiba. Daga haka yaci gaba da duba takaddun da suke gabansa, akai- akai yake murmushi idan ya tuna magaran da sukayi da ita.🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
👏👏👏Rap rap Wow naga Mubah ta samu zunzurutun matayata alhinin tafiya da kuma tarin masu taya Abdul warwara haƙora dan yin dariya wa tafiya Mubah.
Naji daɗin cmnts da fatan alkhairin da kuka min, hakan ya ankarar dani da cewa har yanzu akwai wanan Kimar akwai kuma tarin dafifin da ke ɗauke da GIRAMAMAWAR da ko wani shafi ke ɗauka. Na gode muku sosai. Ina kuma ƙara aranta ko wata martabawa da mutuntakar data zarta ko wacce acikin tafiyar da aka farata.#TaurinKai MafarinWuya😥
#NWA
#CMNTS,LIKE SHARE
#GIRMAMAWA©BY UmNass
DU LIEST GERADE
HANYAR BAUCHI Completed
Kurzgeschichten'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar Ta HAƘURI, da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina, data gagara yi tun farko su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin tau...