Page 2

1.4K 77 6
                                    

🍒🍒🍒          🍒🍒🍒

🍇💦                       💦🍇
        *ALKHAIRI NA*
🍇💦                       💦🍇

  _JANUARY 2019_

     📝 _Written by DEEJA_ 👄

_Bismillahirrahmanirraheem_

  *PAGE 0⃣2⃣*

_Wattpad_ _@deejamranda00_

Bai wani dad'e gidan ba kasancewar ko zama yayi ba firan komai suke yi ba, iyacinsa wannan shirun wanda da alama ya zame masa wani gi6i cikin rayuwarsa, Umma dake zaune gefensa tana k'ara karantar yanayin d'an nata, shiru tayi fuskanta na d'auke da tsan-tsar ban tausayi, tunani take da ace a yau d'in nan tasan abin da zata yiwa wannan yaron ta ga ko da murmushi ne a fuskansa, da kuwa wannan alk'awari ne tayi sai ta nemo sa duk inda yake a fad'in duniya koda zata iya saka masa kad'an daga cikin ALKHAIRIN da ya ma ta a rayuwa. Motsinsa da taji ne ya sanya ta dawowa daga duniyar tunanin da ta fad'a, gani tayi yana shirin barin d'akin kallonsa tayi tun daga samansa har k'asan sa, sanye yake da kayansa na soldier saboda mafi yawa idan zai zo cin breakfast za a kirasa ko lunch da kayan yake zuwa mafi yawan lokuta daga office yake zuwa, murmushi tayi na ganin still k'afansa na sanye da takalminsa kaman ko yaushe, a tun sanin da ta masa abu d'aya ke sanya ya fitar da takalmi daga k'afansa shine sallah ko bacci, in bacin da hakan duk d'akin da zai shiga a rayuwa toh kowa da takalminsa ne, saurin take masa baya tayi ganin yana shirin barin gidan.

      "Babana Allah ya kiyaye hanya Allah ya kai ka lafiya a yi tuk'i a hankali kaman ko yaushe dan Allah kaji Babana?" Umma ta fad'a lokacin da take rik'e da hannunsa a k'ofan gidan. Kansa kawai ya girgiza ma ta alaman yaji, a hankali ya furta.

      "Toh Umma." Daga haka bai k'ara ba bai da d'a ba har zuwa lokacin da ya shige motarsa, tana tsaye a gun har zuwa lokacin da ya ja motar ya bar k'ofan gidan, a hankali ya ke tuk'a motar sanin Umma na tsaye tana kallonsa, ba ita ta shiga gidan ba sai lokacin da ya k'urewa ganinta, numfashe ta sauke mai zurfi a haka ta juya zuwa ciki tana 'yan tunane-tunanenta.

*****

Shi garta gidan zaune ta hangi matan gidan da 'ya'yansu zaune a gidin  bishiyar icen mangwaron dake gidan daga can gefe, sallama kawai tayi cikin muryarta mai sanyi bata samu wanda zata iya cin arzikin da zai amsa ma ta sallaman ba duk kuwa yawan matan dake gidan. D'an nesa da su ta durk'usa tare da mik'awa Inna Amina kud'in dake hannunta, waftar kud'in tayi kaman zata had'a da hannun na Khairiyya, a nan ta shiga irga kud'inta banza ta ma ta ba tare da tace ma ta komai ba, duk kuwa ganin da tayi kud'in sun haura na abincinta. Da kanta ta gaji da durk'uson ta tashi kasancewar tasan duk yawan wannan kud'in bak'ar dala ba zata iya samu a cikinsu ba, wani d'an k'aramin akurkin d'aki naga ta shiga, wanda ba komai a cikinsa sai shirgen tsummakaranta, kayan dake jikinta ta cire tare da yin d'aurin k'irji sai wani d'an dogon hijab da ta sanya wanda tsaban yanda yaji jiki har saman kansa ya huje, tsakiyan gidan taje d'an bucket ta d'auka tare da sanya guga a rijiya ta janyo ruwa, wanka ta shiga tayi wankan da sai mu ce yafi babu, dan kuwa daga ruwan sai ruwan ta watsawa jikinta ko d'an sabulun hamsin babu baren kayi tunanin sabulu mai k'amshi, Allah na tuba ita a rayuwarta wani k'amshi take nema. Dama idan da sabo ta dad'e da sabawa da wannan a haka tayi wanka ta fito tare da mayar da kayan jikinta da ta cire, hankad'e d'an tsummakaran zanen dake tsaye a k'ofan d'akin akayi, wanda yake amsa sunan labule d'an tayar da kanta tayi tana kallon wacce ke tsaye a bakin k'ofar tayi.

     "Me kika zubo min wa'an nan shegun idon nake uwa an sulala masara, ki fito ki d'aukan min awara na kafin in fara jibganki a gidan kuma wallahi idan kawun naki ya shigo kema kin san sauran." Matar ta fad'a tana barin k'ofar d'akin (Innah Sahura kenan) d'an hawayen da suka zubo ma ta tashare a hankali ta fito tare da daukan tallan nata ta fita,  ba ita ta shigo gidan ba sai can marece, haka dare na yi ta d'auki tallan gyad'a dafaffiya wacce ake sanyawa mai da yaji ta fita, a can ma sai dare guraren k'arfe tara na dare ta dawo gidan. A haka rayuwarta ta k'are ina zaki talla ina kika fito talla.... Dama matan kawun nata uku ne Inna Amina ita ce babba sai inna Sahura sai kuwa k'aramar Inna Baraka, kasancewar ko waccensu na sana'a suka raba wannan da safe wannan da maracce wannan da dare, gashi dukkansu suna da yara dan kuwa a gidan akwai 'ya'ya su ashirin da biyu, dan kuwa ko wacce a cikin gasar haihuwa suke, shi ya sanya suka shiga jibgewa Kawun na ta Bala 'ya'ya kaman tururuwa, sai dai a cikinsu ko waccensu ta killace na ta yaran sai ita d'aya ce ke yawon talla kwararo-kwararo a garin..

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now