page 12

707 67 15
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒

        🍇💦💦🍇
      *ALKHAIRI NA*
        🍇💦💦🍇

      _JANUARY 2019_

     _📝Writen by DEEJA_

     _Bismillahi rahmanirrahim_

     *PAGE 1⃣2⃣*

Cikin dare ma taso ko taya ta samu ta fita domin ganin ko Ummah ta dawo, amma still ba hanya a haka ta hak'ura ta barwa Allah komai taga yanda Allah zaiyi da ita zuwa gobe.

Karfe goma na safiyar asabar gidan sun tashi dukkansu sai hada-hada sana'arsu suke ba tare da kowaccensu ta damu da tasan halin da marainiyar Allah take ciki ba. A 6angaren Khairyyy kuwa jiya da zazza6i ta kwanta haka ma yau da shi ta tashi, ga wani tsoro da tsinkewar zuciya da wani irin-irin mugun fad'uwan gaba dake barazanar gusar ma ta da tunani, haka kawai take jin kanta na juya ma ta 6angare d'aya kuwa jikin ta da zuciyarta suna gaya ma ta kaman wani abu mara dad'i zai faru, ganin hakan ya sanyata d'aga hannayensa sama cikin kuka ta shiga furta.

       "Ya Allah kasan halin da nake ciki Allah ka dube ni ka kawo min sauki a cikin rayuwata, ya Allah duk abunda zai faru dani ka sanya shine silan farin cikina da ALKHAIRI NA...." Ta fad'a tana k'ara jin tsoron yanda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri.

    "Ahhhh Malam sai ina haka naga dai yau ba juma'a bace, in ce ko jiya juma'a baka sanyan irin wannan kayan haka ba hala ma birni zaka shiga gurin aure?." Inna Ameena ce da wannan maganar wacce daga d'akinta Kawun ya fito, murmushi yayi tare da kallonsa kansa tun daga sama har k'asa, shi kansa yasan yau yayi kyau sosai cikin farar shaddarsa wacce tasha aiki kaman dai wani alhaji.

     "Ai kuwa kinyi gaskiya, sai dai wannan ranar ai dole in sabanta sabida ita ce ranar nud'ewar arziki na."

     "Malam wani abun arziki muka samu ne.?"

      "Eh, ke dai bari inje in dawo ana jirana." Ya gaya ma ta dan kuwa duk cikin matan nasa nasu yafi zuwa d'aya dan kuwa halin da zuciyar duka iri daya ne, dariyar jin dad'i tayi tana masa fatan ko miye ya zo da yawa a haka ya fita daga gidan.

Numfashi Khairyyy ta fesar jin firan nasu fitarsa daga gidan shiya k'ara tsananta faduwar gabanta. Shiru dai tayi ba tare da tunanin komai ba tana kwance a haka can bayan 1hr taji sallaman Kawun nata.

     "Assalamu Alaikum....?" Ya fad'a cikin muryansa mai mai d'an banzan sauti wacce gaba d'aya ta mamaye dukkan ilahirin gidan, fuskan nan tasa kuwa ta nuna yana cikin matuk'ar jin dad'i da farin ciki." Sahura dake tsaye tana wanke shinkafa ce ta amsa sa.

     "Ina amaryar tamu take....?" Ya tambaya sai wani fara'a yake. Kallon sa tayi daga samansa har k'asan sa tare da fad'an.

     "Amarya kuma? A ina amaryar take kuwa?" Wuce ta yayi ba tare daya amsata ba, kansa tsaye bai tsaya ko'ina ba sai a k'ofan d'akin da Khairyyy take ciki, zanen dake d'akin ya yaye kwance ya hangeta ta dunk'ule gefe d'aya sai rawan sanyi take yi, cikin sauri ya k'arasa gunta d'agota yayi cikin nuna tsan-tsan kulawa ya furta.

     "Yata me yake damunki haka.?" Ya fad'a yana wani ta6a gefen wuyanta wanda kenan yayi zafi kaman garwashin wuta. Inna Sahura da dama tare suka shigo sai Innah Ameena wacce fitowanta kenan daga d'akinta ta hangosu zasu shiga d'akin khairyyaa, ai kuwa ita ma biyosu d'akin tayi shiru su kayi suna kallon sauratar Allah tsaban mamaki sun kasa gane dalilin wannan abun haka asali ma basu fahimci zancen nasa ba. Even Khairyyy dake cikin zafin ciwo she was very surprised ganin irin wannan caring haka da bata saba ganin ba. Kawu Bala kuwa shi ko a jikinsa sai hannunsa ya sanya cikin aljihun babban rigansa, wasu dunk'ulen kud'i ya fito dasu wanda a k'iyasta zasu kai 30k mik'a ma ta kud'in ya shiga yi bayan ya jingina bayanta da buhuhuwan harawa dake jingine a d'akin. Kallon kud'in tayi da idonta da suka ma ta nauhi tare da mayar da kallon ta ma Kawun nata alaman na miye.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now