Page 4

1K 99 12
                                    

🍒🍒🍒          🍒🍒🍒

🍇💦                       💦🍇
        *ALKHAIRI NA*
🍇💦                       💦🍇

  _JANUARY 2019_

     📝 _Written by DEEJA_ 👄

_Bismillahirrahmanirraheem_

  *PAGE 0⃣4⃣*

Wattpad @Deejamranda00

Daga can nesa ya hange ta sai layi take uwa wacce tasha wani kayan maye, ga kayan dake kanta sun rinjayeta sai dai hakan bai sanyata ta yi k'ok'arin tsayawa ba, babban burinta ta ganta a gurin da take ajiye tallan na ta, gaba d'aya ko gani ba ta yi a zuwa wannan lokacin k'arfin ta ya k'are wani luuuu-luuuu take ji idanuwanta na ma ta, hakan ya sanyata yin tangal-tangal zata fad'i gudun motarsa ya k'arawa yawa, saboda da akwai tazara mai yawa a tsakanin su, k'iris ya rage da ya kai gunta sai dai ina ya makara dan kuwa a zuwa wannan lokaci tuni ta dad'e da zubewa k'asa. Parker motan yayi a gaggauce tare da fitowa, tsaye yayi kanta cikin rasa abinyi d'an kallon gefe da gefensa yayi sai dai shiru kake ji garin, kasancewar tsakiyan rana ne a irin wannan lokacin baka cika ganin mutane ba. D'an durk'usawa yayi gabanta yana tunanin abin yi, ganin idan ya tsaya haka wani abun zai iya samunta, ya sanya sa sunkuyawa tare da d'aukanta cifff uwa wata baby. Kawu Bala wanda tun daga nesa ya hango kaman annoba a k'asa (kaman yanda yake kiranta) ya sanya sa karya hanya domin zuwa ya gani, sai dai me zuwansa yayi dai-dai da d'aukanta da Avdool yayi yana shirin sanyata mota, cikin mamaki Kawu Bala yayi kansa.

      "Kai kai bawan Allah ina kuma zaka da yarinyar mutane haka?" idan dutsin dake yashe a k'asa yayi magana toh kuwa Avdool ya masa, k'ara yin kusa dashi Kawun yayi yana k'ara dallo masa wata tambayar.

      "Kaga samari baka ji magana nake maka ba ina zaka je min da 'ya haka, irinku ne masu lalata 'ya'yan mutane daga k'arshe ko tsafe jininsu shi yasanya kuke a jik'e baku san takauci ba, yooo idan ba kud'in tsfi ba ina kai d'an yaro da kai ina hawa wannan motar?." Kawun ya fad'a yana k'ok'arin rik'e murfin motar ta Avdool, still dai gogan naku ko kallon inda Kawu Bala yake bai yi ba, sai ma gyarawa Khairiyya kwanciyarta da yayi  wacce tuni ya sanya ta a mota, ta gefe yake so ya wuce amma wannan mutumen ya hanasa ya wuce dan kuwa wani irin bake-bake yayi masa, Kawu Bala kuwa tsalle ya daka tare da cakume k'walan rigan Avdool kasancewarsa guntu inda Avdool ya tafi a tsaye uwa icen dogon yaro, wanda ina ga gaba d'aya Kawun ya manta da kayan dake jikinsa na soldier, kallon hannu da ya rik'e sa da shi Avdool yayi, a hankali cikin ruwan sanyi ya janye hannun nasa daga rigarsa, haka ya fitar dashi uwa abun kirki ashe kuwa ba haka bane dan kuwa a mutunce ya murd'a hannun Kawun wanda lokaci d'aya kaji yayi wani irin k'ara k'affff. Cikin wani irin azaba Kawu Bala da k'walla wata k'ara dan kuwa ba shakka ji yake uwa ana narke masa k'asusuwan hannu. abunka da soldier wanda ya riga da yasan ta kan mugunta kala-kala, d'an sakin hannun na sa yayi wanda kuma a lokaci d'aya ya k'ara fisgansa, amsawa hannu ya k'ara yi alaman yaji sak'on da ake basa a zuwa wannan lokacin idan ka kalli fuskan Kawu Bala zaka ci dariya dan kuwa kuka yake ta ko'ina da hawayensa ga majina ta suka had'e gu d'aya, ta ko'ina gume keto masa yake duk iya magiya da rok'on da ya rik'ayi cikin kuka Avdool bai barsa ba sai da ya tabbatar da ya gama kashewa wannan mutumen marayar hannu kafin ya watsar dashi can gefe, cikin salon tafiyarsa ya juya zuwa cikin motarsa wanda ya bata key, a guje yaja motar har yana neman markad'a Kawu Bala dake gefe wanda sai da yayi tsallen tashi sama yayi gefe, kuka yake yana tsinewa wannan yaron albakar dan kuwa a iya tsawon rayuwarsa bai ta6a ji akwai azaba makamanciyar hakan ba, a haka yana kuka ya ke tafiya rik'e da tsumman hannunsa wanda sai reto yake.

Cikin k'ank'anen lokaci suka isa Sokoto wani lafiyayyen hospital ya kai ta, inda nan aka shiga duba ta awon farko da aka yi aka gano malaria positive with typhoid, gado suka bata saboda yanda take buk'atan kulawan doctor. Shiru Avdool yayi zaune gefenta yana kallonta, bacci take sosai bayan treating d'inta da doctor yayi drip ne aka sanya ma ta saboda yanda tayi weak sosai, gaba ki d'aya ta sauya a kwana d'aya fuskanta har irin d'an kumbura yayi na rashin lafiya, gefen da ya mare ta ya kallah ga shatin yatsunsa nan a jere uwa an zana su, abunka da wankan tarwad'a wacce farinta kenan uwa na yan America. Sha'afa yayi yana kallonta wani irin mugun tausayinta na ratsa sa, haka yake zaune shi d'aya ba abinda yake sai aikin kallonta yana a hospital d'in har aka gama sallan zuhr bacci take ba ta farka ba, a masjid d'in hospital ya yi sallah, ko da ya dawo ya samu still  a kwance take tana faman bacci, gun da yake zaune ya koma zamansa da ko minty biyu bai yi ba, yaga tana d'an motsa jikinta can bayan second goma ta shiga bud'e idonta, shiru tayi tana kalle-kalle mamaki take ina ne nan? Lokaci d'aya abun da ya faru tun daga fitowarta daga gida har zuwa fad'uwanta ya shiga dawo ma ta, saurin gaske ta zabura tare da tashi zaune, sai faman kallon gurin take abu d'aya ta fahimta shine a asibiti take, da sauri ta kalle hannunta wanda ke sanye da cannula wanda aka sanya ma ta drip, cikin tsoro take neman zare given set d'in daga jikinta.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now