page 8

761 140 21
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒

🍇💦💦🍇
*ALKHAIRI NA*
🍇💦💦🍇

_JANUARY 2019_

_📝Writen by DEEJA_

_Bismillahi rahmanirrahim_

*PAGE 0⃣8⃣*

_Wattpad_ _deejamranda00_

Kaman yanda khairyyy ta ce kuwa hakan ya faru, yayanta ba samu shigowa gidan ba sai yamma lis sanye yake da dogon wando pencil wanda ya kamasa da riga body hug mai masifan kyau. K'amshi kawai yake zubawa fuskansa kuwa murtuk'e dai kaman ko yaushe.

"Assalamu Alaikum.?" Ya fad'a cikin muryansa da ke firgita mai sauraro. Amsa Sallaman akayi.

"Babana yanzu ake tafe.?" Umma ta fad'a wacce ke gyaran k'umba. Zaunawa yayi a hankali kan sallayan dake shimfe.

"Barka da gida Umma.?" Ya fad'a lkcn da yake k'ok'arin amsan rezon dake hannunta, mik'a masa tayi tare da amsa wa.

"Barkan ka dai Babana, ya aike.?"

"Alhmdllh Ummah." Ya amsa mata tare da dan mayar da kallon sa k'ofan parlon, kallonsa tayi tana karantar yanayinsa, sosai take farin ciki da abinda take gani tattare da shi, gani take kaman wanda aka chanja kad'an-kad'an farin ciki yana neman rinjayar bakin cikinsa tasan Khairyyy yake nema ita ma tayi mamakin rashin zuwanta tinda ta fita da safe ba ta k'ara shigowa ba.

"Khairyyyn ai bata shigo ba ina ga da akwai abinda ya hanata zuwa har wannan lokacin, amma nasan ai duk inda take tana kan hanya." Shiru yayi ba tare da ya tanka ta ba, dan shi kunya ma yaji shikenan yanzun ko zuwa gidan yayi Umma tinaninta gurin Khairyyyn yazo, (Ahhh toh ba dole Umma tayi tinanin ba gurinta kake zuwa ba tinda ta san halin kayanta) a haka dai suke zaune har ya kammala cire ma ta sauran k'umban wanda dama kad'an ya rage ta k'arasa. Tashi yayi a hankali zuwa parlo, Khairyyy wacce ke kwance kan dogowar kujera mai cin mutum uku, tintini ta shigo gidan ko da ta zo Umma na kitchen shi ya sanya tayi shigewanta parlorn, ba tare da Umman tasan da zuwanta ba k'ara kallon ta yayi ganin kaman k'arma take ga yanayin kwanciyan da tayi zaka fahimce bai wa taji dad'in kwancin bane, dan kuwa a mugun takure take hannunta d'aya tayi pillow dashi d'ayan kuwa ajiye kasan cikinta, k'afafuwanta kuwa a nannad'e suke. Jan k'afafuwan nasa yayi har gurinta tsaye yayi yana kallon ta wacce ita ba ta ma san yanayi ba, dan kuwa bata san da zuwansa gidan ba bare tayi tsammanin ganinsa a yanzun, a hankali ya durk'usa tare da sanya hannu ya tattare gashinta daya rufe ma ta gefen fuska. Dago kanta tayi a hankali jin an ta6a ta ganin wanda ke gefenta ya sanya ta sakin kukan da take k'ok'arin rik'ewa tintini wanda dama mai tanka ma ta kawai take nema, da gaske take kukan har sautinsa ya mamaye parlon wanda ina tinanin har Umma dake waje ta ji, ido ya zuba ma ta ganin yanda fuskanta yayi jajirr.

"Khairryyy baki da lpy ne.?"
"Meke damunki.?"
"Ina ke maki ciwo.?" Ya jero ma ta tambayoyin lokaci guda. Sautin kukanta ta k'ara jin yanda cikin ta ya k'ara juya ma ta.

"Khairyyy me ke faruwa ne.?" Ya kara tambayanta hankalinsa tashe.

"Ya Majeed cikina zan mutu." Ta gaya masa cikin muryanta mai sanyi ga kuma kukan da take. Saurin gyara ma ta kwanciyan yayi tare da daura hannunsa d'aya akan cikin na ta. D'an dannawa yayi jin yanda gurin yayi tauri. K'ara ta saki tare da zillewa jin yanda gurin ya k'ara ma ta ciwo.

"Khairyyyna me yasa kike haka bakya da lafiya ba zaki gayawa Umma ba.?" Shiru tayi sai hawayen dake ma ta zarya a fuska.

"Babana wa nake gani haka kaman Khairiyya.?"

"Ita ce Umma." Ya amsa ta.

"Me ya samu Khairiyyan? Ni ban ma san ta shigo ba." Umma ta fad'a wacce kukan da taji Khairyyn tayi ya sanyata shigowa parlorn.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now