Page 3

1K 91 7
                                    

🍒🍒🍒          🍒🍒🍒

🍇💦                       💦🍇
        *ALKHAIRI NA*
🍇💦                       💦🍇

  _JANUARY 2019_

     📝 _Written by DEEJA_ 👄

_Bismillahirrahmanirraheem_

  *PAGE 0⃣3⃣*

Wattpad @Deejamranda00

Tun daga nesa ta hango motar wacce ke zuwa a mugun tsiya ce, tsaye tayi gu d'aya jikinta sai makarkata yake gaba d'aya ta kasa ta6uka komai, ganin fa da gaske mai wannan motar ba imani ne dashi ba nema yake ya kashe ta, ya sanyata watsi da kayan dake hannunta cikin wani irin tsalle da kuzari wanda ko kad'an bata san tana da su ba tayi gefe d'aya, Avdool wanda komai dake faruwa a kan idonsa ne bai wani damu da hakan ba hasalima haushi yaji ta yanda bai samu ya markad'a 'yar banza ba, hakan ya bashi daman k'ara fisgan motar a haka ya zo a yanda yake cikin gudunsa na fitar hankali kaman dai yanda ya saba jan motar, haka yazo ya markad'a ma ta dukkan kayanta na tallah dake zube a kan hanya, hatta da kwanukanta na silver sai da ya maud'asu da tayoyin motarsa, a haka yayi tafiyansa ba tare da jin yayi wani laifi ko na rabin hankali bane. Khairiyya cikin wani irin kuka ta shiga duba kayanta, wa'anda tabbas ko a company za a mayar dasu toh kuwa ba zasu k'ara moruwa ba, a haka ta durk'usa gaban kayanta tana kukan haka ta shiga had'a kayan wa'anda ita canta bata san me zatayi da su ba, hanya ta bi tana tafe tana share hawayenta tunda ta sharo kwanar da zata sada ta da gidansu ta hango matarsa ajiye a k'ofan gidan Umma, hamdala tayi tare da k'ara jan k'afafunta cikin sauri dan kuwa a yau ta k'udurawa ranta sau ta gano gidan da yashi ga ya biyata wannan 6arnan da ya ma ta. Isar ta k'ofan gidan na Umma wanda dole sai ta wuce sa kafin ta shiga gidansu, taga ya bud'e murfin motar yana shirin fitowa wanda da alama wani abun ya tsayar dashi a cikin motar, tsayawa tayi gefensa tana kuka ba tare da ta furta komai ba, gogan naku kuwa ganin mutum tsaye a gefensa bai sanya sa fasa abunda yake ba, sakin murfin motar yayi tare da cira k'afafunsa cikin tafiyarsa ta da izzah da isa, Khairiyya ma kuwa bayansa tabi tana kukanta mai sauti, a haka suka shiga gidan Umma dake zaune a parlour sautin kukan da taji ne ya sanyata saurin fitowa tsakiyan gidan, ga mamakinta Avdool ta gani tare da Khairiyya wacce tayi tsaya gefensa tana rusgan kuka, cikin sauri tayi kansu tana magana.

      "A'a Khairiyya me ya faru kike kuka haka?" Umman ta fad'a lokacin da ta kai gefensu.

      "Umma wannan mutumen ne jiya ai na fad'a maki wani ya kad'eni da mota ko....?" Tayi tambayar cikin yanayinta na k'urciya, gyad'a ma ta kai kurum Umma tayi alaman haka ne, nan ta shiga d'ora bayaninta. "Toh Umma shine haka jiya ya kad'eni da mota yau ma kinga yanda ya kad'e ni duk ya farfasa min kayana." Khairiyya ta fad'a cikin muryarta da tasha kuka har ta gaji, dan kuwa ba abinda take tunani sai irin yanda za a jibgeta a gida. Umma mamakin duniya ya ma ta yawa me ya hada Khairiyya da Avdool har haka, a iya sa nin da ta yiwa d'an nata bata ta6a ganin wani ya kawo k'aransa ba sai a yau d'in nan kan Khairiyya.

     "Babana?" Ummu ta kira sa. Tayar da kansa dake k'asa yayi tare da zuba ma ta idonka yana kallonta.
    
          "Me ye ne?" Ya tambaya.

      "Haka ne abinda Khairiyya ta fad'a?" Ummu ta sake tambayarsa.

     "Wai ye ne Ummu?" Ya k'ara furtawa kaman wanda aka tursa sa dole sai yayi magana. Ummu shiru tayi tare da mayar da kallonta kan Khairiyya wacce har wannan lokacin kuka take rusga uwa Allah ya aiko ta. Takawa yayi da nufin barin gurin, wanda yin hakan dai-dai yake da take masa baya da Khairiyya tayi wacce da alama tayi shirin ko ta kwana. Ganin fa da gaske yarinyar biyar bayansa take tana kuka ya sanya sa jan birki cikin mugun 6acin rai ya juyo, tare da zuba ma ta manyan idanuwansa wanda har sun fara chanja launi tsaban yanda ransa ya 6aci.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now