page 13

1.2K 107 50
                                    

🍒🍒🍒 🍒🍒🍒

🍇💦 💦🍇
*ALKHAIRI NA*
🍇💦 💦🍇

_JANUARY 2019_

📝 _Written by DEEJA_ 👄

_Bismillahirrahmanirraheem_

*PAGE 1⃣3⃣*

Wattpad @Deejamrand00



HAFSAT KHAIRAN here's your page gashi nan mallakin kine kiyi yanda kike so dashi thanks for the love Allah yabar k'auna I love you fillah


K'arfe biyu da minti goma na ranar asabar su ka isa cikin garin shagari, lokacin yayi dai-dai da mintin Khairyy biyar a gidan mijinta, Abba a k'ofa gidan Ummah ya yi parking dukkansu fitowa suka yi da nufin shiga cikin gidan.

Avdool kan tsaye yayi jikinsa jingine a motar baya jin k'arfi ko kad'an a tare dashi, sai dai tsinkewan da zuciyansa ke ma sa yana basa gwarin gwaiwan juriya saboda baya so ya kasa baya san zuciyansa na sace masa gwaiwa.

"Babana ya ka tsaya a nan." Ummah ta tambayesa ganin yanda ya tokare a gefen motar. Shiru ya ma ta bai furta komai ba, hankalinsa da idonsa kuwa ba inda suke kalloh sai hanyar da zai sadaka da gidansu Khairyy. Abba wanda yake jin tausayin yaron nasa matsowa yayi cikin sanyi jiki tare da dafa gefen kafad'ansa, d'an d'ago kansa yayi ya mayar da kallonsa wa hannun na Abba wanda yake kan kafad'ansa sharewa yayi baice komai ba kuma bai jaye hannun ba, ganin haka ya fara k'arfafawa Abba gwaiwa.

"Kayi hak'uri Babana." Abban ya furta cikin sanyin murya. Avdool haka kawai yaji wasu hawaye masu d'imi sun zubo masa, wadanda ko bindiga aka d'aura a kansa ba zai ce ga dalilin zuwan su ba, ganin hakan ya sanya Abba ya kwantar dashi a jikinsa, ji yayi he can't reject him he just want shoulder to cry, haka kawai yaji yana so yata kukan da baya so a rarrashe ta.

"Abba Khairyy i love her with all of my life dan Allah kabba karka bari in rasata zan mutu." Ya furta cikin sautin kuka.

"In shaa Allah matuk'ar hakan zai zame maka silan farin cikin daka rasa a baya ni kuwa na maka alk'awarin nema maka auren Khairyy." Abban ya furta yana jin tausayin yaron nasa wanda gaba d'aya ya zama kaman wani mace akan soyayya. Ummah ganin kaman hankalin jama'a ya d'an fara zuwa kansu ya sanyata saurin rik'e Avdool da nufin shiga ciki.

"Gun Khairiyyaa zanje." Ya fad'a yana zare jikinsa daga nasu. Dukkansu ido suka zuba masa Ummah wacce tafi saurin fahimtarsa ita ta girgiza kai wa Abba da ke k'ok'arin hanasa, ganin Avdool d'in yana shirin kama hanya wacce shakka babu tasan inda yake k'ok'arin zuwa, ya sanyata furta.

"Alh. Dole zamu bisa." Amsata Abba yayi wanda shima bayajin zai iya barin yaron nasa ya k'ara masa nisan ko second biyar ne, Abban mota ya shiga Ummah ma haka ya sanyata fad'awa ciki, yar tazaran dake tsakaninsu kad'an ce shi ya sanya ya suka same sa kafin ya kai gidan, gashi dama a yanayin tafiyar ta sa haka yake kaman wani sabuwar mai jego ba k'arfi a tare dashu, a hankali yake tafiya zaka rantse ba wannan jarumin soldier d'in bane bai miji da samartaka da k'arfi ba. Lokacin da Abba ya bud'e masa front side bai mu sa ba, sabida shi kansa yasan yana buk'atan mai taimakonsa, dan kuwa ya yarda da bazai iya kai kansa gidan ba.

Isar su k'ofan gidan a lokacin Sahura ta budurwan 'yarta suka iso gidan, wanda dama mutun uku suka kai Khairyy gidan mijinta, d'ayar mak'ociyarsu ce sai Inna Sahura da Altine yarta, kalloh suka bi jibgegiyar motar da suka ga ta tsaya a k'ofan gidan masu, dukkansu suna mamakin wad'an nan daga ina. Mamakinsu ya d'an ragu ganin Ummah ta fito daga ciki, sai kuwa Abba wanda shima ya fito daga driver side.

"Sahura sannunku." Umman ta fad'a tana san kawar da mamakin da ta gani shimfid'e a fuskan Sahuran.

"Yawwa Haj. sannu." Ta amsata da sunan da ake kiranta a garin.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 10, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now