Page 9

832 103 17
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒

🍇💦💦🍇
*ALKHAIRI NA*
🍇💦💦🍇

_JANUARY 2019_

_📝Writen by DEEJA_

_Bismillahi rahmanirrahim_

*PAGE 0⃣9⃣*

A hankali yaji wani sanyi na ratsa dukkan wata ga6a ta jikinsa, ganin kaman yana neman zubewa a k'asa ya sanyasa d'an jingina bayansa a jikin ginin dake gefensa, Khairyyy wacce ke tsaye sake da baki in bacin kallonsa ba abinda take, duk da kasancewarta mai k'ananun shekaru hakan ya sanya ta tinanin da akwai abinda Yayan nata yake 6oye ma ta, matsosa tayi tare da rik'o hannayensa dake nad'e a k'irjinsa, cikin sanyin muryanta ta furta.

"Kayi hak'uri Ya Majeed.?" Numfashi ya saki mai sauti, tare da bud'e lumsassun idanuwansa zubasu yayi akan fuskanta cikin k'ank'anen lokaci ya gano irin tsoron da taji. K'ok'arin dai-daita kansa yayi.

"Ya wuce kema kiyi hak'uri." Ya furta yana k'ok'arin barin gurin, da kalloh ta bisa ganin shirin barin gidan yake ya sanya ta jin wasu hawaye sun zubo ma ta, a haka Umma ta same ta durk'ushe a k'asa tana dirzan kuka kaman Allah ya aikota cikin tashin hankali ta k'ara sa gunta kafad'unta ta rik'o tare da d'agata.

"Me ya faru Khairiyyya.?" Umma ta furta lokacin da ta d'agota zuwa jikinta.

"Umma Yaya Majeed ya tafi fushi yake da ni." Ta furta hakan cikin sanyinta da yanayinta wanda kai tsaye zaka iya kiransa da na shagwa6a, Kallonta Umma tayi cikin k'ok'arin gano abinda ya faru.

"Me kika masa yayi fushi dake.?" Ta k'ara tambayarta tana tsare ta da ido. Cikin sautin kuka ta gaya ma ta abinda ya faru, shiru kawai Umman tayi tana mai k'ara girmama al'amarin Avdoolmajeed, rarrashin Khairyyyn tayi tare da k'ara kwantar ma ta da hankali, har sai da taga tayi shiru.

"Umma dan Allah ki gayamin abinda yake faruwa da Ya Majeed dina.?" Khairyyy ta furta a hankali. Umma saurin kawar da kanta tayi gefe cikin son basar da maganan ta furta.

"Ba yanzun ba idan lokaci yayi zan gaya miki koshi ya gaya miki da kansa, yanzu kije gida kar a ne miki." Saurin barin jikinta tayi da gudu ta bar gidan tana kukan da ya ri ga da ya zame ma ta jinin jikinta.

******

Tinda ya bar gidan motansa ya fad'a ba tare da ko Umma yayiwa sallama ba, cikin k'ank'anen lokaci ya isa gida tin daga nesa ya hangon motarsa ji yayi 6acin ransa ya k'ara ninkuwa, d'aya daga cikin mutane da yafi tsana kenan a rayuwa d'aya daga cikin mutanen da sukayi sanadiyan fad'awansa cikin wannan matacciyan rayuwa, mutanen da yake tunanin sud'in ba ALKHAIRI bane a garesaba, ko gefen da yake bai k'ara kallon ba dan kuwa idan yaci gaba da kallon gefensa ko shakka babu zai iya aikata abinda zuciyan sa ke gaya masa, dan kuwa ayyana masa take yabi ta kansa ya markad'asa, ya mutu kowa ma ya huta, dan kuwa k'azantar ganin fuskansa yake wacce babu komai a cikin sai 6akin tabo, saurin danna hancin motar cikin gate d'in da aka bud'e masa yayi, ko parking d'in kwarai bayi ba ya fad'a cikin gidan yana cika yana batsewa, zuciyansa sai tuk'uk'i da kumburin bak'in ciki take masa wallahi baya son su baya buk'atan ko d'aya daga cikinsu yafi son k'arasa rayuwansa a haka da yayi tarayya da d'aya daga cikinsu.

Kwallan da suka zubo masa ya share tare da koma cikin motarsa ya zauna, bayajin zai gaji ko da a ce zai k'are rayuwansa gurin neman farin cikin Avdool, jikinsa na k'ara k'arfafa masa gwaiwa cewa wata rana zaiyi nasara akansa zai dawo da farin cikin gidansa gidan zai dawo kaman da, kaman ko wanne irin gida da ake rayuwan 'yanci dajin dad'i, tintini kowa ya gano gaskiya, Avdoolmajeed kawai ya rage shima dan bai tsaya ya saurare ba, bai tsaya ya bashi yarda da aminci da ya rasa a gunsa ba shekara biyar da suka wuce ba, amma yanzun yasan lokaci zai zo wanda zai fahimci hakan, farin ciki yaji ya shigesa cikin jin dad'in kwarin gwaiwan da zuciyansa ta basa yaja motansa zuwa masaukinsa.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now