page 2

227 25 0
                                    

*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 2.

*Gargaɗi*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a kafar youtube channel ko website ko facebook ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, da fatan za a kiyaye_

Dr Fadeela tayi shuru na 'yan seconds daga bisani ta nisa

"Shikenan Baba nayi Imani ga Allah kuma ina maka kyakkyawar zato, shigo mutafi" tace tare da bud'e masa k'ofar gefenta ya shiga ya zauna.

Duk da ta samu Natsuwa amma tsoro na mak'ale a zuciyarta tana karanto Addu'a

'La'ilaha Illa Anta Subhanaka Inni Kuntu Munazzalumin, ya Allah ka Amintar da ruhina bisa ga duk kan abin k'i, ka bani kariya bisa yardar ka, wannan Bawa naka in mugu ne karka bashi nasara a kaina ka fidda dani daga tarkonsa, Ameen'.

Baba Habu yana jinjina k'arfin hali na Fadeela, yace a ransa

'Tabbas Yarinya kinyi jarumta da juriya, Allah kasa mu fita hanyar nan lafiyan ba tare da komai ya cutar da ita ba, Ameen.'

Dr Fadeela ta juya akalar motarta tabi wannan jejin cikin wani irin yanayi na tsoro har suka isa wurin. Baba Habu yace

"Yauwa Yarinya yi parking anan mun iso, gashi can na rufeshi da ciyayi bari na d'aukoshi"

"humm" ta iya cewa saboda bugun da zuciyarta ke mata, yana fita a motar ta sanya lock, tana kallonsa harya isa wurin Imran.

Ciyayin ya cire masa ya rabashi da jikin bishiyar ya juya da bayansa ya kamashi ya jashi a k'asa har zuwa wurin motar, kasantuwar gaba d'aya jikin Imran d'in ya saki ga kuma gajiyar da ya d'iba na noma ba zai iya d'agashi ba.

Ganin haka yasa Fadeela fitowa da sauri ta taimaka masa suka sanyashi a seat d'in baya suka kwantar dashi, da sauri ta koma mota jikinta na rawa, shima Baba bai bi ta kan kayan Nomansa ba ya shiga mazaunin gaba, ta tayar da motar tare da yin wani mugun ribas ta figi motar a guje suka bar jejin.

Saida suka hau kan babban hanya Dr Fadeela ta samu damar sauke ajiyar zuciya, Baba Habu ya kalleta

"Nagode 'yata kinyi namijin k'ok'ari da bajinta, a irin wannan zamanin samun irinki wuya sai an tona, Allah ya miki Albarka yasa ki gama da duniya lafiya"

"Ameen" tace fuskarta d'auke da murmushi da jin dad'in yabawan da Baba Habu ya mata.

Sun wuce wasu gine-gine dake bakin hanya sai baba yace
"Yarinya wancen Asibitin zaki kaimu dake kallon titi" ya k'arasa maganar yana nuna Asibitin da yatsa.

Fadeela ta waigo ta kalleshi tana murmushi sai ta k'ara maida kallonta kan titi tace

"Sunana Dr Fadeela Umar ni babbar Likita ce a nan Abuja, Baba kamar yanda Allah ya bani ikon tsayawa na taimake ka to zanyi k'ok'arin na cike Ladana Nice zan duba Yaron ka da duk wani taimako daya kama ya samu Insha Allah, fatan mu Allah ya bashi lafiya."

Mamaki ne k'arara shinfid'e a fuskar Baba cikin rawar Murna yace

" 'Yata kin cikani da mamaki dan iya taimakon da kika min ma yanzu ya ishe ni, karki damu ki saukeni a nan d'in kawai, nagode da duk taimakonki gareni".

"Baba karka sanya na karaya ka barni nayi aikin Lada, zanyi iya k'ok'arina akai domin naga lalurarsa kamar ta shafi b'angaren aikina ne dan yana Unconscious, lallai yana buk'atar gwaje-gwaje, Addu'a kawai nake buk'ata ka min Baba" ta k'arasa maganar tana murmushi.

K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang