SERIES 2

2.9K 135 10
                                    

♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*PRINCE KHALEED!*
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
_Continuation_
_of ƘADDARAR SO!_
♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥



©®
*MISS XERKS*✍🏼

*BESTOWED TO:*
*XUMUNT@ NOVELL@ GRP*📚

~21 June 2019~.
18:00PM

_______________________
'''SACRIFICE TO:'''
*_SANAZ DEEYAH👄_*
_______________________

∇ΩTΣ & ҒΩLLΩШ 4ШΔTTPΔD
@OUM-RAMADHAN1433

بسم الله الرحمن الرحيم...

'''NOT EDITED'''.
*SΣRIΣS 2*

*_FLASH BACK:_* 🎯

••••tin alokacin da Rahinat ta baro gidan Khaleed take gudu batare data san inda take jefa ƙafarta ba.

haka Khalid ya fito ya gama bulayinsa bai sameta ba harya gaji ya koma cike da damuwar zantukanta.
daren ranar barinta ya wuce delhi.

tsalleken titi take tsallakewar rijiya da baya, shigowarta wata anguwa da babu jama'a ta hangi wasu tsaffi zasu wuce.

ƙwala masu kira ta shiga yi har Allah yasa suka jiyota, saboda rashin yarda ta yanzu tsohuwar matar dake tare da mijinta tace dashi," anya kuwa ma tsaya, duba fa ayanda take, Mlm shige mu tafi"

"a'a bazai yiwu mu wuce mu barta cikin wannan halinba na tsananin buƙatar taimako, karfa ki manta keda kanki kike tinatar dani wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi, yanzu duba kiga fa yanda take a wahalce ,kiyi haƙuri ki bari mu sami ladan wannan taimakon kinji"

matace dake tsananin yima mijinta biyayya babu musawa a tsakaninsu hakan yasa tace dashi, "tom Malm mu jira isowarta, Allah ya jiyartar damu alkhairi atare da ita"

tsaye sukai suna jiran ƙarasowarta, duk ta gama galabaita da ƙyar take takawa, tangaɗi take kaman wata ƴar maye daka ganta kasan ta wahala dole kuma ta baka tausayi ,murfayen idonta saboda nauyin da idonta yay da ƙyar suke haɗewa wajen rufuwa.

tin tana takawar har ta kasa saita koma jan ƙafa ɗaya, dai² da zuwanta tsallakawa wani mai mota yay awon gaba da ita.

ƙara ta ƙwala mai ƙarfi buguwar da tayi yasa ta dogon suma.
dukansu a ruɗe suka kinkimeta akasa a mota suka wuce asibiti.

tsawon watansu guda bata dawo hayyacinta ba,wani tinani yazo ma Mlm Hardo alokacin da suke zaman jinyarta yace da matarsa suce da mutumin daya kaɗeta ƴarsu ce karsu nuna basu da wata alaƙa a tsakani.

kyakykyawan matashin saurayin daya kaɗeta kullum sai yay zirga akanta ba dare ba rana,kuɗaɗe masu yawan gaske yake bawa su Mlm Hardo duk lokacin daya zo, duk zuwan nasa kuma saiya kawo sayayya mai uban yawa.

alokacin da aka basu sallama zasu wuce gida su ƙarasa jinyarta acan wasu mahaukatan kuɗi Raihan ya zube masu yana mai daɗa basu haƙuri akan abinda ya faru.

bawai dan lokacin dischrge ɗinsu yayi ba aka basu sai dan takurawa da sukai aka masu hakan, duk yanda likita da Raihan sukai akan su haƙura aci gaba da jinyarta a asibiti sukace a'a su gida zasu wuce domin suna so su haɗa dana hausa.

hakan da sukayi Inna Jummala ce ta ɓullo da dabaran, domin idan suka koma gida kulawan Raihan zai ninku akan na yanzu, dan da haka zasu samu su tara abinda zasu tara har zuwa lokacin da yarinyar zata sami sauƙi, saboda ta lura yarinyar hanyar arziƙinsu ce, in ta zamace su zauna tare da ita dan dama basu taɓa haihuwa ba in kuma ta wucewa ce to shikenan.

PRINCE KHALEED Completed.Where stories live. Discover now