SERIES 14

1K 91 12
                                    

♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
     *PRINCE KHALEED!*
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
             _Continuation_
        _of ƘADDARAR SO!_
♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥

         
 ®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A''' 🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼*

      ©
*MISS XERKS✍🏼*

~15 November 2019~
         08:00AM

_______________________
'''SACRIFICE TO:'''
*_NUSAIBA Y GIƊAƊO_*
*(UMMU MUHSIN)*
_______________________

         ∇ΩTΣ & ҒΩLLΩШ 4ШΔTTPΔD
            @OUM-RAMADHAN1433

بسم الله الرحمن الرحيم...


*SADAUKARWA GA MARASA YIN COMMENTS, KUJI DAƊINKU, XERKS NA GAIHEKU BOHOT-BOHOT😍😘.*


*SΣRIΣS 14*

*__________📖*  da zallar ɓacin ran kalamanta Abibi ya nufi inda take, yana zuwa ya tsinketa da marin da saida taga hasken wuta.

"ƙarya kikeyi munfuka, wallahi baki isa kin ɓata mana suna ba domin kuwa muɗin mutanen arziƙi ne kuma kowa ya shaida hakan, wace ke? nawa aka biyaki?, to bari kisan abinda baki sani ba daga ke har jahilan mutanen da suka aiko ki domin kici zarafinmu kunyi kaɗan" ,

"nida Sa'adatu ba irin shaiɗanun mutanen nan bane marasa imani masu butulcewa ni'imar ubangiji da zai ɗauki kyauta mai girma ya bamu mu wulaƙantata ba, Ƴaƴa da kike ikirarin mun haifa tabbas wannan haka yake komi kin faɗi dai-dai sai zance ɗaya da kikai kuskure akai, bamu saida ƴarmu ba, Allah'n daya bamu shiya amsa abarsa, bawai dan baya sonmu da ita ba sai dan yafimu sonta, da hannuna na ɗau gawar RAIHANA na kaita maƙabarta, amma ni ban saida ƴata ba saboda wani abin dubiya, kuɗin dana fi ƙarfinsu tin kamin zuwan RAHINAT da RAIHANA duniya"

ta ɗago idanunta suna masu zubda hawaye tace, "to Abbi ni kuma wace? mine matsayina a wurinku? miye asalina?  dan Allah ka fitar dani daga ruɗani domin kuwa a yanzu inada buƙatar jin ɗumin iyayena, ina son na sami kusancinsu koda babu soyayyarsu kamin na koma ga Allah"

Abii yace, "mu bamu sanki ba, hasalima bamu da wata masaniya akanki, wala'Allah su macutan da suka sauya maki kamanni zuwa irin siffar ƴarmu suke son yin amfani dake ta wata hanyar, yanzu gashi suna neman saki a wuya, domin kuwa ni Abdullahi bazan ƙyaleki ba kuma bazan yafe maki ba har sai na ɗaukarma ƴata fansar wuyar da kika jefata aciki....."

ta katsesa da faɗin, "to Abii idan kuma nice Rahinatu fa?"

wani irin juyowa yayi da jin zancen nata, ya daɗe yana ƙare mata kamin ya koma kan Rahinat ma ya ƙare mata kallo,wani tsoro yaji ya ziyarce shi, karfa aljanu su buɗe masu ido.

ta kuma katse tinaninsa, "Abii baka tinanin nice salahar Rahinat ɗinka waccen kuma ƴar basaja...."

itama bata kai aya ba Khaleed ya nunata da yatsa yace,

"ƙarya take Abii, ba itace Rahinat ba, ga Rahinat kusa dani...kamar yanda na gaya maki ni ba mutum ne mai son a ɓatawa lokaci ba, dan haka karki kuskura gaskiya ta fito daga bakin waɗanda nike tsare dasu domin bazaki ji da daɗi ba....."

shima maganarsa ce ta tsaya lokacin da Mami ta jefo masa tambaya.

" kai taya kake da tabbacin cewar wannan ce Rahinat Aayan?"

PRINCE KHALEED Completed.Where stories live. Discover now