SERIES 22

1.1K 86 5
                                    

♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
     *PRINCE KHALEED!*
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
             _Continuation_
        _of ƘADDARAR SO!_
♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥

         
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A''' 🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼*

      ©
*MISS XERKS✍🏼*

~21 January 2020~
       07:00AM

_______________________
'''SACRIFICE TO:'''
*_NUSAIBA Y GIƊAƊO_*
*(UMMU MUHSIN)*
_______________________

         ∇ΩTΣ & ҒΩLLΩШ 4ШΔTTPΔD
            @OUM-RAMADHAN1433

بسم الله الرحمن الرحيم...

*SΣRIΣS 22*

*__________📖* "wanna kashedi nayi maki akan shiga hurumin matata?".

"amma taya zan bari ƙaramar yarinya kamar wannan ta raina ni, gaskiya Sultan bazan iya ba,bazan iya bin umarnin ka ba indai akan haka ne".

cikin salo na mugunta ya sake barƙalo da wuyan ta ta gefe.

"wannan ya zama kashe di na ƙarshe da zan yi maki Nadeeya, kallon banza kika kuma matata sai kin gane baki da wayo".

ya sake ta yana binta da mugun kallo.

"amma Sultan wannan ai rashin adalci ne kake nunawa, ya kake fifi-tata akai na, yanda take matar ka nima fa haka nike matar ka....".

maganar ta tsaya mata sakamakon hannu daya sa ya matse bakin nata gaba ɗaya.

"sau nawa zan faɗi maki ni ba mijin ki bane kar ki kuma alaƙanta aure a tsakanin mu?, ke baki da wani matsayi a wuri na face sharar bola, idan kowa na ɗaukan ki matsayin matata to ni ba komi na ɗau ke ki ba face baiwa ta, dan haka ina mai gargaɗin ki da kije ki sake bin hanyar da kika sa aka ƙulla wannan aure a war-ware shi, ni ba zaki taɓa kasancewa matata ba domin bazan taɓa haɗa Angel da wata ba, idan kuma kin ƙi to ina maki maraba da shigowa ƙoramar wahala".

ya sake bakin nata yana ƙyasta mata hannu,
"and this should be the last worning da zan yi maki, kar ki ƙara bin hanyar da Heenat take bare har ki saukar mata da ɓacin rai sanadin ganin ki".

ya ƙarashe faɗi mata yana mai take mata yatsun ƙafar ta da takalminsa, ƙarar zafi ta saki ta shiga bashi haƙuri tare da ƙoƙarin janye ƙafar.

ransa matuƙar ɓace ya fice daga ɓangaren nasa yayi na shi, hana dakawa bin sa yayi, a ƙasan malelen carpet ɗin dake parlo'nsa ya zauna.

hannu ya miƙa saman wani glass table ya ɗauko giya ya fasa ya kwan-kwaɗa kana ya kunna siggaret ya shiga zuƙa.

daga saman kujerar ya kishingiɗar da kansa tare da lumshe ido'nsa da sukai masa zafi.

Nimrah ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakin ta har ta ƙaraso gaban sa bai ma sani ba, tana ta masa magana sam bai san tana yi ba, hannu tasa ta ɗan bibbigi kafaɗar sa, a hankali ya buɗe idon yana kallon ta.

tace dashi, "kazo inji Mami".

duk da sama-sama yaji zancen nata amma ya gane abinda tace, sai daya ɗauki kusan minti biyar kana ya ɗaga mata kai alamun yaji.

bai tashi ya amsa kiran Mammy ba sai daya ɓata kusan awa ɗaya, a cikin ɗakin ta ya sameta hadima'nta suna mata hidima, daga masu tausa sai masu firfita.

ganin shigowar sa duk suka miƙe suka fita suna masu rissinawa.

yana tangaɗi ya ƙarasa wurin ta, zama yayi ya kwantar da kan sa saman cinyar ta.

hannu tasa cikin sumar sa saboda ganin irin yanayin da yake, kamar yanda damuwa ta bayyana ƙarara a fuskar sa haka itama.
cike da so da kulawa take shafa gefen fuskar sa, tace dashi,

"ba damuwa ya kamata ka sawa ranka ba,ka cire jida kai ka lallashi Rahinat, kai fa namiji ne kasan yanda zakai ka shawo kan kowacce mace, fishin Rahinat akan ka ƙaramin alhaki ne,".

"Mami bazan iya kuma mata komi ba, bana son zama da mutumin da bai sona dan haka zan mata yanda take buƙata, ni ai ba sa'a'nta bane da zata ke raina min wayo tana bin duk abinda taga dama dan ina son ta".

"a'a zancen saki bai taso ba, kasan dai yanda zaka ci gaba da shawo kan ta, kar ka gaji kayi fushi kaji Aayan ɗina, ina so naga kun kasance a tare cikin farin ciki".

kai kawai ya gyaɗa mata sannan ya ɗaga kan nasa daga saman cinyar tata ya miƙe zaune.

abinci ya buƙata data ba shi, dama ita ma abincin zata ci dan haka ta zuba masu tare suka ci.

bayan ya gama ya tashi ya fita daga ɓangaren ta ya wuce na Rahinat.

ko da ya shiga ɗakin ta tana cikin toilet, kwanciyar sa yayi a kan gadon, fitowar ta taga mutum sheme kamar wani matacce.

sai da taja tsoki ta cuno baki sannan taci gaba da goge ruwan ƙafar ta saman foot mat, jin wayar ta tayi ƙara da sauri ta nufa beside drower dan ɗauko, baƙuwar numba ce, tana ɗagawa taji Raihana ce ke magana.

tace da ita, "ni Y Raihana bazan kulaki yanzu ba".

ta kashe wayar ta maida ta ijje.

juyawa tayi zata nufa closet taji ya riƙe hannun ta, a ƙufule ta juyo zata ƙwace, ganin ya kafe ta da shanyayyun idanunsa da suka ƙanƙance sose.

bai bari tayi maganar da take so ba ya fizgo ta ta faɗo jikin sa.
yatsina fuska tayi ta shiga kiciniyar ƙwacewa,

"bana son rashin mutunci ka sake ni, wannan ma ai iskanci ne zaka shigo mani ɗaki ba neman izini kuma ka kwanta min har kan gado,dilla ni ka sake ni".

"haka kike so naci gaba da zuba maki ido Angel, wallahi bayan azabta ta sonki harda addaba ta sha'awar ki ma,plss ki daina wannan fushin dani haka ya isa, ki daina wahalar da zuƙatan mu, mai kike so nayi maki ki haƙura ki daina fushi dani ummm Beauty nah?".

kasa wani motsi tayi saboda yanda yake tafiyar da yatsansa a ƙashin bayan ta ta cikin towel ɗin ta daya zame.

wani yawu ta haɗiye a maƙoshin ta, yunƙura wa tayi zata miƙe ya dawo da ita ta hanyar kamo buttocks ɗin ta ya matse ta da jikin sa gaba ɗaya.

"أرجوك قل لي".

ya faɗi yana mai hura mata iska cikin kunne.

*#Vote,Comment,Share&Follow.*

*©MISS XERKS•*

PRINCE KHALEED Completed.Where stories live. Discover now