SERIES 3

2K 104 9
                                    

♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
     *PRINCE KHALEED!*  
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
             _Continuation_
       _of ƘADDARAR SO!_
♥ω♥°♥ω♥°♥ω♥

         
      
      ©®
*MISS XERKS*✍🏼

       *BESTOWED TO:*
*XUMUNT@ NOVELL@ GRP*📚

~24 June 2019~.
       22:00PM

_______________________
'''SACRIFICE TO:'''
*_SANAZ DEEYAH👄_*
_______________________

         ∇ΩTΣ & ҒΩLLΩШ 4ШΔTTPΔD
            @OUM-RAMADHAN1433

بسم الله الرحمن الرحيم...

*IDAN HAR FITSARI BANZA NE KAZA TAYI MANA,RUBUTU DA KUKE GANINSA BAIWACE,MU KUMA DA MUKE ZAMAN RUBUTASHI BA AIKINYI MUKA RASA BA WE HAVE ALOT TO DO ,KUMA KU BAR TINANIN DAN IYAKA NISHAƊINKU MUKEYI,NOOO KUNYI KUSKURE HARMU KANMU DA MUKE RUBUTAWAR, DAN HAKA DUK WANDA YA ZAGI WRITERS BAN SAN DA ABINDA ZAN KIRASHI BA FACE WAHALALLE MARA AIKINYI*...

_Dedicated to Hauwa M.u Smasher sakallahu khairan da kulawarki agaren._

*SΣRIΣS 3*
*NOT EDITED*❌

••••Zaune Nadeeyah tayi shiru bisa katafaren gadonta tayi tagumi, baiwar dake tare da iita ke tambayarta,

"ranki ya daɗe naga kamar kina cikin damuwa, ko lafiya?"

bataji ta ba har saida ta sake magana a karo na biyu sannan Nadeeyah ta ɗago ta kalleta.

kamar bazata bata amsa ba can kuma tace,

"babu komai,kije kawai ina son hutawa"

"tom ranki shi daɗe,ahuta lapia"

daga haka ta fice tabar ɗakin.

fitarta Nadeeyah ta miƙe ta shiga wanka, bayan ta fito ta gabatar da sallolinta kaman yanda ta tarasu akanta over dan rabonta da sallah tin shekaranjiya.

bayan ta idar ta kwanta domin yin bacci amma sam yaƙi zuwa.

yanzu ya zatayi idan har Papi ya koreta itama a wannan masarautar? ina zata nufa dan neman Khaleed bayan bata san inda yay ba? toko saudia zataje,amma idan taje tabbas babu mai saurarenta tinda sun san anwa jikansu laifi,wurin Abbi shine abinda ɗaya zuciyar tata ta sanar mata.

aikam da sauri ta miƙe zaune,saukowa tayi daga saman gadon ta nemi doguwar rigarta baƙa ta sanya sannan ta ɗora blue ɗin hijab, kasancewarta fara ƙal sai tayi masifar kyau acikin hijabin.

kallon fuskarta take cikin madubi,duk ta faɗa kaman mai jinya, ko dayake jinyar take wadda tafi ko wacce jinya zafi, tabbas rasa khaleed shine ƙarewar rayuwarta.

tsaye tayi tana saƙawa da warwarewa akan zuwa wurin Abbi,tinawa da bai cikin masarautar yana can president house yasa ta koma ta kwanta haka har bacci ya ɗauketa.

washe gari bata sami daman farkawa sai kusan 12 ta tashi da ciwon kai.
wanka tai ta fito tai shirinta mai kyau tare da sanya rantsetsiyar alkyabbarta.

zama tayi ta sanya wayarta gaba tana kallon hoton Khaleed dake kan screen ɗin wayarta,murmushi tai ɗan ƙarami tare da lumshe ido taja gajeran numfashi.

_ko yanzu ya ya koma,nasan tabbas ya ƙara kyau fiye dana da,insha'Allahu yau zaka zama mallakina Aayan kuma da yardar Allah saina sami matsuguni a zuciyarka._

gabanta ne ya faɗi ras lokacin data tina fa yana da aure wataƙilan yanzun ma yana da yaro ko yarinya,hawaye masu ɗumi suka shiga bibiyar kuncinta, wannan wacce irin ƙaddara ce ta so ta kamata,ta rasa wanda zata so sai wanda inuwarta bai ƙaunar gani a rayuwarsa sunan wai tana ƴar'uwarsa.

PRINCE KHALEED Completed.Onde histórias criam vida. Descubra agora