Tsokaci

20.2K 1K 93
                                    

To my three musketeers, for what we lost, I AM SORRY, for what we had I WILL FOREVER BE GRATEFUL.

WAHIDAH SHU'AIB HAROON. This is for you. Thank you for the was, is and yet.

YUSRA ABDU FARI there is strength in every weakness. We don't need blood to define US.

MY FAMILY. May we find each other in JANNA. Amin thumma amin.

**********

"Mutumin da kike so na tare da uniform din nan, ban san waye ni batare dasu ba, ban taba son kaina babu su ba, bana tunanin zaki iya"

Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amman sunki zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji zasu kasance cikin addu'arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matukar radadi.

"Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba mika maka dukkan zuciyata bane yake mun wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, bazan damu da raba soyayyarka da Uniform dinka ba, shi din da yafi ni muhimmanci ne matsalar"

Ta karasa maganar tana jin dacin son kan da take son yi a harshen ta, zabi take bashi, ita da take bakuwa a rayuwar shi ko Uniform dinshi daya girma da soyayyar shi? Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta dago nata su sauka cikin su, amman taki yarda hakan ya faru.

"Waheeda..."

Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kadai yake iya hakan.

"Karki ce mun in zaba... Ba zaki so amsar ba"

Runtsa idanuwanta tayi tana bude su da wani irin ciwo. Me yasa yaki ganin abubuwan data sadaukar saboda soyayyar shi.

"Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform dina muhimmanci ba...karki so kanki da yawa haka"

****

Assalamu alaikum.

Kaman ko da yaushe alkalamin rubutuna baifi na kowa ba, sai dai yasha banban dana sauran. Ban yarda da wani abu mai kama da happily ever after ba, sai dai akwai farin ciki na yau da kullum, farin cikin dakan zo da nutsuwa ta ban mamaki.

Wannan karin tafiyar ta banbanta da kowacce, saboda korafin da nake samu a kowacce tafiya. Karo na farko da jigon tafiyar zai ginu kacokan akan SOYAYYA. Zaizo a manhajar wattpad da whatsapp a kyauta.

#AnaTare
#LubnaSufyan
#FWA

ABDULKADIRWhere stories live. Discover now