07

7.9K 679 148
                                    

Zaune take gaban mudubi badan zatai kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta sakama jikinta riga da wando na Pakistan, ta dauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna batare da tasan asalin abinda take tunani ba. A hankali ta dauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken kara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta tayi baya da kujerar da take sama tana mikewa tsaye. Madai-daicin tsayin da take dashi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta.

Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riqe da hijab

"Ke ba dake za'aje kun shin ba?"

Mami ta bukata, tana kallon Waheedah data girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yanda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah din tace a aji shidda sakandire, Waheedar tace take shirin zana jarabawar gama aji shidda, ko Amatullah ta gitta sai taita kallon su, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take ma fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zaiji abinda ake ji.

"Jikina yamun nauyi Mami, suje abinsu, nace Amatu zata sakamun jan lalle idan zamu kwanta..."

Waheedah tai maganar tana katse wa Mami tunanin da take.

"Allah ya kaimu... Zamu fita kasuwa da Haj. Halima"

Kai Waheedah ta jinjina tana fadin

"Saikun dawo..."

Tsaye tayi har saida taga Mami ta fita daga dakin tukunna, daga nan cikin dakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da zasu sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta baya mata ciwo, dan bawai tana son hayaniya bane, amman biki yara uku ita kanta tasan saidai suyi hakuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za'a daga, dan ginin shi ko rabi baikai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai daki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi.

Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulkadir ne manne da zuciyarta, zata iya cewa tun tafiyar shi da rana daya bai taba barin tunaninta ba. Lokutta da dama tana tashi daga bacci takanji kirjinta yai mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara daya akace zaiyi yazo gida, amman yanzun shekaru biyu kenan. Watannin baya kasa hakuri tayi, batasan lokacin da tambayar ko yana lafiya ta subuce mata a gaban Abba ba, shine ma yace mata yaje ya duba shi sau daya. Yana lafiya, tukunna taji tadan samu nutsuwa ta wasu fannonin.

Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma'a. Ta rigada ta saba data idar da sallar asuba take karantawa, yau din bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, dan duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja. Tunanin taje ta dauko Qur'an din takeyi, Aminu ya shigo da sallamar data amsa mishi cikin sanyin murya

"Commander an diro..."

Ya fadi yana dariya, hadi da wucewa kitchen, muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma'anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta taji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, dan yanda ta fara doka mata, in bata miqe ba, tanajin tsaf zata fito daga kirjinta tayi kafafuwan kanta ta fice daga dakin dan neman duk inda Aminu yace Abdulkadir din yake. Mikewa Waheedah tayi tana saka hannu ta dafe kirjinta, inda take jin zuciyarta na kara gudu da duk daqiqa. A bakin kofa ta zira takalman bandaki da batasan ya akai suka zo wajen ba. Manya-manya ne, karamar kafarta na yawo a ciki, amman bata ma kula ba.

Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, kafafuwanta take takawa tana nufar bangarensu, badan sun taba doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amman tanajin wata irin sanayya da tai mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in akazo maganar sanin halayen shi. Abdulkadir din data sani bazai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa bangarensu zai wuce yaga mahaifiyar shi, banda Abdulkadir, zai iya jira, daya shiga hayaniyar da take bangaren Hajja gara ya jira. Tana da tabbacin yana bangaren su.

ABDULKADIRWo Geschichten leben. Entdecke jetzt