27

8.5K 949 249
                                    

AbdulKadir Comments
Zauren Biebee Isa
Wattpadians
Daukacin makaranta AbdulKadir
Godiya mai tarin yawa
#SonSo saboda Allah

A waya Hajja ta kira mishi Abba, amman ca yayi bayason ganin AbdulKadir din, idan sulhu yake nema yaje wajen Waheedah, shi kam ba zai saka musu baki ba. Da wani irin sanyin jiki AbdulKadir yabar gidan. Amman tsintar kan shi yayi da nufar hanyar gidan Yassar, ba zai iya zuwa gida ba, har a kasusuwan shi yakejin bukatar Waheedah a kusa dashi. Bai taba zaton zaiyi kewarta irin haka ba, ko watannin da yakan shafe batare da ita ba, inya tuna cewar tana gidan shi, tana jiran komawar shi kan nutsar da wani bangare na zuciyar shi.

Amman yau yana gari daya da ita, da auren shi a kanta ace ta kwana bakwai bata cikin gidan shi, gidan su, abin yana ci mishi zuciya fiye da yanda zai iya fadi. Gidan Yassar ya karasa yana parking din motarshi, a jiki yabar mukullin yana fitowa, ya karasa bakin kofa yaci karo da Yassar din da yake girgiza kai

"AbdulKadir..."

Katse shi AbdulKadir yayi da fadin

"Hamma dan Allah, banajin tashin hankali, magana kawai zan mata, dan Allah karka cemun wani abu, na roke ka"

Da bayanannen mamaki Yassar yake kallon AbdulKadir, yasan kaf gidan su daga su Hajja sai shi AbdulKadir kan dagawa kafa lokutta da dama, amman Yassar yasan su Hajja kawai yake saukewa murya irin haka, ya kasa yarda da AbdulKadir ne a gabanshi yake rokon shi alfarma yau. Mutane kan ce in da ranka ka sha kallo, kallon yake sha yanzun. Rabashi AbdulKadir yayi yana wucewa cikin gidan, yaji dadi da baici karo da Hauwa ba har ya karasa dakin da Waheedah take ya kwankwasa tukunna ya murza hannun kofar yana shiga.

Ta sake kaya, rigar bacci ce a jikinta, doguwa har kasa. Kalar rigar bata dami AbdulKadir ba, idanuwan shi na kan fuskar Waheedah da take kallon shi da gajiya shimfide cikin idanuwanta, takawa yayi ya karasa gefen gadon yana kama hannuwanta ya dumtse cikin nashi

"Me yasa zaki karya alkawarin ki? Kince ba zaki barni ba, da bakin ki kin sha fadamun zaki kasance tare dani.... Wahee in ke zaki iya barina ni bazan iya barin ki ba.... Wallahi ba zan iya ba"

Kallon shi Waheedah take tunda ya fara magana, amman zuciyarta a bushe take ballantana kalaman shi suyi mata tasiri, a hankali ta tara abinda ya kawota inda take yanzun, batajin akwai kalaman da zasu canza ra'ayinta. Hakan AbdulKadir ya kula dashi, ya sake dumtse hannuwanta da ta fara zamewa daga cikin na shi.

"Waheedah ni ne fa, ki kalle ni, ni ne, ban aureki dan in rabu dake ba..."

Ya karasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryar shi, yana kasa yarda Waheedah ce take son barin shi. Yana tuna lokacin da aiki ya kaishi tsakiyar inda ake tarzomar yan boko haram a Maiduguri.

*

Ta dauka tashin hankalinta kan aikin shi ya fara tsagaitawa, sai da aikin ya daukar mata miji yayi Maiduguri da shi. Tana da cikin Fajr wata kusan bakwai. Ko yaushe wajen awo ca suke mata ta kwantar da hankalinta, amman tasan ita da kwanciyar hankali sunyi hannun riga har sai AbdulKadir ya dawo gida. Kasancewar in da suke babu network, duk Asabar yana samu ya fito ya kirata, idan bai kirata ba, wani idan ya fito cikin abokan aikin nashi zai turo mata da sakon AbdulKadir din. Yanda kwanaki kan wuce mata tsakanin Asabar zuwa wata Asabar din ba zatace ba.

Sai dai duk wani tashin hankali da take tunanin ta taba shiga, ko ta taba jin labari bai kai wanda take ciki a yanzun da satika uku suka wuce batare da labarin AbdulKadir ba, wata na hudu yake nema lokacin a Maiduguri, bai kuma taba wuce sati biyu bataji daga wajen shi ba. Ya fada mata idan sati hudu suka wuce bai kira ba, ko sakon cewar yana lafiya bai sameta ba, to wani abin ya faru dashi, tayi mishi addu'a. Kukanta bai tsananta ba sai da satika hudun suka cika babu labarin AbdulKadir, musamman da su Hajja suka fara kiranta suji ko AbdulKadir din ya kira, Anty ma ca tayi zata zo ta dauketa su koma gida, tunda ga cikin ya tsufa, ga kuma tashin hankali, sai dai ba zasu gane ba.

ABDULKADIROnde histórias criam vida. Descubra agora