24

8.9K 861 379
                                    

Wayar tasa a chargy kamar yanda ta fada mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da tayi. Wayar take kallo tana gane asalin ma'anar 'Yawo kan gajimare'. Duk da ba zatace ga ranar da wuyanta ya gajiya da daukar nauyin kanta ba, yau kan jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta. Kafin kan nata yai wata irin sarawa cike da fahimtar ma'anar

'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan ya zan fada miki ba'

Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta takeji yana barazanar kin wuce kirjinta yakai inda zai ba zuciyarta damar cigaba da dokawa yanda ya kamata. Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da takeji yafi karfin hawayenta.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ta samu furtawa tana zama sosai kafin taja kafafuwanta ta dora kanta a sama ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taba shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da zata shiga tafi waccen wahalar sha'ani ba sai yanzun. Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin kasusuwan jikinta. Idan tace ga asalin abinda ya fi mata ciwo karya take.

Auren da yayi da batada darajar da zata sani kafin a daura shi, kallon idanuwanta bayan an daura din dayi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zabar ya fada mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta sakon waya.

"Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki? Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al'amari ba?"

Waheedah take maganar kamar zararriya, dan batasan a fili takeyin ta ba, ta dai san daga wani bangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa. Bata san iya lokacin da ta dauka a zaune tana kallon bango batare da tasan asalin abinda take tunani ba, banda wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi batajin komai. Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, dakyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar

'Sadauki'

Ta gani rubuce a jiki

"Me kake so dani Sadauki?"

Ta tambaya tana kallon wayar harta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa. Hannu ta mika ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran hadi da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya tace

"Hello..."

Tana mike kafafuwanta da sukai mata sanyi, ga abinda ke cikinta da taji ya dunqule waje daya kamar yana tayata daukar ciwon da takeji, hakan nasata fahimtar wani irin ciwon mara da batasan tun yaushe ya fara mata ba.

"Kin fara bacci ne?"

Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da taji muryarshi na kara mata ciwo, taji da magana dashi gara mata kallon bangon da takeyi, shi baya kara mata ciwo, amman muryar AbdulKadir din kamar gishiri a sababbin ciwukan da yaji mata takejinta.

"Na sa chargy ne"

Dan jim yayi ta dayan bangaren kafin yace

"Inata kira tun dazun babu network"

Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri

"Har kun taho?"

Ta tsinci kanta da tambaya

"Tun dazun, amman cunkoso har yanzun muna cikin Lagos"

Kai ta jinjina mishi

"Allah ya tsare maka hanya ya kawo ka lafiya"

ABDULKADIRWhere stories live. Discover now