13

8.7K 666 204
                                    

"Mutumin da kike so na tare da uniform din nan, ban san waye ni batare dasu ba, ban taba son kaina babu su ba, bana tunanin zaki iya"

Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amman sunki zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji zasu kasance cikin addu'arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matukar radadi.

"Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba mika maka dukkan zuciyata bane yake mun wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, bazan damu da raba soyayyarka da Uniform dinka ba, shi din da yafi ni muhimmanci ne matsalar"

Ta karasa maganar tana jin dacin son kan da take son yi a harshen ta, zabi take bashi, ita da take bakuwa a rayuwar shi ko Uniform dinshi daya girma da soyayyar shi? Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta dago nata su sauka cikin su, amman taki yarda hakan ya faru.

"Waheeda..."

Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kadai yake iya hakan.

"Karki ce mun in zaba... Ba zaki so amsar ba"

Runtsa idanuwanta tayi tana bude su da wani irin ciwo. Me yasa yaki ganin abubuwan data sadaukar saboda soyayyar shi.

"Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform dina muhimmanci ba...karki so kanki da yawa haka"

**

"Adda! Addaa!!"

Idanuwanta da take ji sun mata nauyi ta bude, tana jin Amatullah ta kwashe da dariyar da ta sata jan karamin tsaki, dan mafarki take, kamar yanda a kwanakin nan mafarkan AbdulKadir din suke addabarta. A cikin daya daga mafarkan ta kira shi da Sadauki, tun bayan tashin ta tsinci kanta da kiran shi Sadaukin dan sunan ya dace dashi ta kowanne fanni. Batasan murmushi ya kwace mata ba saida taji Amatullah ta sake kwashewa da dariya

"Addaaaaa!"

Hararta Waheedah tayi da yasa Amatullah din sake yin dariya

"Jiba inda kike bacci fa, cikin kaya"

Miqa Waheedah tayi hadi da yin hamma tana miqa hannu ta dauki wayarta qirar Nokia Symbian E5 dake ajiye a gefe ta danna dan ta duba lokacin, karfe biyu harda kwata. Gabaki daya jikinta a gajiye take jinshi.

"Anata nemanki fa..."

Kai Waheedah ta dagama Amatullah din, tana kallo ta fice daga dakin. Zaune tayi a wajen tana tunanin ta inda zata fara miqewa, gajiyar da take ji har cikin tsoka da kasusuwan jikinta. Idanuwa ta lumshe, fuskar Abdulkadir na mata yawo, wata irin kewar shi take ji taban mamaki, zata alaqanta hakan da jimawa da tayi bata ganshi ba, tun hutun da yazo na sallah, shima ranar idi ne, tun da suka dawo daga masallacin idi bata sake sakashi a idanuwanta ba harya tafi. Satin da zata fara zuwa makaranta, Babban Yaya ya basu wayoyi, taga cikin mazan gidan ma kusan duk ya ba 'yan matasan. Matanne yace sai sun gama aji shidda.

Sosai taji dadin kyautar wayar har ranta. Yassar ya saka mata manhajar kafofin sada zumunta, ciki harda Whatsapp, har kati Yassar din ya saka mata. Lambar Abdulkadir ce ta farko da tazo sakawa taga Yassar duk ya saka mata lambobin su. Sunan kawai ta sake zuwa Sadauki. Shi kuma ta fara dubawa a whatsapp, sai lambar ta nuna bayayi. Sosai zuciyarta taji tai mata nauyi, lambar Yazid ta nema taga Yassar ya saka mata, shi kuwa yana Whatsapp. Sallama tayi mishi tana fada mishi itace. Shima tayi kewar shi ba kadan ba. Zata iya cewa shima tun bayan Sallah da canjin wajen aiki ya dauke shi zuwa Abuja.

Sai kwanaki da akace mata ya shigo, ita kuma taje gidan kanwar mahaifinta, kuma ba sosai take kwana ba, ranar dai rabon ba zata hadu dashi bane yasa ta kwana din, taji takaicin abin. Ta kuma yi mamakin da Yazid baije can din ya sameta sun gaisa ba, Yazid din data sani zai nemeta, bazai zo Kano bayan watanni masu yawa ya koma basu gaisa ba. Sai dai Zahra tace mata da Asuba ya wuce, a cewar shi ayyuka sun mishi yawa. Abdulkadir din kuwa text tai mishi tana fada mishi itace, tukunna ta sake tura mishi wani tana tambayar lafiyar shi. Kasa hakura tayi duk da bai amsa mata sauran sakkonin ba, ta tura mishi wani tana cewa bata ganshi a Whatsapp ba, ya bude.

ABDULKADIRHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin