29

10.9K 1K 431
                                    

Tsugunnawa yayi yana fitar da numfashi a wahale, cikin shi ke ciwo saboda hanjin shi da yakeji sun tattaru sun kulle a gefe daya. Ko ina na jikin shi ciwo yake, har wajajen da bai taba sanin zasuyi mishi ciwo batare da zubar jini ba. Waheedah na tsaye tana kallon shi, yanda yakeyi kamar shi yayi watanni da ciwon da tayi fama da shi, a karo na farko halin da yake ciki bai taba zuciyarta ba, tana jin dadin yanda yake jin kadan cikin quncin da zuciyarta take fama dashi

"Kirjin ka kamar zai bude ko Sadauki?"

Ta bukata cikin wani irin sanyi murya da yasa AbdulKadir daga idanuwan shi da har sun canza launi yana kallon ta, rausayar da kai tayi

"Haka nake ji duk idan naganka tare da Nuriyya..."

Mikewa AbdulKadir yayi yana karasa inda Waheedah take, hannuwan shi yasa ya kama kafadunta yana dan dannawa cikin alamun ta zauna, batayi mishi musu ba tayi kasa tana zama kan kafet din dakin, shima zaman yayi a gefenta, dan dakin ya fara jujjuya mishi da jirin tashin hankali. Idan taci gaba da magana baisan inda zai saka rayuwar shi ba, ya bude bakin shi ya kai sau biyar amman ya kasa furta komai. Sai da yaja numfashi yana fitar dashi, kafin ya iya cewa

"Waheedah..."

Kalmar na fitowa daga wani sashi na zuciyar shi da yau dinne ranar farko daya san da zaman shi, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, cikin kan shi yake ji babu komai, baisan ko yanajin alamun kwakwalwa ba a baya, amman a yanzun bayajin komai sai kokon kan, balle yayi tunanin kwakwalwar shi zata taimaka mishi da wasu kalamai, amman kirjin shi ciwo yake kamar zai bude, da gaskiyar zancen Waheedah, bai gane yanda zai fassara abinda yakeji ba sai da ta fada, kan shi babu komai, amman zuciyar shi cike take fam da yanayoyi daban-daban, bude bakin shi yayi yana barin zuciyar shi ta mulki abin zai fito daga bakin shi

"Ina da son kai, ban taba sanin ina da son kai ba sai yau, kina da rashin adalci..."

AbdulKadir ya karasa maganar cikin muryar da ta dira kunnuwanshi kamar ta wanda yasha gudu, yana saka kwayar idanuwan shi cikin na Waheedah da take ware mishi nata cike da maiqon hawaye, kai ya daga mata a hankali

"Me yasa baki fadamun ba? Me yasa baki fadamun ba Wahee? Kince kina sona, ni nagani kina sona, me yasa kika boyemun?"

Kai Waheedah take girgiza mishi, idanuwan ta na tsiyayo wasu hawaye masu dumi, ba zai mata haka ba, ba zata bar shi ya dora mata laifin da bata da shi ba

"Me yasa ka boyemun za kai aure? Ka boyemun kayi aure har wata daya? Ka boyemun Kawata ka aura sai da ka shigomun da ita cikin gida?"

Jinjina kai AbdulKadir yayi, kalamanta duka suna dirar mishi kamar zubar ruwan gishiri a sabbin ciwukan da kalamanta na baya sukai mishi, yasan tana da muhimmancin a rayuwar shi fiye da yanda zai misalta da kalamai, bai dai san a tattare da muhimmanci akwai iko akan abubuwa da yawa da suka shafe shi ba, ciki harda zaman lafiyar shi, kwanciyar hankalin shi, nutsuwar shi gabaki dayan ta

"Hakane..."

AbdulKadir ya iya furtawa yana kallonta da wani nisantaccen yanayi, muryar shi yakeji na fitowa da wani sauti da baida fasali

"Ba uzurin da ya sani yin abinda nayi nake so in baki a kurarren lokaci irin yanzun ba..."

Ya fadi yana maida numfashi kafin yace

"Banda komai, ko kalaman ban hakuri bani dasu, wallahi banda kalaman baki hakuri"

Dan har zuciyar shi yakejin hakuri yayi kadan ya wanke girman laifin da yayi mata

"Shisa zan baki wani abu daban, zan baki dukkan gaskiyata, ban san zanyi aure ba, lokaci daya tunanin ya zo mun..."

Kai Waheedah take girgiza mishi, bata son ji, bata son jin yanda yayi aure, tunda ya rigada yayi, shima kan yake girgiza mata

ABDULKADIRWhere stories live. Discover now