Jumma'at Kareem from Mimsqueen Allah yataimaka yabiya mana bukatunmu na Alkairi ya tsaremu daga dukkan sharri Ameen 👏 next update I won't promise you a weekend it depend on yadda nasami kaina no hard feelings guys love you😘
Yau antashi da wani irin yanayi dan Maijiddah tafarfado anma saboda yanayin yadda ta farfado hospital aka wuce da ita direct
Dan Abdul na barin gidan Zoya aka sanar dashi ko gun Amarya bai sama zuwa ba sai text ya mata ita da Rukayya karsu jishi shiru,
Ran baby iya baci ya baci Jin Maijiddah ta farfado Sam bata so hakan ba gaba daya
Attention din kowa kanta ya koma da safe Abdul yace driver ya kawo su ita da Rukayya hospital dan 'yan uwa nacan Ana addu'a kanta,
Ko wacce ta fito cikin Isa da takama inda Rukayya ta bude gidan baya tashiga kallon banza baby tabita dashi tare da ciro key din motar ta
" hajiya Alhaji yac......"
" no Karka damu nazo da mota ta daga gidanmu dama I don't need hada kafada da talaka"
Sosai zancen ta ya daki Rukayya amma saita share ta sauke glass din " Dadinta mace gidan ta shine gidan mijin ta abunda yabata dashi take tinkaho sai dai kash na tausaya miki ragowa zaki samu dan haka kiyi a hankali muje kaji"
Tsayawa baby tayi Tana kallonta tabbas taci mata fuska amma bakomai zata gangaro kanta sannu a hankali mtsw tayi tsaki tashiga tata motar.Tunda tafito take saurar music din amma gaba daya ranta baya mata dadi kashe wakar tayi
" I have to deal with that fool first" Tafada tana tafe Tana tsaki wayarta ce ta shiga ringing,
Dauka tayi da sauri " inakika shiga tun tuni nake neman ki"
" sorry darling kinsan akwai gajiya fa infact meya tada ke da wannan Safiyar iye"
Tsaki baby taja tare da tabe fuska kamar Tana ganinta
" hmm wannan shanyayyar matar tasa ta farfado tun dare dan iskanci"
" wayooo Allah Allah ubangiji ya bata laf....,"
" dallah malama niba addu'a nakira kiyi ba kawai inason Jin ko akwai Wanda kika sani a hospital din doctor Sa'ad" shiru billy tayi
" no but wata friend dita tasani yes Nima nasan yarinyar Nurse ce but why do you ask"
" I want to kill that bitch"
Wani irin nishi billy tayi kamar wacce aka tado tace " No ba zaki kashe kowa ba is unlike you kawata you are not a killer please"
" shut up ba permission dinki nake nema ba I have made my mind"
" please baby ki cire wannan shawarar a ranki karki manta kinsama Abdul a hannu tunda ya aure ki me kuma kikeso ki achieving please"
Murmushi baby tayi ta kashe wayar." billy kenan inama zaki fahimci damuwa ta gefe she is Zoya sister, doctor Sa'ad love, Abdul wife
" dole she must die for us to enjoy all"
Maida music dinta tayi gudu take sosai a hanyar
Tariga su Rukayya Isa hospital din Abdul na kokarin fita siyo wasu allurai yaganta,
Tsayawa yayi yana kallonta har tayi parking tafito Tana hango shi ta kawata fara'arta
" oyoyo sweetyna"
Tafada sanda take shirin hugging dinsa ja da baya tayi Tana murmushi
" no worry I understand kana bukatar lokaci ko"
Girgiza kai yayi dan yana da abunda yafita damuwa a gunshi burinshi Allah yatashi kafadun Maijiddah
Shigowar su Rukayya yakara tsaidashi a gate din inda tagaidashi ya amsa cike da fara'a haryana wasa da Yasmin wani irin kishi yakara rufe baby,
Ganin haka yasa ta shige ciki abunta itama Rukayya bayan sun gaisa yashiga motar dan driver yakaishi ta wuce ciki itama sosai take so Maijiddah ta tashi kodan auren da Abdul yayi
At least tasan Maijiddah akan wannan sabuwar fuskar shiga ciki itama tayi inda suka tarar da yan uwa dayawa sukai gaishe2
Still ba'a cewa komai kan jikin Maijiddah din a wannan lokacin sam doctors sunki magana akai sai dai suce abasu lokaci.Zoya na kwance Tana bacci taji nanny na knocking din kofar ta a hankali ta bude ido
Duba time tayi taga is 10am already " oh ya Allah"
Tafada sanda ta tashi da sauri ta bude kofar " nayi bako ko"
" no ma'am doctor ne dadyn Amyra"
" alright ki fada mishi Ina nan zuwa Amyara fa"
" she is with him ma'am"
" alright you can go"
Murmuring tafara ita kadai sanda take tubewa " what brings him here at this time"
Cigaba tayi da mita sanda ta wuce toilet din sosai ranta ke bace a wannan lokacin dan bashi take expecting ba a yanzu.
" Dady why are you not living with us even in Nigeria"
" nothing my angel"
" but dady you once told me you will when we get back here"
" yes my angel"
Yafada kanta kallonsa kasan yana cikin damuwa,
" why dady you are always not with us and momy"
Kallon innocent yarinyar yayi ya rungumota wasu hawaye masu zafi ke fita daga idannunsa
Yana matukar son Amyara kamar yar cikinsa hakan yasa inyana tare da ita yake iya pouring duk problem dinsa,
Shiru tayi a jikinsa can ta soma bubbuga mai baya wayo ne da ita sosai hakan yasa shi murmushin dole.Koda Zoya tafito tsayawa tayi a gefe batare da sun saniba Tana kallonsu tabbas Sa'ad mutumin kirki ne Wanda yake kaunarta matsayin yar uwa,
" dady Why are you crying"
Share hawayensa yayi tare da dagota " no my angel I am not crying you see" sa hannu tayi tana sake goge mai ragowar hawayen dake face dinshi,
" momy always cry a lot"
Mamaki yaji yana kallonta kenan Zoya na kuka dama ko dake ba mamaki dan suna cikin matsala daya harta fishi damuwa
" is alright my angel go to nanny and ask her to make some tea for dady"
Zoya tafada ganin Sa'ad Yafada duniyar tunani hakan ya farfado dashi
" meya faru doctor"
Kallonta yayi yamai da kansa kasa " Zoya is your sister"
Cike da damuwa da tsoro ta zauna Tana tambayarshi
" meya faru please tell me is she fyn ba abunda ya sameta ko dan Allah fada mun"
Ganin yadda ta shiga damuwa yasa yafara kokarin calming nata dakyar ya Shawo kanta ya sanar mata da abunda ke faruwa
Daukan key din motar ta tayi " zanje hospital"
" no please Zoya not in your state"
" aa niyanzu zan tafi"
Amyara dake saurarsu Sam tadai ga momyn ta na kuka dady na bata hakuri saita sa kuka.Kukanta yasa suka koma lallabata dakyar suka sama kanta tayi shiru nan doctor yace
Su tafi tare nan suka lallaba Amyra suka barta dan haryanzu ba'aso Abdul ko family su san da ita sam
Tukasu yayi basu dau lokaci ba suka Isa hospital din
Zoya bata jira fitowar shi ba tasa kai ciki Tana zuwa tafara tambayar jikin yar uwarta Sam idonta ya rufe bata iya gane kowa agun,
Wani dattijon dake zaune kusa da momyn Maijiddah ne ya tashi ya nufeta inda yaja hannunta ya manna mata wani mahaukacin mari
Sautin marin yaja hankalin jama'ar dake zaune gun hatta baby saida marin ya tsorata ta
Abdul kuwa kasa tak yayi agun dan ba Wanda yayi expecting hakan,
Kafin tagama dawowa hayyacinta yaja hannunta yayi waje da ita su Abdul ne suka bishi da sister din Zoya suna ba dadyn nasu hakuri
Bai ajiye Zoya ko inaba sai a harabar hospital din ya saki hannunta " Meya dawo dake meyasa kikeson shiga cikin rayuwarmu bayan bamu bukatar ki bayan ke
" zainab kinzabi karuwanci akan mu kinyi fatali da dukkan tarbiyar da muka baki kije duniyace ta isheki riga da wando"
" dady dan Allah ka saurareni walh ba abunda kake zargi bane"
Saki hankade ta yayi Tana kuka " nasha fada miki not to ever show your face in my presence ko ba'ayi haka ba".Komawa tayi gaban momyn Maijiddah " dan Allah momy kitaimakeni kifada ma dady gaskiya"
Hankade ta momy tayi inda ta juyo kan Abdul Wanda tun kafin ta karaso ya juya mata baya
Jawota dadynta yayi zaikara wanka mata mari sanda doctor Sa'ad ya tare mamaki ne yakara Kama mutane especially ma'aikatan hospital din,
Jikin doctor har rawa yake ganin idanun yan uwa da ma'aikatan su yasa yashiga ba dady hakuri,
Da lallashi kan koma me tayi bai dace ace sun tsaya a cikin jama'a suna magana ba hakan bai dace ba,
Dakyar doctor ya kashe matsalar har saida jamaa suka shiga sannan dady ya koma ciki
Inda su Abdul suka bishi aka bar Zoya zaune Tana shekar kuka me mugun ciwo doctor Sa'ad ne ya lallaba ta tashi ya kaita Motarsa
Saida ya bude mata tashiga kafin ya koma side dinshi ya shiga tunda yatada mota yabar hospital din ba abunda yake Ji sai kukanta,
Sosai yake feeling din kukan a ranshi yarasa meyasa ya damu da lamuranta damuwarta jiyake kamar tasa..................(doctor why do you take the trouble injini mimsqueen).Happy Friday to all my readers I really appreciate your vote, comments everything sorry yesterday bansama reply comments ba I wasn't feeling alright thanks all👏
YOU ARE READING
RASHIN DACE
Romancewani ihu sukaji da alama ta can baya ne da sauri suka nufi bayan, Inda suke Jin hayaniya " na duke ta kiyi wani abu akai", " Rukayya ni kike fadama kinduke ta din ni sa'arkice", Tafada tana nuna ta da hannu ita kuma sai murguda baki take tana harart...