Chapter 51: You Reap...........S

2.3K 195 19
                                    

Today Is Monday blah......blah.... kunriga kunsan me zance kan day din already so I will no hold you back what are you waiting for scroll down and start reading your favorite Story Have a Wonderful time but do not forget my share....votes, comment and also share the more you comment the more I type always I mean it👌


🅿️111 to 112

Yamma ne sosai kusan 5pm Abdul ne zaune a harabar gidan su yana latse2 phone dinshi
Horn din da ake ne yaja hankalinsa yabi gate din da kallo lokacin da aka me gadi ya wangale gate din hancin motar dady ta danno kai,
Tashi yayi ya nufi motar fitowa dady yayi ya rufe motar da key " sannu Alhaji"
Me gadi Yafada daga mishi kai dady yayi alamun yaji " sannu da dawowa dady"
Kallon Abdul dady yayi irin na kur Nina sama da kasa kamar Wanda yake dan tunani sosai Abdul yaji ya tsargu da irin kallon da mahaifin nasa kemai a wannan lokacin,
" follow me!"
Dady Yafada tare da wucewa direct fallonshi da ba kowa suka nufa dan momy anyi sa'a bata gidan
" bisimillahi!"
Kalmar da tafito bakin dady kenan lokacin daya zauna kan lutsumammen kujerarsa kallon Abdul yayi Wanda kanshi ke kasa yana jiran umarni nodding kansa dady yayi yana kallonsa,
" you can seat"
Dagowa Abdul yayi kamar Wanda baiji abunda dadyn ya fada ba " nace ka zauna"
Dady ya maimaita mishi yana kallonshi kokarin zama kasa Abdul yake shirin yi lokacin da dady ya dakatar dashi " ka zauna kan kujerar i want to have a man to man conversation with you so seat next to me ok".

Zama Abdul yayi yana murmushi shiru sukai na dan lokuta,
" Abdul!"
Daga kai Abdul yayi " na'am dady" ganin yadda dadyn ke kallonshi ya sake maida kanshi kasa
" Abdul!!!"
Dady ya kuma kira wannan karon Abdul be dago ba ya amsa saboda jikinsa da yaji ya mutu tabbas zancen da dadynsa keso suyi mai muhimmanci ne sai da dady yakira sunansa sau uku yayi shiru tare da ajiyar zuciya,
" sau nawa na kira sunan ka"
" sau uku Dady"
Yafada cikin wata irin kasalalliyar murya
" mata nawa nake dasu"
Dagowa yayi Jin tambayar dadyn ganin shi dady ke sauraro yasa yayi saurin Jin kunya ya maida kanshi kasa,
" Biyu!"
Murmushi dadyn yayi " kai kuma nawa gareka da Wanda suke cikin gidanka da Wanda basu nan",
Shiru Abdul yayi kamar Wanda ruwa ya cinyeshi
" Abdul kasan wani sirri"
Dagowa Abdul yayi yana girgiza kai " da a son rainane da mace daya zanyi a duniya mahaifiyarku tabbas da ta isheni rayuwa,
" Amma akwai dalilai da dama wadanda wasu ka sani wasu ba zaka taba sanin su ba kuma tabbas na yarda matar mutum kabarinsa"
Ajiyar zuciya dady yayi yana kallon Abdul can ya nisa ya kuma kallonsa.

" Abdul inaso ka hakura da Zainab a rayuwarka ka manta ka taba aurenta saboda Sam ka kasance Mara adalci a gunta inaso ka daina kallonta matsayin wacce ka taba aura ka kalleta matsayin yar uwar ka kayimun hakan ka gama cika mun burina a kanka",
Wani irin zufa Abdul yaji yana keto mishi tun daga saman kansa har kan dan yatsar kafarshi
" Ina sane da kasan kuna da 'ya da ita amma Inaso ka bar mata wannan yarinya a gunta hakan shine zai bata farin ciki a bisa wahalhalun daka daurata a rayuwarta,
" bance karka ga yarka ba sam ta kace har a bada ba Wanda zai gogeshi karkace zaka taba karbarta indai ba zainab tabaka itaba da kanta ko mijinta in bazai rike ta ba hakan ba yana nufin ka kasa kulawa da ita bane no sam you can still be fulfilling your fatherly duty to her duk inda take inafata ba sai nayi dogon bayani akai ba ka fahimceni kana iya zuwa ka ganta ko a kawo ma ita amma ba yarda ka kwace ta takarfi ko in Zainab bata soba wannan ne kadai inafata zaka iya mun hakan",
Haka dady ya daddaure Abdul da igiyoyi a wannan yammacin.

" Hajiya Salamatu ban fahimci inda zancen ki ya dosa ba ki fahimtar dani dallah2"
Murmushi wacce aka Kira hajiya salamatu tayi Tana hura shisha dinta ko a jikinta daga ita sai daurin kirji su kusan shida ne zaune tsakar dakin wadan da kusan duk hajiyoyine banda biyu da suke yan matasan mata masu shekaru da ba zasu wuce 30 ko 35yrs ba,
" wai hajiya Rabi meye baki gane ba cikin zancen ta kinfa San wannan har ka ba tun Yau ba"
Daya daga cikin matansan matan tayi magana Tana kallon hajiya Rabi,
" yo naga ni yaushe ta hadu da yarinyar da har za'a hada ta cikin 'yan matan da zamu siyar ko dirzar kudin ta bata gama yi bafa"
Murmushi ta gefe hajiya salamatu tayi tare da ajiye abunda take zuka Tana kallonsu
" ke hajiya Rabi kibar wannan yarinyar bafa irin ta nake komawa dasu ba a waje kika San Aisha ba ciki ba yarinyar da duk ta gama rabarwa ta zama ragowa yo mezan dirza Amma kinga in nahada a shirin Alhaji Tanimu ae zai bani wani abun",
Zaro ido hajiya Rabi tayi cike da mamaki yayinda sauran ke dariyar zancen hajiya salamatu
" tabdi jam yanzu dama kyan iya waje ne lallai kam da wannan sai ince gwanda da bazawara ma kika samo da tafi miki yanzu yar yarinya kamar wannan tirkashi"
" yo kedai ayi sha'ani yaran yanzu ba iskacin suka saniba basu San gyara ba ke dai kawai ayi sha'ani" dayar babbar ta cafe
" Salamu Alaikum"
" Lafiya idi meya faru"
" dama wannan yarinyar ce tazo uhmmm yauwa sunanta tace Aisha"
Kallon juna sukai suka sheke da Dariya " yo wannan shegiyar 'ya zatai dogon rae"
" lami barta kawai in Alhaji ya cillata can ae tayi a can mugani shegiya" nan suka cigaba da sheka dariyarsu ta mugunta.

RASHIN DACENơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ