Dedicated to RASHIN DACE fans always
🅿️103 to 104
" look billy walh nagaji i am very sleepy infact ko Abdul ban fada ma zan fito ba na fito da sanmakon nan"
Cike da takaici billy ke kallon baby wacce keyi kamar ita kadai ce ta gaji " haba ka wata karki damu mun kusa Isa kauyen ok"
Shiru baby tayi duk ta gaji sai kace Wanda zasu bar Kano tun safe ace basu kai unguwar da malamin yake ba wani irin takaici ne ya rufe baby,
Shiru sukai ba'akai 30'mins ba suka Isa kofar inda suka bar me taxi din dan jiransu su kamalla dan ya maidasu har cikin gari
Tun daga waje suke ganin cinkoson mata da alama layi ake agun nan hankalin baby ya kuma tashi,
" billy yanzu duk wannan wahalar"
" no wait let me call him mu tace Tafada mai basai munbi layiba" gyara tsayuwa baby tayi Tana yatsine yatsinen fuska
Fiddo waya billy tayi takira malamin inda ko 2mins basu karaba akazo aka shiga dasu ciki wasu daga matan dake bin layi nata fada amma Ina haka dole akashiga dasu baby,
Baby na shiga gidan tashiga sheka amai sakamakon wata kwata me shegen wari dake tsakar gidan ga shirgin da tarkace gashi ta shaki tsamin matan dasukaita kutsawa suka shigo.Wani rinannen Ruwa da yayi ja aka mika ma baby ta dauraye bakinta da sauransu
Inda Allah ya taimakesu suna da bottle water a mota dole shi billy ta dauko sanin halin kawar tata
Da sallamar su suka tunkari dakin da malamin ke ciki inda yake aiki kenan wani irin dum dakin yake yi tunda yaga baby yake yage baki yana dariya dakyar baby ta daure tashiga suka zauna,
" Aha lale sanunku da zuwa hajiya ya jikin"
Tabe fuska baby tayi Tana Karema dan dakin nasa dake Kama da cage kallo take billy ce tayi sauri ta amsa mishi da " Lafiya kalau",
" Masha Allah ku saki jikinku Insha Allahu tunda kuka zo wannan guri matsalarku ta warke Amma duk da kun mun bayani a waya inaso a kuma yi mun
Billy ganin hankalin baby baya tare da su yasa tadan fisgota " dama wannan kawata ce to akaramakallahu mijin ta Sam bai kulata tunda akayi auren gaba daya ba wani abu daya taba shiga tsakaninsu sai bakar magana",
Sake kallon baby yayi yana washe baki " na fahimta matsala kam ta warke Insha Allahu dan Annan zata mallake abunta sai yadda tace dashi in tace zauna zai zauna haka in tace tashi dole sai ya tashi".Katon jarbinsa ya dauka yana ja sai ya watsa jarbin a kasa " hajiya dauka daya!"
Kallonshi baby tayi cikin rashin fahimta billy tayi mata alamu hakan yasa ta dauka sai ya mika mata hannu ya karba dai2 gun,
Sunyi haka yakai 3times duk sanda y a karba sai ya tsaya yayi shiru kamar Wanda ke karanta wani abun bayan anyi na ukun ne ya kallesu
" mijinki anyi asiri ne babba a kanshi dan karya kusance ki Sam shiyasa kike ganin baiko Jin wani abu game dake kuma macece kinada kishiyane"
" eh Tana dashi akaramakalllahu" wani shu'umin murmushi yayi yana kallon baby wacce takaici ya isheta gaba dayansu shida billy haushi suke bata,
" zanmata aiki sai dai akwai abunda zan bukata a gunta"
" akaramakallahu indai kudine Baka da matsala ae ka fadi kawai",
Dariya yayi Wanda kanaji kasan Tana da wata manufa kurama baby ido yayi yana bin jikinta da kallo sosai take jinta uneasy agun
Girgiza kanshi yayi sanda dukansu ke jirarsa yayi magana,
" ba kudi kawai nake bukata ba aikin da za'ayi saida sperm dinta"
A razane baby ta tashi daga zauna da take billy tashi tayi tare dafa baby wacce tayi kamar sabuwar kamun jinnu." billy lets go bana so dama Tunda muka shigo na fahimci baisan komai ba tunda sai an mai dallah2 Wanda nasaba jin basai anma malamin gaske bayanai ba duk kame2 yake oya let's get the hell out of this place"
" haba hajiya zauna mukarashe magana mana walh aikin da zan miki ba kowa zai miki shiba ba maven da zata zo nan ta tafi da rashin sa'a walh"
Billy ce ta tsaya tanason ba baby baki amma Ina tuni baby ta fice fuuuu daga dakin
Itama billy shirin fita take sanda taji akaramakallahu ya rikota a tsorace ta kalleshi tare da fisgewa,
" tunda kawar ki taki ke kiban kanki tunda kuka shigo hankali na yake a dukan ku bana ki"
Cike da takaici billy takara kokarin fita aiko sai Ji tayi ya jawo ta yana kokarin danna bakin cin goronsa a nata bakin wani irin karfi tasa ta hankade shi gefe saida yakai kasa,
"Amma gaskiya kan bata wayonka ashe dama kai mutumin banza ne Allah ya isa wahalar da mukai na zuwa"
Fita tayi cike da takaici ganin irin matan dake gun ta tabbatar ba karamun barna akaramakallahu yake ba a wannan tsukkun dakin nashi na bincike,
A mota ta tarar da baby wacce tagama cika taf da bacin rae lallai Yau tasan mita kam zata sha shi da bala'i harsh koma gida,
Haka kuwa zuwa tayi tashiga ciki Tana nan baby tayi ta mata ihu kan ta bata musu lokaci a shirmammen waje " walh billy shiyasa banson harkar malaman nan sam har gwanda in yazama dole naje gun asalin boka Wanda dama can nasan ba Allah a tattare dasu bare Raina ya baci irin haka mtsw"
" baby ba zaki gane bane walh ni kaina I am not happy about this Amma ya zanyi sai hakuri".Zaune yake a office lokacin da phone dinshi ta shiga ringing sam Yau baisan meyasa jikinsa yayi sanyi ba
" momy!"
Yafada sanda ya dau wayar tare da kaiwa kunnuwansa yayi sallama shiru yayi yana nodding head dinshi yana saurarenta,
Lokaci daya ya tashi tsaye tare da da daya hannunsa aka " Yau ba sai gobe ba zan shigo ko jirgin yamma ne zuwa kd momy Insha Allahu",
Kashe wayar yayi ya koma ya zauna " ya ilahi meke shirin faruwa dani no I can't let that happen"
Kamar Wanda aka mintsula kuma saiya tashi da sauri yafara tattara yan shirgin shi yasa wanda zai tafi dasu a black suitcase dinshi
Wayarsa ya dauka yafara dialing wata no Ana dauka baiyi wata2 ba " please ka duban karfe nawa ne zan sama flight yanzu to kd"
Yana fada ya kashe wayar ya rufe office din ya fita ko gida bai koma dan yayi sa'ar samun jirgi kusan lokaci ya kusa hakan yasa direct ya nufi airport cike da damuwa,
Tunda ya shiga jirgi yake kallon Hoton Zoya yana ciza lebe yayinda flight attendance din suka fara magana kan a kashe waya daya daga ciki ne tazo kanshi
" please sir can switch off your phone" dagowa yayi batare da yace komai ya maida kansa dan already wayarsa yasa ta a flight mode.Mutumin dake kusa dashi ne ya kalla screen din wayar Abdul din ya kalla yarinyar wacce still take tsaye Tana shirin sake maimaita wa,
" but one can always leave his phone on flight mode so"
" yes Sir"
Nan yayi mata bayani ta tafi but cike da mamakin Abdul din,
" Salamu Alaikum"
Mutumin dake kusa dashi din ya bashi hannu sauke wayar Abdul yayi zuwa aljihu
" yakake"
Nan kan kace me daga gaisawa mutumin ya cika Abdul da surutu tun yana kin kulashi harya hakura ya sake dashi
Cikin dan kankanin lokaci suka saba nan sukaita hira har suka karaso kd inda sukai sallama kowa ya Kama gabansa but still sunyi exchanging number Abdul na mamakinsa " he is very strange man".Direct gidan su Zoya ya nufa Ana shirin kiran magrib a lokacin Amma heart dinshi cike yake da damuwar abunda zai tarar yake,
Knocking yayi sanda taxi me taxi din ya saukeshi a bakin gate din
" waye?"
Megadi ya tambaya sanda ya karaso ya leko yana ganin Abdul ya bude mishi " Ah Alhaji kaina"
Nan suka gaisa kai tsaye part din momy Abdul ya nufa zaune take a falonta Tana kallo ita daya gidan ma tsit
Sallamar shi da taji ne yasa tashiga gyara zama cike fara'a ta amsa mishi ya shigo falon,
" Ai tuntuni nake sa ran ganin ka Ashe kana nan tafe"
" inawuni momy"
Yafada sanda ya tsuguna cike da girmanawa kamar yadda ya saba mata kallon falon yayi Jin ko ina shiru ya kalleta,
" suna can sunbi doctor tun da suka zo da rana su Safiya da Ahmad kuwa sunje gidan yar uwar maman su kaga daga ni sai zainab ne gidan kamar mayu",
Gaban Abdul ne ya fadi Jin yaranshi sunbi doctor Amma yaji dadin Jin ba kowa and zoya na nan,
" bari nakirata ta kawo ma kayan sha ko"
" no momy bana bukatar komai yanzu Tana Ina ne Zainab din"
" Tana can dakinsu" Tafada da sauri kamar dama jira take taji ya tambaya shiru yayi ta lura kunyar ta yake Ji hakan yasa ta kalleshi,
" ka shiga ciki mana".Cike da nauyi da jin kunya yatashi ya shige cikin corridor din da zai sadashi da dakin
Sallama yayi shiru ba'a answer mishi ba hakan yasa ya tura kofar yashiga Jin karar Ruwa a toilet dinyasa ya fahimci tana ciki,
Zama yayi bakin bed din yana shakar kamshin turarenta daya ke tashi a dakin nodding din kansa yayi tare da ciza lips dinshi
" you will never change my Zoo",
Yajima zaune a gun Jin alamun tana kokarin fitowa yasa ya canza mazaunin sa zuwa inda bazata iya hango shi ba sam,
Bude kofar tayi ta fito yana kallonta daga ita sai towel zuwa gwiwa tana dan shashare jikinta dashi " you be calling me calling, calling you",
Wakar da ta fara kenan sanda tafito direct dressing mirror ta nufa taja kujera ta zauna
" will you die for me, die for......" haka kawai jikinta yabata Ana kallonta da sauri ta waiga suka hada ido ihu tayi tare da tashi dan bata ga fuskarshi dakyau ba,
Ji tayi anjanyota tare da matse bakinta Tana kokuwar kwacewa a hankali ta daura idannunta kan nashi yana mata murmushi
Rasa me zatai tayi a wannan lokacin sun jima a tsaye a hakan ba Wanda yace da dan uwansa komai..................(What is the problem with Mr.A and momy again).Sai mun hadu a next page in Allah me kowa me komai ya kaimu don't forget to comment, vote share 👌
YOU ARE READING
RASHIN DACE
Romancewani ihu sukaji da alama ta can baya ne da sauri suka nufi bayan, Inda suke Jin hayaniya " na duke ta kiyi wani abu akai", " Rukayya ni kike fadama kinduke ta din ni sa'arkice", Tafada tana nuna ta da hannu ita kuma sai murguda baki take tana harart...